28/09/2025
Duk Wanda yake gudun nadama, da dana sani to Kar yayi kuskuren shiga HND a Mai Idris Alooma Polytechnic Geidam a ko wani department.
Hakika Mai Idris Alooma Polytechnic Geidam makaranta wacce ta kasance tana bada iLimi Shekara da Shekaru a matakin Diploma, saide kash ta Gaza a bangaren kawo HND da s**ayi wannan makaranta.
Magana ta zahiri shine course na HND ba'ayi accreditation nashi ba sannan ba rana, Dan haka duk Wanda yayi kuskuren Shiga to inamasa albishir da a karshe sai yayi nadama kmr yadda mukayi a yanzu haka.
Yau akallah mungama HND Computer Science Shekara biyu da rabi Amma Shiru kakeji babu maganar tafiya NYSC Wanda wannan kuma muna ganin gazawar management na Wannan makaranta musamman Shi dakuma domin munyi tazuwa domin shawo Kan matsalar saide kullum Labari Daya suke ta maimaita mana a karshe har muka gaji da zuwa.
Abu biyu shine Rashin Uploading na sunan wadanda s**a gama diploma a portal din Jamb domin samun daman yin regularisation, sbd jamb sun ciro tsarin duk wanda zai cika Direct Entry to sai yayi regularisation idan ba ita jamb din bace ta bashi admission a Lokacin da ya Shiga national Diploma haka zalika wadanda s**aje wani garin ma s**ayi HND basu tsira sbd ana buqatar jamb registration number wajen yin registration na NYSC amma haka poly musamman Yake batawa daruruwan students Rai.
Muma dalibai ne kamar saura kuma karatun nan kowa ya sheda munyi Shi to meyasa baz'a turamu NYSC ba, bayan wannan itace Kadai shedar da zaka nuna domin Neman aiki, kokuma zuwa mataki na gaba domin cigaba da karatu kmr PGD ko Masters, hakika mungaji da Jira kuma tura takai bango, dan haka muna Kira ga mai girman gwanma H.E Hon (Dr) Mal Mala Buni, kwamishinan iLimi na jahar Yobe, da sauran wanda abun yashafa da su shigo lamarin nan domin cikamana mafarkin mu. Allah yasa Mudace.
Nagode
Lawan Kolo Modu Geidam
QS Graduate
Class of 2023.