01/11/2025
HARKAR MUSULUNCI TA NAJERIYA TA KARYATA ZARGIN KISAN KIRISTOCI
Ta bakin Farfesa Abdullahi Danladi
Daga Resource Forum, Islamic Movement in Nigeria
Harkar Musulunci a ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky, ta daɗe tana tsayawa kan zaman lafiya, adalci, da haɗin kan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko jam’iyyar siyasa ba. Harkar na ganin cewa Musulunci da Kiristanci addinai ne guda biyu daga Allah waɗanda ke kira ga alheri, tausayi da gaskiya.
A ganinta, Musulmi da Kiristoci suna da abubuwa da yawa da s**a haɗa su fiye da waɗanda s**a bambanta su, sai dai ‘yan siyasa masu son zuciya ne suke amfani da waɗannan bambance-bambancen don cimma burinsu.
A bisa tushen wannan akida, Harkar Musulunci ta yi imani cewa matsalar Nijeriya ba ta addini ba ce, amma ta ɗabi’a da siyasa. Matsalar ta samo asali ne daga rashawa, son kai, da yaudara da manyan ‘yan siyasa ke yi wa talakawa. Duk da ana ta ƙoƙarin jefa Musulmi da Kiristoci cikin gaba, a gaskiya abokan gaban su na gaskiya su ne waɗanda ke sace dukiyar ƙasa suna ci gaba da zalunci. Sheikh Zakzaky ya sha faɗi cewa, “Talakan Kirista da talakan Musulmi ba su da matsala da juna; abokin gaban su na gaskiya shi ne tsarin zalunci da ke bautar da su duka.”
A bisa wannan fahimta ne Harkar Musulunci ta nuna damuwa da ƙaryar da shugaban Amurka, Donald J. Trump, ya yi, inda ya zargi gwamnatin Nijeriya da goyon bayan “kisankai akan Kiristoci,” tare da barazanar sanya Nijeriya cikin jerin “ƙasashen da ke da matsalar ‘yancin addini.”
Trump da wasu ‘yan siyasa a Amurka sun yi ikirarin cewa “Musulmi masu tsattsauran ra’ayi” na kashe Kiristoci a Nijeriya, har ma suna nufin a turo sojojin Amurka don “kare su.” Harkar Musulunci ta Nijeriya ta karyata waɗannan zarge-zarge gaba ɗaya, tana kiran su ƙarya, tunzura, da kuma haɗari.
Ta bayyana su a matsayin wani ɓangare na farfaganda ta yammacin duniya da nufin tada fitina da neman hanyar tsoma baki cikin harkokin Afirka. Wannan irin zargi na karya yana watsi da ainihin matsalolin da s**a shafi siyasa da tattalin arzikin Nijeriya, yana kuma rage ta zuwa labarin “yakin addinai” wanda bai dace ba.
A gaskiya, Musulmi da Kiristoci duka suna fama da matsalolin tsaro iri ɗaya — ta’addanci, fashi, da zaluncin gwamnati. Ana kashe mutane a arewacin ƙasar inda Musulmi s**a fi yawa, haka ma ana kai hari kan coci da unguwannin Kiristoci. Waɗannan ba yakin Musulunci da Kiristanci ba ne, amma sakamakon tsarin mulki mai cike da rashawa da rashin adalci.
Harkar Musulunci ta kuma bayyana rashin gaskiyar ‘yan siyasar Yammacin duniya waɗanda ke da hannu wajen ƙona ƙasashe da kashe Musulmi miliyoyi a Iraki, Afghanistan, da sauran wurare, amma yanzu suna ikirarin kare hakkin dan Adam a Afirka. A ganinta, wannan “tausayin” da suke nunawa Kiristoci ba gaskiya ba ne, illa kawai wata dabarar siyasa ce don raba kan ‘yan Nijeriya da samun damar sarrafa albarkatun ƙasar.
Gwamnatin Nijeriya ma ta mayar da martani ta bakin mai magana da yawunta, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, inda ta musanta maganganun Trump, tana cewa “’Yan Nijeriya na addinai daban-daban sun daɗe suna rayuwa tare cikin zaman lafiya.” Gwamnati ta kuma tabbatar da kudirinta na “ƙarfafa haɗin kai tsakanin addinai da kare rayuka da haƙƙin kowa.” Harkar Musulunci ta yaba da wannan matsayi, tana kuma kira ga gwamnati ta tabbatar da gaskiya da adalci domin samun zaman lafiya na gaskiya.
Harkar ta yi gargaɗi cewa ƙasashen waje sun dade suna amfani da addini don rusa ƙasashe da neman dalilin tsoma baki. Kiran Musulmi na Nijeriya da sunan “radical Islamists” wani ɓangare ne na labarin ƙarya da Yammacin duniya ke yadawa don nuna addinin Musulunci a matsayin na tashin hankali. Wannan ra’ayi ba kawai yana karya Musulunci ba ne, har ma yana lalata zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Tun shekaru da dama, Harkar Musulunci ta yi aiki don bunƙasa tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin Musulmi da Kiristoci. Mabiyanta suna ziyartar coci a lokutan Kirsimeti da Easter, haka ma shugabannin Kirista suna halartar taron Harkar a matsayin alamar zumunci. Harkar tana la’antar kowacce irin hari da aka kai kan coci, kamar yadda take la’antar harin da ake kai wa masallatai. Manufarta ita ce cewa duk wanda ya kashe marar laifi, ba tare da la’akari da addininsa ba, kamar ya kashe dukkan bil’adama ne.
Harkar ta ci gaba da jaddada cewa zaman lafiya na gaskiya ba zai tabbata ba sai an samu adalci. Shugabannin Nijeriya su daina amfani da siyasar yaudara da rarrabuwa, su maida hankali wajen yaki da rashawa, talauci, da rashin tsaro. Jama’a kuma su gane cewa rikicin addini kawai yana amfanar da masu satar dukiyar ƙasa. Idan talakawa sun rabu, azzalumai s**an fi samun ƙarfi; idan sun haɗu, zalunci zai rushe.
A ƙarshe, Harkar Musulunci ta kira Musulmi da Kiristoci su ƙi yarda da labaran ƙarya da ƙasashen waje da wasu ‘yan Nijeriya ke yadawa don cin moriyarsu. Ya kamata mu haɗu a matsayin ‘yan ƙasa guda, mu dogara ga imaninmu da Allah da kuma burin samun ƙasa mai adalci da zaman lafiya.
Sakon Harkar ya bayyana a sarari: haɗin kan ‘yan Nijeriya ya fi ƙarfi fiye da ƙaryar da ke neman raba su. Ainihin yakin ba tsakanin Musulmi da Kiristoci yake ba, amma tsakanin gaskiya da ƙarya, adalci da zalunci, amana da yaudara. Har sai mun haɗu don fuskantar wannan gaskiya, ba za mu tsira daga danniya ba.
Harkar Musulunci ta Nijeriya ta tsaya kyam wajen zaman lafiya, adalci da haɗin kai, tana ƙin duk wani yunƙuri — na cikin gida ko na ƙasashen waje — da ke ƙoƙarin jefa ‘yan Nijeriya cikin gaba ta sunan addini.
Sayyid Ibraheem Zakzaky Office