
26/08/2025
Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni, yayiwa Jihar Yobe komai, wannan wata hanyace wacce take Cikin hanyoyi mafi hatsari da lalacewa a Jihar Yobe tsawon Shekaru, Danchua zuwa Jajere mai nisan kilomita 35.
*Daga. Yakubu Mukhtar Ibrahim Nguru.
Wannan hanyar dukkan Wanda yabi hanyar jajere Danchua Yasan irin wahalar da Motoci Kesha Dama Al'umma, hanyar ta kasance idan har ba Motocin Dake Binta kullum ba sune Golf, bakuwar mota Bata Isa ta ratsa wannan hanyarba, saidai idan Hilux" Amma yanzu ta zama tarihi zuwan Gwamna Mai Mala Buni.
Akwai lokacin da munje gaisuwa da Abdulkadir Jajere wallahi tun a kolere nagane motana bazata iyabin wannan hanyarba najirasu sunzo da Hilux nashiga Hilux na ajiye motana a Kolere, idan kuka dubba wannan rami da aka dauka a photon zakuga ba karamin rami bane' kuma fa bawai wannan ramin kadai bane har kaje garin irinsu zakayi ta gani. "Alhamdulillah Gwamna Buni' yasharemusu hawaye.
A lokacin na tsaya nace ikkon Allah, na tambayi wani nace tsawon Shekara Nawa wannan hanyar take haka Yace yajima, nace Alkali jajere sanda yake Senata a haka take Yace kwaraima kuwa nace lalle bakuyi dacen senataba, nashiga garin mungama Sallah Gidan Mai gari nasake cewa wani gaskiya na tausayamuku wannan hanyar taku Yace Wallahi sun jima a hakan, nayi shiru nace ikkon Allah.
Kuma wani abin mamaki fa, Motocin da suke iyabin wannan hanyar Wallahi Golf ne Amma zakaga an Daga bayan motocin anyi Kari da karfe, ko tsoro kuma basayi Babu dare Babu rana sukebin hanyar, domin Kamar inaga Motocin sunsabama dabin wannan hanyar.
Muna rokon Allah Yasakawa Gwamna Mai Mala Buni da Alheri hakika zuwansa yagera hanyoyi Wanda Shekara Goma baya ana fama dasu. Allah Yasa Gwamna Mai Mala Buni idan yatafi musamu Mai kishin Al'umma irinsa Amin.
Yakubu Mukhtar Ibrahim Nguru.