08/03/2025
Takaitacecen Tarihin Karamar Hukumar Damboa, Jihar Borno
Damboa wata karamar hukuma ce da ke Jihar Borno, a Arewa maso Gabashin Najeriya. Karamar hukumar na da muhimmanci ta fuskar tarihi, al'adu, da tattalin arziki, musamman dangane da noma, kasuwanci da kiwo.
Tarihi da Asali
Damboa tana cikin yankunan da s**a daɗe da kasancewa a cikin daular Kanem-Borno, wadda ta yi fice a tarihi tun zamanin da. Yankin ya kasance muhimmin wurin kasuwanci da zamantakewar al’ummar marghi da wasu kabilu kamar kanuri, Fulani
Dam Sauran yaruka
A shekarar 1976, lokacin da aka kirkiri sabbin kananan hukumomi a Najeriya, Damboa ta samu matsayin nata, daga cikin tsoffin yankunan da ke ƙarƙashin Borno.
Damboa na da manyan garuruwa da kauyuka da s**a hada da:
Damboa (hedikwata)
Wasu daga cikin manyan kauyukan Damboa
Talala,Ajigin,Sabon Gari,Kafa,Wajiroko,Mulgoi
Akoi kauyuka samata 500 a karamar hukumar Damboa
Tattalin Arziki
Ana samun arziki ta hanyar:
Noma: Manoma na shuka gyada,gero, dawa, masara, wake, da kayan lambu.
Kiwo: Fulani makiyaya na kiwon shanu, tumaki, da awaki.
Kasuwanci: Ana gudanar da sana’o’i irin su fataucin dabbobi. Shanaye, Awani, raguna, zuwa wasu sassan kasar
Matsaloli da Kalubale
Rikicin Boko Haram: Damboa na cikin wuraren da rikicin Boko Haram ya fi shafa a Jihar Borno, inda hare-haren da aka sha fuskanta s**a haddasa rasa rayuka da raba mutane da muhallansu da Asaran makudan dukiyoyi.
Rashin Hanyoyi: Akwai matsalolin rashin kyawun hanyoyi, wanda ke hana sauƙin sufuri da cinikayya.
Karancin karancin noma: Rikicin da ya daÉ—e yana faruwa ya hana wasu manoma aikin gona, wanda ya haddasa karancin abinci a wasu lokuta.
Al’adu da Addini
Yawancin mutanen Damboa Musulmai ne, kuma suna da al’adun da s**a samo asali daga daular Kanem-Borno. Ana gudanar da bukukuwa irin su Sallah da bukukuwan gargajiya.
Damboa tana da muhimmanci a Jihar Borno, musamman wajen noma da kasuwanci. Duk da haka, rikicin da ya daɗe yana addabar yankin ya shafi rayuwar al’umma