24/10/2025
ALAMONIN KYAKYAWAN QARSHE GUDA BIYAR.
Alama Ta Farko :
Musulmi yana mutuwa ne da gumin Goshi, MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCI YACE " Mumini yana mutuwa da gumi a Goshin sa.
Alama ta Biyu :
Musulmi ya Mutu cikin Daren JUMA'A ko a cikin Yinin JUMA'A, MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCI YACE" : Ba wani Musulmi da zai mutu ranar JUMA'A ko Daren JUMA'A face sai ALLAH ya tsare shi daga fitinar Kabari".
Alama ta Uku :
Mutum ya mutu da Kalmar Shahada Kafin Mutuwar sa, MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCI YACE " : Duk Wanda Kalmar sa ko maganar sa ta qarshe a duniya ta kasan ce , LA ILAHA ILLALLAH, Zai shiga Aljannah insha Allah.
Alama ta Hudu :
Wanda yayi Mutuwar Shahada, Ba mutuwa a fagen yaqi kadai ake nufi da mutuwar Shahada ba, Annabi Muhammad TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARESHI ya bayyana cewa duk Wanda ya mutu ta sanadin qunar wuta, Ko ya dulmiye a Ruwa ya mutu, ko Ciwon ciki ko haihuwa ko Annoba, ko ya Mutu yana qoqarin kare kansa da mutuncinsa ko dukiyar sa wannan YAYI Mutuwar Shahada.
Alama ta Biyar :
Mutum ya Mutu yana kan aikata wata ibadah, Misali ya kasance yana Sallah, ko Azumi ko ya fita zuwa Muhadara ta addini, MANZON ALLAH YACE": Idan Allah na nufin bawan sa da ALKHAIRI saiya tsarkake shi kafin Mutuwar sa, Sahabbai s**a ce menene tsarkake shi? Annabi TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARESH YACE " Allah zai kinsa masa son ibadar a zuciyar sa ya riqa aikatata har ALLAH ya karbi Rayuwar sa...
Allah kasa Karshen mu Yayi kyau mu dace da shiga Aljannatul Firdausi.
Allah ka Karba Mana ibadunmu ka yafe mana Zunuban mu.
Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum