Da'irar Danmaigauta

Da'irar Danmaigauta Domin yadda abubuwan da s**a shafi addini, da'irar Danmaigauta, da Harkar muslumci a Nigeria.

JAGORA (H) YA GANA DA DALIBAN KARBALA Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)Cikin daren yau Talata 29 ga Almuha...
15/07/2026

JAGORA (H) YA GANA DA DALIBAN KARBALA

Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Cikin daren yau Talata 29 ga Almuharram 1448 (14/7/2026), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da 'yan uwa almajiransa da suke karatu a Hauzozin Karbala mai tsarki a ƙasar Iraq.

Yayin da yake jawabi ga daliban, Jagora (H) ya bayyana Shahadar Sayyid Khamenei (RH) wadda ta auku a watan Shahadar Amirulmumin (AS), wato watan Ramadan, kuma aka bizne shi a daren Shahadar Imam Zainul Abidin (AS) a matsayin wani abu na hikimar Allah Ta'ala, wanda bai zama bisa hadari ba. Yace, wannan kuma ya nuna hanyar dai kenan, hanyar Shahada wadda ta kiɗima maƙiya, s**a kasa ganewa.

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana yadda kullum makiya ke ganin kamar in s**a kashe A'alam daga cikin mutane, kamar sun kashe addini ne. Inda ya nanata maganar da ya wa wasu jami'an tsaro bayan Wakiar Buhari. Yace, “Ku a tsammaninku in kun kashe mutum za ku kawar da abu ne. To da kashe wani mutum zai kawar da Shi'a, to da wannan mutumin Imam Husaini (AS) ne. To amma kashe shi sai ya tambatsa Shi'a.”

Jagora ya bayyana cewa, har yanzu al'amarin haka yake, duk abinda maƙiya s**a yi, sai dai su tambatsa. Yace: "Ballantana ni ƙaramin alhaki, wanda in kun kashe ni, sai dai ku ƙara yawan Shahidan Karbala.”

Ya bayyana yadda tunanin makiya ya nuna musu cewa, in sun kashe Sayyid Khamenei shi kenan. “Maimakon haka, sai s**a ga sun raya shi ne.”

Da ya juya bangaren nasiha ga daliban, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana musu cewa, dukkansu, maza da mata da yaransu sun zo diban ruwa ne, za su je su shayar da gida. “Don a gida ana matukar kishin ruwa (na ilimin tafarkin Ahlulbait (AS).

Ya bayyana yadda tsawon zamani aka haramta ma yankinmu sanin tafarkin Ahlulbaiti (AS), yace, amma yanzu cikin garejen lokaci abin yana haɓɓaka.

Jagora (H) ya kawo misalai na irin dakewar Amirulmumin (AS) a tarihi, da kuma yadda mabiyansa a jiya da yau s**a kasance jarumai wajen bayar da kariya ga addinin Musulunci. Yace: “(Wannan shi ne Tafarkin waɗanda suke dakewa, waɗanda su a wurin su a kashe ka a tafarkin Allah ɗaukaka ce.

“Darajan wanda aka kashe a cikinmu, yana zama ne daram a zukatanmu, tasirinsa ma sai ya fi (yawa) bayan Shahadarsa, fiye da lokacin da yake da rai, kamar yadda muka gani a Shahadar Sayyid Qa'id, wanda da yawan mutane sai bayan Shahadar shi s**a gane waye wannan bawan Allah din.”

Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jaddada cewa: “Wannan makaranta ta sadaukarwa (ita ce kawai mafita). Duk wani wanda zai ce maka akwai wata dabara, ko wata hanya ta daban, ko wani yanke, wanda akan bi cikin sauƙi a cimma nasara, to kace da shi, in dai dabara ce, da Imam Husaini (AS) ya yi wannan dabaran, da sauran mabiyansa ma sun yi dabaran. Har ma yanzu abinda muke gani, da abin dabara ne, shi ma sai mu ce, da Sayyid Qa'id shi ma sai ya yi dabara. Amma al'amarin sadaukarwa ne. Tsayawa ne ƙyam a tafarkin Allah, sai dai Allah ya yi hukuncin.”

Sayyid Zakzaky ya jaddada cewa: “Kuma mun san cewa muna da wani garanti, mun san cewa ba yadda za a yi a murkushe mu. Mu fa ba masu murƙusuwa ba ne. Ba kawai ba za mu murƙusu ba ne, mu ne ma masu murƙushewa. Nasara tamu ce, ko mutum ya ƙi, ko ya so, don muna tare da Wanda ke ba da nasara. Insha Allah.”






29/Muharram/1448
14/07/2026

13/07/2026
TAƘAITACEN TARIHIN FUTOWAR IMAMU HUSSAINI (AS) DAKA MADINA ZUWA MAKA ZUWA KARBALA.(1) - FITOWARSA DAGA MADINA ZUWA MAKAH...
19/06/2026

TAƘAITACEN TARIHIN FUTOWAR IMAMU HUSSAINI (AS) DAKA MADINA ZUWA MAKA ZUWA KARBALA.

(1) - FITOWARSA DAGA MADINA ZUWA MAKAH

A ranar (28 ga Watan Rajab, Shekara ta 60 Bayan Hijira)
Bayan rasuwar Mu'awiya l.a, ɗansa Yazid ya karbi mulki kuma ya bukaci gwamnan Madina da ya tilasta wa Imam Husaini (AS) ya yi masa mubaya'a (biyayya).

- Dalilin barinsa Madina: Imam Husaini (AS) ya ki amincewa da zaluncin Yazidu, inda ya bayyana cewa "mutum irinsa ba zai taba yi wa mutum irin Yazid mubaya'a ba".

- Tafiyar Sirri: Domin kare jinin al'umma da kuma kin mika wuya ga zalunci, Imam Husaini (AS) ya bar garin kakansa (Madina) da daddare, tare da iyalansa da sahabbansa, ya nufi birnin Makka.

(2) - ZAMA A BIRNIN MAKKA.
Daka (3 ga Watan Sha'aban zuwa 8 ga Watan Zul-Hijjah)
Imam Husaini (AS) ya isa Makka kuma ya zauna a can na tsawon kimanin watanni hudu.

-Wasiku Daga Kufa:* A lokacin da yake Makka, labari ya bazu cewa Imamu Husaini as ya ki yi wa Yazidu mubaya'a. Mutanen garin Kufa (da ke Iraki) s**a fara aiko masa da dubun-dubatar wasiku suna cewa: *"Ba mu da Imami, ka zo mu yi maka mubaya'a ka jagorance mu."*

Sai Imamu Husaini as ya aika Muslim bin Aqil: Don ya tabbatar da gaskiyar lamarin, Imam ya aiki dan uwansa Muslim bin Aqil zuwa Kufa. Muslim ya isar da rahoton cewa mutane dubbai sun yi mubaya'a kuma suna jiran isowar Imam Husaini as zuwa kufa.

-Barazanar Kisa a Makka: Yayin da lokacin aikin Hajji ya gabato, Yazidu l.a ya turo dakarun sirri don su kashe Imamu Husaini (AS) koda a dakin Ka'aba s**a sameshi. don kare alfarmar dakin Allah, Imam Husaini as ya canza aikin Hajjinsa zuwa Umrah, kuma ya yanke shawarar barin Makka ranar 8 ga watan Zul-Hijjah (Ranar Tarwiyyah).

(3) - TAFIYAR IMAMU HUSAINI AS ZUWA KUFA (IRAQI)

Imam Husaini (AS) ya fito daga Makka ya nufi Kufa. Hanyar tana cike da darussa da sauye-sauye:

-Labarin Shahadar Muslim bin Aqil: Suna cikin tafiya a hanya, labari ya riski IMAM Husaini as cewa sabon gwamnan Kufa (Ubaidullah bin Ziyad) ya tsoratar da mutanen Kufa, sun juya wa Muslim bin aqil baya, kuma an kashe Muslim bin Aqil da Hani bin Urwah.

-Taron Jama'a: Bayan jin wannan labari, Imam ya shaida wa wadanda ke biye da shi halin da ake ciki, inda ya ba kowa damar komawa idan suna tsoron mutuwa. Da yawa daga cikin wadanda s**a bi shi don neman dukiya ko mukami s**a rarrabe, s**a juy, ya rage daga shi sai sahabbansa na kusa da iyalansa.

-Haduwa da Rundunar Hurr bin Yazid Al-Riyahi: Kafin su karasa Kufa, runduna ta farko ta makiya karkashin jagorancin Hurr ta tare Imam Husaini (AS). Hurr an bashi umarnin kada ya bar Imam Husaini as ya koma Madina kuma kada ya kyale shi ya shiga Kufa, sai dai ya tura shi zuwa wani waje da babu kariya.

(4)-ISOWAR IMAMU HUSAINI DA SAHABANSA DA IYALANSA KASAR KARBALA.
a ranar (2 ga Watan Muharram, Shekara ta 61 Bayan Hijira)
Sakamakon matsin lamba daga rundunar Hurr, Imam Husaini (AS) da iyalansa sun sauka a wani waje da ake kira *(Karbala) (kasar da Imam ya ambata cewa ita ce kasar "Karb" [bakin ciki] da (Bala'i).

ABUBUWAN DA SU FARU A KARBALA

-Ranakun su na Fari a Karbala : Daga ranar 2 ga watan Muharram, Imam ya kafa tantunansa.

-Kewaye Ruwa: Bayan 'yan kwanaki (ranar 7 ga Muharram), dakarun Umar bin Sa'ad (wadanda Ibn Ziyad ya turo) s**a canza Sheka daka inda suke tsaye zuwa kewaye kogin Furat, s**a hana iyalai da yaran Imam Husaini (AS) shan ruwa.

Hu Haɗu a Rubutu na gaba

Usama Aminu ✍️

MAHIMANCIN HALARTAR ZAMAN MAKOKIN IMAMU HUSAINI AS. Makokin juyayin Imamu Husaini as ba kawai taruka ne na al'ada da ke ...
18/06/2026

MAHIMANCIN HALARTAR ZAMAN MAKOKIN IMAMU HUSAINI AS.

Makokin juyayin Imamu Husaini as ba kawai taruka ne na al'ada da ke shudewa ba, a'a, makaranta ce ta tunani da tarbiya, wanda ahalu baiti s**a yi kwadayin dasawa da kafawa, kuma s**a yi kira ga mabiyansu (Shi'a) da su raya su, saboda girman tasirinsu wajen kiyaye addini da sabunta mubaya'a da biyayya.

Ga Wasu Hadisai daka Aimma tsarkaka game da falala da mahimmancin halartar Majlisin tunawa da imamu Husaini as da sahabansa da 'ya' yansa.

(1) - RAYAR DA AL'AMARIN AHALUL BAITI AS,
A'imma sun dauki zama a wadannan taruka a matsayin rayar da addini da dabi'un da Imamu Husaini ya sadaukar da ransa a kansu.

Daga Imamu Ja'afar al-Sadiq (a.s): Ya fada wa Fudhail bin Yasar: "Kuna zama kuna tattaunawa?" Sai ya ce: Eh raina fansa gareka (haka ne). Sai Imamu ya ce: "Lallai wadannan taruka ina kaunarsu, saboda haka ku rayar da al'amarinmu. Ya Fudhail, wanda duk ya ambace mu, ko aka ambace mu a gurinsa sai hawaye ya fita daga idonsa koda gwargwadon fiffiken sauro ne, Allah zai gafarta masa zunubansa koda sun kasance sun kai kumfar teku."

( 2)-SAMUN CETO SAYYIDA FADIMA SA,
Ruwayoyi sun tabbatar da cewa tsayar da juyayi, ta'aziyya ce ga Manzon Allah (s.a.w) da kuma iyalan gidansa tsarkaka, musamman Sayyida Fatima sa.

Daga Imamu al-Sadiq (a.s): "Lallai Fatima 'yar Muhammad (s.a.w) tana halartar wurin masu ziyarar kabarin danta al-Husain (a.s) tana nema musu gafarar zunubansu."

Kuma a wadansu ruwayoyin, nassoshi sun nuni da cewa masu kuka da masu tsayar da juyayi imamu Husaini as suna cikin addu'arta mai daraja.

(3)- Ra'ya Zuciya da Rashin Mutuwarta
A lokacin fitinu da rudun duniya na abun duniya, tarukan juyayi suna kasancewa matattarar ruhi ce da ke kiyaye lafiyar zuciya da tsarkinta.

Daga Imamu Ali bin Musa al-Rida (a.s): "Wanda duk ya zauna a zaman da ake rayar da al'amarinmu a cikinsa, zuciyarsa ba za ta mutu ba a ranar da zukata ke mutuwa."

(4)-Sakamako Mai Girma da Lada Mai Yawa ga Kuka da Sanya Kuka
A'imma sun mayar da hankali kan bangaren shauki na nuna baƙin Ciki da alakar zuciya da masifar Karbala, kuma sun sanya wa hawaye na gaskiya matsayi mai girma.

Daga Imamu Muhammad al-Baqir (a.s): Wajen kwadaitarwarsa kan juyayin Husaini a ranar Ashura a cikin gida je ya ce:
"Sannan ya kamata ya koka wa Husaini ya kuma yi kuka a kansa, kuma ya umarci wanda ke cikin gidansa da su yi kuka a kansa... kuma su riga suna yi wa juna ta'aziyya saboda masifarsu ta al-Husain (a.s)."

Daga Imamu al-Rida (a.s) zuwa ga Ibn Shabib:
"Ya kai Ibn Shabib, idan ka kasance mai kuka ne ga wani abu, to ka koka wa al-Husain bin Ali bin Abi Talib (a.s), domin lallai shi an yanka shi kamar yadda ake yanka rago... Ya kai Ibn Shabib, idan yana faranta maka rai ka kasance tare da mu a cikin darajoji madaukaka na gidajen aljanna, to ka yi bakin ciki saboda bakin cikinmu, kuma ka yi farin ciki saboda farin cikinmu."

Usama Aminu✍️

18/06/2026

مِثْلِي لَا يُبَايِعُ مِثْلَ يَزِيد

Ma'ana:

Mutum Irina ba zai yi mubaya'a ga wani kamar Yazidu ba.

Wannan itace huɗubar ƙarshe ta Shaheed Imam Khamene'i (QS) kafin shahsdarsa, wacce aka sanar a matsayin taken Ashura da Arba’in na wannan shekarar.

Allah ya amshi shahadarsu ya tashesu cikin shahidan Karbala.

عظَّم اللَّه أجورنَا وأجوركم بِمصابِنَا بِالْحسينِ "عليه السلام"، و جعلَنَا و إِياكم مِنَ الطالِبِينَ بِثَأرِهِ معَ ولِيهِ و الْإِمامِ المهدِيِّ مِن آلِ محَمدٍ







02/Muharram/1448
17/06/2016

Address

Danmaigauta
Danja

Telephone

+9647840313248

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Da'irar Danmaigauta posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Da'irar Danmaigauta:

Shortcuts

Share