Labari Daga Jihar Yobe Da Kewaye

Labari Daga Jihar Yobe Da Kewaye Domin Samun Sabbin Labarai Na Siyasa Da Abubuwan Dake Faruwa A Duniya.

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da Amarya da Uwargidan shugaban ƙaramar hukuma a JigawaWasu ‘yan bindiga da ba a san ko su ...
04/11/2023

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da Amarya da Uwargidan shugaban ƙaramar hukuma a Jigawa

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari gidan shugaban ƙaramar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa tare da sace matansa guda biyu.

Shugaban ƙaramar hukumar Honarabul Nasiru Ahmed Kiyawa – wanda ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin – ya ce ‘yan bindigar sun je gidan nasa ne bayan sallar Isha’i a ranar Juma’a daddare, inda s**a kore mutanen da ke kofar gidan nasa kafin su shiga ciki.

Ya ƙara da cewa “sau biyu suna harba bindiga a ƙofar gidana kafin su shigo ciki”.

Daga nan ne kuma s**a tafi da matan nasa guda biyu, inda kuma har yanzu suke garkuwa da su, k**ar yadda ya tabbatar wa BBC.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Lawan Adam Shiisu ya tabbatar wa BBC faruwar lamarain, inda ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ta samu kiran gaggawa kan lamarin, inda kuma nan take s**a tura jami’ansu domin kai ɗauki.

Sai dai kafin zuwan jami’an na ‘yan sanda tuni ‘yan bindigar sun yi awon gaba da matan shugaban ƙaramar hukumar.

DSP Shiisu ya ce tuni rundunar ‘yan sanda jihar ta baza jami’an a lungu da saƙo na ƙaramar hukumar domin kuɓutar da matan.

Ya kuma ce rundunar ‘yan sandan na maraba da duk wasu bayanai da za su taimaka wajen kai ga gano masu garkuwan don kuɓutar da matan.

Matsalar garkuwa da mutane dai wani baƙon al’amari ne a jihar ta Jigawa, to sai dai matsalar na neman kunno kai cikin jihar a baya-bayan nan.

Dangote Na Yi Min Bita Da Kulli ~ BUAKamfanin BUA ya fitar da dogon jawabi a matsayin martani ga zargin da kamfanin Dang...
04/11/2023

Dangote Na Yi Min Bita Da Kulli ~ BUA

Kamfanin BUA ya fitar da dogon jawabi a matsayin martani ga zargin da kamfanin Dangote Group ya jefe sa da shi.

A wasikar da ta fitar ga duniya, BUA Group ya karyata Dangote, an dade Abdul Samad Rabiu yana ta gwabzawa da Aliko Dangote.

Kamfanin na BUA ya dauko tarihi tun daga 1991 lokacin da aka yi wahalar s**ari, amma sai aka yi sa’a Abdul Samad Rabiu yana da s**ari a kasa.

BUA ya ce Aliko Dangote ya nemi a saida masa s**arin, sai a karshe lamarin ya kare a kotu, kamfanin ya ce haka Rabiu ya jajirce na watanni uku.

Har ila yau, kamfanin ya ce ya taba karban aron fili daga Usman Dantata domin ya kafa kamfanin siminti, amma Dangote ya jawo aka karbe filin.

A dalilin wannan abin da ya faru a gwamnatin Olusegun Olusegun Obasanjo, BUA ya yi asarar filin da ya karbi aro daga hannun kawun na Dangote.

Wasikar ta ce haka kamfanin ya yi ta fama bayan samun lasisin kafa kamfanin siminti, BUA ya ce sam kalubalen nan ba su iya taka masu burki ba.

Kar Kayi HASSADA, Domin Tana Zubar Da Ladanka, Kuma Tana Mayar Dakai Baya A Cikin Al'umma Kuma Tana Bakanta Zuciya. Ka G...
30/10/2023

Kar Kayi HASSADA, Domin Tana Zubar Da Ladanka, Kuma Tana Mayar Dakai Baya A Cikin Al'umma Kuma Tana Bakanta Zuciya.

Ka Guji Yin KARYA, Domin Karya Tana Zubar Maka Da Mutunci A Wajen Allah Da Bayinsa, Kuma Tana Kusantar Dakai Zuwa Ga Wutar Jahannama.

Ka Guji Aikata HA'INCI, Domin Ha'inci Yana Toshe Maka Kofofin Arziki, Kuma Yana Hana Maka Albarkar Rayuwa Sannan Kuma Yana Nauyaya Maka Kafafunka Akan Siradi A Ranar Alkiyama.

Ka Guji ZINA Da Dangoginta (Kamar Su Luwadi Da Madigo) Domin Suna Cire Maka Imani Daga Zuciyarka, Kuma Kullum Suna Nisantar Dakai Daga Aljanna Suna Kusantar Dakai Zuwa Ga Wuta Kuma Suna Hana Maka Ni'imomin Kwanciyar Kabari.

Ka Guji CIN KUDIN RUWA (RIBAA) Da Dangoginta, (Kamar Cin Dukiyar Marayu, Karbar Cin Hanci Da Rashawa) Duk Wadannan Suna Janyo Maka Tsinuwar ALLAH Ne, Kuma Masu Cin Haram Za'a Tashe Su A Ranar Alkiyama Da Katon Ciki, Wuta Yana Fitowa Ta Bakinsu.

Ka Guji CIN MUTUNCIN MUSULMI, Domin Kuwa A Ranar Alkiyama Za'a Kwashe Ladan Aiyyukanka A Biya Su Dashi.

Kuma Ba Zaka Samu Lada Ta Hanyar Zagin Wani Ba, Ba Zaka Taba Samun Alkhairi A Wajen Allah Ta Wannan Hanyar Ba.

Rashin Kunya Ko Tsinuwa Ko Zage Zage Ba Halayen Mumini Bane, Babu Mai Yinsu Sai Fasiki.

Ka Guji GIRMAN KAI, Domin Shi Girman Kai Halin Fir'aunoni Ne, Kuma Allah Yana Nisantar Da Masu Girman Kai Daga Rahamarsa, Sannan Yana Kaskantar Dasu A Ranar Alkiyama Kuma Babu Wanda Zai Shiga Aljanna Da Girman Kai.

Mutanen Kirki Da Gaskiya Aka Sansu Da Kaskantar Da Kai Rikon Amana Da Kyautata Mu'amala.

Lawan A Zeeko Damaturu✍️...

Uwa ta sakawa yaranta maganin feshi, tayi sanadin mutuwar yayanta Mata guda Uku.A rahotanni da muka samu yaran su uku 3 ...
29/10/2023

Uwa ta sakawa yaranta maganin feshi, tayi sanadin mutuwar yayanta Mata guda Uku.

A rahotanni da muka samu yaran su uku 3 sun rasu ne bayan mahaifiyyarsu ta saka masu maganin feshi Akai.

Wani mazauni anguwarsu yace mamar su tace wai yaran suna da korkota akan su, kuma tayi magani tayi magani amma basu mutu ba.

Dalilin haka yasa tasa masu maganin Feshi (na kashi ciyawa) akai rashin saa magani yashiga cikin kan yara wanda shine har yayi sanadiyyar mutuwar su.

Muna kara jan hankalin iyaye mata a rika kiyayewa da Abubuwan da ake amfani dasu wajen kula da jiki.

Allah yayi musu rahama su kuma iyayen Allah ya basu haqurin wannan babban rashi.
Rahoto 📷: Mujahid Saleh Saad Mujahid Saleh Saad - Dan maliki

YANZU -YANZU: Atiku Abubakar zai gabatar da shirin manema labarai kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, wanda ya tabbatar...
28/10/2023

YANZU -YANZU: Atiku Abubakar zai gabatar da shirin manema labarai kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, wanda ya tabbatar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasar Najeriya.

Za ayi taron manema labaran a ranar Litinin, a sakatariyar jam'iyyar PDP ta ƙasa dake Wadata Plaza, Abuja.

Na yi nazarin waƙoƙin Rarara sama da 80, kuma abin da ya yiwa Buhari ɗabi’arsa ce, sannan tabbas nan gaba ma sai ya yiwa...
28/10/2023

Na yi nazarin waƙoƙin Rarara sama da 80, kuma abin da ya yiwa Buhari ɗabi’arsa ce, sannan tabbas nan gaba ma sai ya yiwa ATM Gwarzo da Tinubu, Cewar Farfesa Abdalla Uba Adamu

Me zakù cè ?

Matsalar Rarara Ita Ce: Bai Sani Ba, Kuma Bai San Bai Sani Ba, Cewar Kwararren Ɗan Jarida, Ja'afar Ja'afarMé zakú cé?
27/10/2023

Matsalar Rarara Ita Ce: Bai Sani Ba, Kuma Bai San Bai Sani Ba, Cewar Kwararren Ɗan Jarida, Ja'afar Ja'afar

Mé zakú cé?

Gwamnatin Mai Mala Buni ta raba wa ƴan Gudun Hijira mutum 5000 kayan abinci a garin Goniri.Yau Laraba, 25th ga watan Okt...
25/10/2023

Gwamnatin Mai Mala Buni ta raba wa ƴan Gudun Hijira mutum 5000 kayan abinci a garin Goniri.

Yau Laraba, 25th ga watan Oktoba, shekarar 2023, Gwamnatin Mai Mala Buni, karkashin hukumar Agajin Gaggawa (SEMA) karkashin jagorancin Dr. Mohammed Goje a raba wa ƴan Gudun Hijira magidanta har mutum dubu biyar (5,000) kayan abinci a garin Goniri dake karamar hukumar Gujba.

Tallafin, wanda ta samu kekkyawar tsari musamman wajen zaƙulo wadanda s**a dace domin a rage musu halin da suke ciki.

Idan bamu manta ba, a makonni biyu da s**a gabata, mai girma Gwamnan Talakawa kuma Jajirceccen Gwamnan Jahar Yobe, H.E Mai Mala Buni, CON, ya ziyarci yankin Goniri da Mandunari, bayan ya saurari koke-koken Mutanen yankin, yayi musu alwashin Gwamnatinsa zata cigaba da yin kokarin kawo musu ɗauki da cigaba mai ɗorewa.

Alhamdulillah!. Kwanaki kaɗan bayan mai girma Gwamna ya bada umarnin a fara shiriye-shiriyen kai wutan lantarki yanki, yau kuma Hukumar Agajin Gaggawa SEMA ta shigo musu da Alkhairi na kayan abinci domin rage musu raɗaɗin halin yau da suke ciki.

Mustapha Moh'd Gujba,
The Political Banker.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff a fadar Shugaban kasar dak...
25/10/2023

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff a fadar Shugaban kasar dake Abuja.

Innalillahi wa inna ilaihil Raji'un.Anyi rashin daya daga cikinDattawa Arewa Alhaji Adamu Fika.Marigayi Alh Adamu Fika y...
25/10/2023

Innalillahi wa inna ilaihil Raji'un.

Anyi rashin daya daga cikin
Dattawa Arewa Alhaji Adamu Fika.

Marigayi Alh Adamu Fika ya rasu ne a daren jiya Talata 24 ga watan Oktoba cikin jirgi sama a kan hanyar dawo wa Najeriya Daga kasar Ingila.

Wazirin Fika, Adamu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 90 Aduniya

Adamu Fika Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Nijeriya ne

Danburan Fika, Alhaji Idris Adama Kukuri shi ya tabbatar wa Daily Trust labarin mutuwar a wata ganawa ta wayar tarho.

Ubangiji Allah ya jikan sa da rahama yasa Aljanna ce makomar sa.

Hukumar farin kaya ta civil defence tayi nasarar k**a mutane 76 da ake zargi da auren kinsi.A rahotanni da muka samu, Ru...
25/10/2023

Hukumar farin kaya ta civil defence tayi nasarar k**a mutane 76 da ake zargi da auren kinsi.

A rahotanni da muka samu, Rundunar tsaro ta Civil Defence a Najeriya (NSCDC) Reshen Jihar Gombe ta k**a mutane 76 da take zargi da ƙoƙarin ƙulla auren jinsi a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedkwatar hukumar ta jihar, Kwamandan Civil Defence na jihar Muhammad Bello Mu’azu wanda ya yi magana ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SC Buhari Sa’ad, yace an k**a waɗanda ake zargin ne a rukunin shaguna na 'Dua Plaza' bayan samun rahotannin sirri kan mummunar aniyarsu.

“Ina sanar da ku cewa, a yunƙurin da rundunarmu ke yi na kawar da miyagun laifuka da rashin ɗa'a a cikin al’umma, jami'anmu sun k**a mutane 76 da ake zargi da shirin yin auren jinsi.

An k**a su ne a Dua Plaza dake kan hanyar Bauchi, suna gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar ɗaya daga cikinsu yan luwaɗi, kuma a wannan bikin, suna niyyar ƙulla auren jinsi.

Yace bisa tsegumta mana hakan da aka yi, dakarunmu s**a far wa wurin, s**a damƙe mutane 76 da muke zargi”.

Buhari Sa’ad yace daga cikin mutane 76 da ake zargin, 59 maza ne, 17 kuma mata, daga cikinsu maza 21 sun furta da bakinsu cewa su ‘yan luwaɗi ne, sauran kuma sun je wurin ne bisa gayyatarsu da aka yi.

Yayin da yake ƙira ga iyaye su riƙa sanya ido kan ‘ya’yansu da sanin a su waye abokansu da inda suke zuwa, jami'in hulɗa da jama'an ya nemi ƙarin haɗin kai da goyon bayan jama’a don ganin an magance aikata laifuka da rashin ɗa’a a jihar.

Yace da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

Da yake zantawa da manema labarai, babban wadda ake zargi da shirya taron Bashir Sani wanda aka fi sani da Bushrat ɗan anguwar Tabra a cikin fadar jihar, yace su kawai suna bikin zagayowar ranar haihuwarsa ce.

To sai dai mahaifin shi Bushrat, yace ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya ɗora ɗan bisa turba ta kwarai amma ya fanɗare.

Yace shi yanzu ba ruwansa, jami'an tsaro su ɗauki duk matakin daya.

Rahoto:📷 Mujahid Saleh Saad - Dan maliki Mujahid Saleh Saad

TÀMBAYA GA RARARÀ: Ka Yi Kira Ga 'Yan Arewa Su Fito Kidaya, To Wa Zai Je Ya Kirgo Wadanda Ke Hannuń 'Yan Bíndíga?Daga Al...
24/10/2023

TÀMBAYA GA RARARÀ: Ka Yi Kira Ga 'Yan Arewa Su Fito Kidaya, To Wa Zai Je Ya Kirgo Wadanda Ke Hannuń 'Yan Bíndíga?

Daga Aliyu Ahmad

Gwamnatin Yobe tana kokari don mahajjata su cilla kasa mai tsarki ta sabon tashan jiragen sama na garin Damaturu a sheka...
24/10/2023

Gwamnatin Yobe tana kokari don mahajjata su cilla kasa mai tsarki ta sabon tashan jiragen sama na garin Damaturu a shekarar 2024.

Cikin wata ziyara na musamman da Gwamnan Jahar Yobe, H.E Mai Mala Buni, CON tare da tawagar sa s**a kai wasu kamfanonin kere-kere injina da na'urorin tashoshin jiragen sama a ƙasar Spain domin haɗin-guiwa wajen kammala aikin titin sauka da tashi (Runway) na sabuwar tashan jiragen sama na garin Damaturu.

Wanda inganta titin sauka da tashi (Runway) musamman wajen saka wasu na'urori da fitilu su ne zasu bawa Gwamnatin damar tashi da sauka cikin duhun dare daga Jahar Yobe zuwa kasa mai tsarki ko daga kasa mai tsarki zuwa jahar Yobe a Hajjin 2024.

Aikin saka fitilun Runway sune kaɗai s**a rage wa tashan jiragen saman.

Cikin jawabinsa, shugaban Kamfanin, Daniel Randell, yayi alwashin zaiyi aiki da Gwamnatin Jahar Yobe don inganta tashan jiragen.

Daga Banker Gujba

ALLAHÚ AKBÀR: Babu Abinda Yake Sa Ni Farin Ciki Kamar Na Ji An Ambaci Annabi Muhammadu (SAW), Cewar Dr. Maryam ShettyWan...
22/10/2023

ALLAHÚ AKBÀR: Babu Abinda Yake Sa Ni Farin Ciki Kamar Na Ji An Ambaci Annabi Muhammadu (SAW), Cewar Dr. Maryam Shetty

Wanne fata zaku yi mata?

KACÍCÍ - KACÍCÍ: Mace Ta Farko Da Ta Fara Shan Sigàri A Ƙasar Hausa, Sunanta Ladi Bushe - BusheShin kò zaku iya faɗa man...
22/10/2023

KACÍCÍ - KACÍCÍ: Mace Ta Farko Da Ta Fara Shan Sigàri A Ƙasar Hausa, Sunanta Ladi Bushe - Bushe

Shin kò zaku iya faɗa mana ƴar wace jiha ce a Arewacin Nàjeriya ?

DAGÀ Shafin DOKIN KARFE TV

Rahama MK da aka fi sani da Rabi Bawa Maikada a cikin shirin Kwana_casa'in ta samu karuwar diya mace a gidan aurenta na ...
22/10/2023

Rahama MK da aka fi sani da Rabi Bawa Maikada a cikin shirin Kwana_casa'in ta samu karuwar diya mace a gidan aurenta na zahiri.

RA’AYI: Ai Zulum Ya Kera Tsara! Waye Abba Kuma? Ana Babbakan Zomo Wa Ke Maganar Bera, Ra'ayin Alhaji Haruna Dan BornòMe ...
22/10/2023

RA’AYI: Ai Zulum Ya Kera Tsara! Waye Abba Kuma? Ana Babbakan Zomo Wa Ke Maganar Bera, Ra'ayin Alhaji Haruna Dan Bornò

Me zakù cè ?

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNAllah yayi wa sabon Kwamishinan sake gine-gine da tsugunar da 'yan gudun Hijira na Jih...
21/10/2023

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah yayi wa sabon Kwamishinan sake gine-gine da tsugunar da 'yan gudun Hijira na Jihar Borno rasuwa.

Ibrahim Idris Garba ya rasu a cikin baccinsa a gidan hutawarsa wato Guess House dake unguwar rukunin gidaje na 777 a birnin Maiduguri.

Ana zargin dai guba aka saka masa inda tuni aka wuce da shi asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri don gudanar da bincike.

Allah ya gafarta masa ameen.

Address

Damaturu
110

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labari Daga Jihar Yobe Da Kewaye posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Labari Daga Jihar Yobe Da Kewaye:

Share