08/09/2022
Labaran Safiyar Alhamis 08/09/2022CE - 11/02/1444AH.
Sep 08, 2022
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kashe wani malamin addinin musulunci a jihar Ebonyi.
Gwamna Bunin a jihar Yobe ya bai wa matan Marigayi Sheikh Goni Aisami gidaje 3.
Kananan ‘yan sanda sun yi zanga-zanga kan rashin biyansu albashi a jihar Osun.
Gwamna Zulum ya bayar da umurnin daukan ma’aikatan lafiya 30 a asibitin Bama
‘Yan sanda a jihar Gombe sun k**a wani mutum da ya yi wa wata yarinya fyade a makabarta.
Hukumar DSS ta tabbatar da cewa mai shiga tsakanin ‘yan bindiga da wadanda aka sace a harin jirgin kasar Abuja-Kaduna, MAmu yana hannunsu.
Gwamnatin Tarayya ta shirya kara yawan iskar gas din da ake kai wa Turai.
Napoli ta sami nasara a kan Liverpool da ci 4-1 a wasan jiya na zakarun Turai.