Jawad Media Danja

Jawad Media Danja Dan Isar da Sakon Ahlul bait(as)
(3)

Meyasa masu Kafirta Mahaifan Manzon Allah (S) da Imam Ali (As), ba sa Kafirta Baban Sahabi Umar da Usman, duk da cewa a ...
19/08/2026

Meyasa masu Kafirta Mahaifan Manzon Allah (S) da Imam Ali (As), ba sa Kafirta Baban Sahabi Umar da Usman, duk da cewa a KAFIRCI s**a mutu?.

18/08/2026

Saƙon Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ga ’yan uwa

— Tare da Sheikh Sale Lazare, Niger 🇳🇪

Atayamu Share dan yan uwa su amfana

MUZAHAR TARBAR WATAN MAULUD DA CANZA TUTAR ASHURA ZUWA TA MAULUD...بسمه تعالى.اللهم صل على محمد و آل محمد و عجل فرجه الش...
16/08/2026

MUZAHAR TARBAR WATAN MAULUD DA CANZA TUTAR ASHURA ZUWA TA MAULUD...

بسمه تعالى.
اللهم صل على محمد و آل محمد و عجل فرجه الشريف 🌹🥀🌷

Ƴan uwa musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky (H) na da'irar ɗanja sun gudanar da zuharar tarbar watan maulud da kuma canza tuta.

Angudanar da Muzahar ne daga Fudiyya Ɗanja inda aka zagaya wani ɓangare na cikin garin ɗanja. Muzahar wadda tasami halartar wasu ba'adin ƴan uwa dake Da'ira Ɗanja Ayau asabar (16/8/2026) wadda yayi daidai da (3/3/1449).

Muna rokon Allah ya bamu albarkacin wanda ya sauka a wannan wata ma'ana Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (saww) ya darmu tare da Maulaya Sayyid Zakzaky (H) yasa ƙarshenmu yazamo shahada.

~Jawad Media Danja
26/8/2026
3/3/1449

SANARWA ❗‎‎بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيْمِ‎اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ‎‎وَمَا أَرْسَلْنَاك...
15/08/2026

SANARWA ❗

‎بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيْمِ
‎اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ

‎وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِينَ
‎ Suratul Anbiya - 107

‎السَّلامُ عَلَيكَ يا رَسولَ اللهِ وَرَحمَةُ اللهِ وَبَرَكاتُهُ

‎MUZAHARA MARABA TARE DA DA SAUYA TUTA ZUWA NA MAULUD | A FUDIYYA DANJA

‎ Ƴan Uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem Yakoub Al-Zakzaky (H) na Da'irar Danja.

‎ Suna farin cikin gayyatar Ɗaukacin Al'ummar Musulmi zuwa wajen Muzaharar maraba da watan Mauludin fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAWA), da kuma chanza tuta daga na Ashura zuwa na Mauludi.

‎WANDA ZAI GUDANA A YAU ... ASABAR Lokaci: 03:00 na Yamma
‎Wuri: Fudiyya Danja

‎Allah ya bada ikon Halarta Ilahee.

15/08/2026

Assalamu alaikum Ya Shuhada

ZIKIRA TUNA WA DA WAKI'AR BUHARI A DA'IRAR DANJA An gudanar da zikira ta tunawa da waƙi'ar Buhari wadda ta gudana shekar...
14/08/2026

ZIKIRA TUNA WA DA WAKI'AR BUHARI A DA'IRAR DANJA

An gudanar da zikira ta tunawa da waƙi'ar Buhari wadda ta gudana shekara 11 data gabata. Zikirar wadda aka gudanar a Fudiyya Ɗanja.

Zikirar wadda tasami halartar ƴan uwa da waɗanda abin ya rutsa dasu a zariya dukda yanayi na ruwa bai bada damar angunar da taron yanda yakamata ba.

an tattauna game da abinda ya faru tun daga gabari har abinda ya faru ya faru. Muna rokon Allah ya Tsinema duk wanda yakeda hannu a wannan waƙi'a. Muna kuma barar Salatin Annabi Hadiyya Zuwaga Ruhin Shahidanmu Kasatan na waƙi'ar Buhari.

✍️Muhsin Ibrahim Sabaty
PHOTO #

Waki’ar La’anannen Allah Buhari wacce ya aukar ranar daya ga watan maulud a garin zaria, ta bankade wasu abubuwa da yawa...
14/08/2026

Waki’ar La’anannen Allah Buhari wacce ya aukar ranar daya ga watan maulud a garin zaria, ta bankade wasu abubuwa da yawa a wannan kasa, waki’ar ta iya bude wa al’umnar da suke neman gaskiya subi idanu.

Sannan ta budewa wadanda keson bin karya idanu, duk mai hankali da son adalci a cikin zuciyar sa, idan yagani ko yasan ko yaji labarin me akayi a wannan waki’a tofa lallai zuwa yanzu zai dau matsaya!

Waki’ar tuni ta raba mana al’ummar wannan kasa gida biyu, masu tausayi da sanin ya kamata, da kuma marasa tausayi da rashin sanin ya kamata, wannan kuwa a fili yake ga dukkanin al’ummar duniya musamman na wannan Nagoya.

Da zarar kaga mutum na goyon bayan kisan kan da akayi a zaria ko waye ko daga ina yake kai tsaye turashi fannin wadanda basusan muhimmancin dan adam ba, akasin haka kuma kunsan ina zaku turashi.

Tahini bazai taba mantawa da wannan ranar ba ilal abad kuma za ai ta tunawa da wadanda s**ayi wannan kisa ana tsine musu albarka, sannan kuma za ai ta tunawa da wadanda aka kashe a matsayin gwaraza madaukaka.

Allah ya karawa buhari nauyin kasa.
Allah ya daga darajar shahidan mu.

Naziru Addarkawy
14 Aug, 2026.

TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH (S.A.W.A.) A DA'IRAR DANJA‎‎Danja — 12 ga Agusta, 2026‎‎A ranar Laraba, 12 ga Agusta, 202...
12/08/2026

TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH (S.A.W.A.) A DA'IRAR DANJA

‎Danja — 12 ga Agusta, 2026

‎A ranar Laraba, 12 ga Agusta, 2026, al’ummar Musulmi Ali majiran Sayyid zakzaky H na garin Danja sun gudanar da zaman juyayin na musamman domin tunawa da wafatin Manzon Allah Muhammad (S.A.W.A.), tare da tuno irin bakin cikin da iyalan gidansa s**a shiga a lokacin da rashin lafiyarsa ta tsananta har zuwa fitar ransa.

‎An gudanar da zaman juyayin ne daga ƙarfe 3:00 na rana zuwa 8:30pm na dare, bayan kammala sallar La’asar, inda mahalarta s**a hallara domin sauraron jawabi da darussa kan kwanakin ƙarshe na rayuwar Manzon Allah (S.A.W.A.) da kuma abubuwan da s**a biyo bayan wafatinsa.
‎Anfara ne da azah mai ratsa zukuta wanda matasa s**a jagoranta bayan nan sai ziyarar Annabi (SAWW) daganan kuma sai jawabin Malama Maryam Tukur bayan takammala sai jawabin jagora (H)

‎A cikin jawabinsa, ya mayar da hankali ne kan irin tsananin bakin ciki da Imam Ali (A.S.), Sayyida Fatima al-Zahra (S.A.), da sauran Ahlul Baiti (A.S.) s**a shiga yayin da rashin lafiyar Manzon Allah (S.A.W.A.) ke tsananta.

‎Ya bayyana yadda wannan lokaci ya kasance mai matuƙar raɗaɗi ga iyalan Annabi (S.A.W.A.), musamman ganin cewa suna fuskantar rabuwa da wanda shi ne jagora, uba, kuma Manzon Allah da s**a fi so.

‎Haka kuma, an saurari jawabin kan wasiyyar da Manzon Allah (S.A.W.A.) ya bari ga Imam Ali (A.S.), da irin nauyin da ya rataya a kansa bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W.A.).

‎Bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W.A.), ya yi bayani kan yadda Imam Ali (A.S.) ya kasance cikin waɗanda s**a jagoranci jana’izar Manzon Allah, ciki har da wanke shi,sa likkafani, gudanar da sallarsa da kuma binne shi.

‎Ya kuma nuna yadda wannan lokaci ya kasance ɗaya daga cikin mafi girman lokutan baƙin ciki a tarihin Ahlul Baiti (A.S.), domin rasuwar Manzon Allah (S.A.W.A.) ta kasance babban rashi ga al’ummar Musulmi baki ɗaya.

‎ An saurari jawabin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ne, wanda aka gabatar a matsayin babban darasin da ya ƙara haskaka abubuwan da s**a shafi kwanakin ƙarshe na rayuwar Manzon Allah (S.A.W.A.), dangantakarsa da Ahlul Baiti (A.S.), da kuma abubuwan da s**a faru bayan wafatinsa.

‎Jawabin ya kasance mai jan hankali, inda aka tunatar da mahalarta cewa tunawa da wafatin Manzon Allah (S.A.W.A.) ba wai kawai tunawa da wani tarihi ba ne, a'a, dama ce ta komawa ga koyarwarsa da kuma fahimtar matsayin Ahlul Baiti (A.S.) da rawar da s**a taka wajen kare saƙon Musulunci.

‎Zaman juyayin ya kasance cike da yanayin alhini da tunani, inda mahalarta s**a nuna girmamawa da juyayi ga Manzon Allah (S.A.W.A.) tare da tunawa da irin musibar da ta sami iyalansa bayan wafatinsa.

‎An kammala taron da addu’a ga Manzon Allah (S.A.W.A.), Ahlul Baiti (A.S.), da kuma addu’ar Allah Ya ƙara haɗa kan al’ummar Musulmi, Ya ba su ikon bin tafarkin ManzonSa da riƙe da koyarwarsa.

‎ # JawadmediaDanja — 12/08/2026

12/08/2026
SANARWA ❗‎‎إنَّا للهِ وَإنَّا إلَيهِ راجِعونَ 😭💔‎‎ZAMAN TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH (SAWA) A DA'IRAR DANJA. ‎‎  Ƴan M...
11/08/2026

SANARWA ❗

‎إنَّا للهِ وَإنَّا إلَيهِ راجِعونَ 😭💔

‎ZAMAN TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH (SAWA) A DA'IRAR DANJA.

‎ Ƴan Musulmi uwa Musulmi Almajiran Sayyid Yakoub Al-Zakzaky (H) na Garin Danja.

‎ Suna gayyatar da ɗaukacin Al'ummar Musulmi, zuwa wajen Tunawa da Wafatin Nabiyyur Rahma Annabinmu Muhammad Bin Abdullah (SAWA).

‎ Wanda zai Gudana in Allah ya kaimu Gobe.

‎ RANA: Laraba 28th ga Watan Safar 1448BH - 11th August 2026M
‎ LOKACI: 03:00 na Yamma
‎ WURI: Fuddiya Danja

‎ Ana tunatar da ƴan uwa akan sanya baƙin tufafi, domin alamta juyayi.

‎ Allah ya bada Ikon Halarta ... Ilahee 🤲.

Address

Danja
164

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jawad Media Danja posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jawad Media Danja:

Shortcuts

Share