Al mahaara School for Qur'anic Memorisation Damaturu

Al mahaara School for Qur'anic Memorisation Damaturu SABUWAR MAKARANTAR HADDAR ALQUR'ANI MAI GIRMA DA KE CIKIN ANGUWAR KRIKASAMMA (NEW JERUSALEM) DAMATURU JAHAR YOBE

08/01/2025

SABUWAR MAKARANTAR HADDAR ALQUR'ANI MAI GIRMA DA KE CIKIN ANGUWAR KRIKASAMMA (NEW JERUSALEM) DAMATURU JAHAR YOBE.

Don Neman Karin bayani a Kira wannan lambar 07033875250

20/03/2024

Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da fara biyan albashin limamai, na'ibai da ladanai na masallatan juma'a a fadin jihar.

13/03/2024

Wannan ba shauƙi bane hauka ne tsantsa.........

10/11/2023

Mu ƴan Malikiyya ne kuma muna alfahari da haka. Idan ka ga mun sauka daga mu'tamad na mazhabarmu, to ra'ayin wani mujtahidin (daga ko ina ya fito cikin da'irar Sunnah) da ya fi mu'tamad na mazhab zamu k**a.
Babban malami Shaikh Muhammad Ahmad Abdul-Qaadir Al-Gillaawy Ash-Shinqeeti ya ce: idan akwai nassi sarihi kan mas'ala, ba ruwana da ra'ayin kowa; amma idan mas'alah ce ta ijtihadi, to babu ijtihadin da ya fi na Maliku soyuwa a wurina.
Al-Gillaawy wani babban malamin Sunnah ne wanda hatta Ibn Baz da Imamush Shinqity mai Adwaa'ul Bayaan sun kasance masu girmama shi sosai, har Imamush Shinqeeti yake cewa be san wani malami da ya kaishi sanin Sunnah cikin ƴan Shinqeet da s**a zo Madina ba.

Allah ya ji ƙansu duka. Amin.

Said by "wani ɗan uwa"

Farin Naik, Sarkin Musulmi Sa'adu,da Dr Zakir Naik
30/10/2023

Farin Naik, Sarkin Musulmi Sa'adu,da Dr Zakir Naik

30/10/2023

ماالنصر إلا على عدو أقرب، ألا و هو الهوى.

أشد الجهاد جهاد الهوى، وما كرم المرء إلا التقى، وأخلاق ذوالفضل معروفة، ببدل جميل وكف الأذى

28/10/2023

Daga cikin abin da yake nuni ga cewa; Ahlus Sunna Mabiya Salaf Ahlul Hadith su suke kan gaskiya, da za ka duba littatafansu da s**a wallafa a Aqida, tun daga na farkonsu har zuwa na karshe, na da da na yanzu, za ka samu duka a kan tafarki guda daya suke tafiya, babu banbanci, maganarsu guda daya ce, duk da banbancin zamunansu da nisan da ke tsakanin garuruwansu. Ba za ka same su suna sabani a mas'alolin Aqida ba, b***e rarrabuwa, ta yadda in da za ka tara dukkan abin da aka nakalto daga magabatansu to za ka same su k**ar maganar daga zuciyar mutum daya ta fito, ta gudana a kan harshen mutum daya.

Shin akwai dalili da yake nuni a kan gaskiya k**ar wannan?

Amma idan ka kalli 'Yan Bidi'a da mabiya son zuciya za ka same su cikin sabani da rarrabuwa kungiya - kungiya, har ya kai ba za ka samu mutum biyu a cikinsu a kan Aqida guda daya ba. Sashe yana bidi'antar da sashe, har abin ya kai ga kafirtawa. Za ka samu Da yana kafirta ubansa, makobci yana kafirta makobcinsa, a kullum za ka same su cikin sabani da kiyayya a tsakaninsu da rarrabuwa. Har karshen rayuwarsu ba za su taba ittifaqi a kan kalma daya ba.

- Abul Muzaffar Al- Sam'aniy, cikin Al- Hujjah na Taimiy (2/ 239 - 240).

Wannan shi ne abin da ya banbanta Ahlus Sunna na gaskiya da kuma 'Yan Bidi'a da masu bin son rai da sha'awowin zuciya. Saboda haka 'Yan uwa mu yi hattara.

Dr. Aliyu muhd Sani

Address

Sabon Fegi
Damaturu

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al mahaara School for Qur'anic Memorisation Damaturu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share