
15/07/2022
ILLAR SHAYE-SHAYE GA AL'UMMAR MU MUSAMMAN SHUWAGABANNI NA SIYASA - SHIN INA MATSALAR TAKE?
Matsalar Shaye-shaye musamman ga Shuwagabanni da matasa a wannan zamani matsala ce babu dan talaka, babu dan mai kudi, babu dan malamai, babu mace babu namiji, ta shafi kowa, hantsi ce data leka kowane gida, idan babu dan gidanku akwai dan ahalinku ko makocinku, a haka abin har yakai ga Shuwagabanni da masu madafan iko a cikin Al'umma.
Babban abin damuwar shi ne idan kana tunanin naka baya ciki, to abu ne me sauki abokai su yaudare shi ya tsunduma, babu maganar shaye-shaye a loko ko a kango, yanzu babu jami’a babu sakandare, ko ina zaka iya ganin matashi k**arka, k**ata/k**arki a cikin wannan harka ta Shaye-shaye.
Tabbas Idan har muka ce kullum sai dai mu ta magana akan siyasa, cin hanci ko tsokanar juna, to muna gani al’umar mu kullum za su yi ta fadawa cikin halaka, kuma muna da gudummawar da za mu bayar amma munyi shiru saboda idan jifa ya wuce kan ka kawai ya fada kan kowa.
Lokutta dayawa Iyaye na cikin gida basu san abin da ke faruwa ba a dakunan yaran su, a haka yaran kullum ke girma cikin dabi’ar maye, daganan kuma har tabi jikinsu, shikenan sai suja ra’ayin abokanan su, a haka Al’ummar mu kullum ke afkawa cikin bala’i da masifu a dalilin ta'ammali da miyagun kwayoyi iri daban daban.
Ya zama wajibi gare mu mu saka ido akan masu chemists na unguwanni, haka suma iyaye da Al'ummar unguwanni su bada hadin kai wajen taimakawa da bayanan sirri ga hukumomi masu alhaki a wannan bangrw domin ganin an shawo karshen matsalar Shaye-shaye domin samun Shuwagabanni nagari a cikin Al'umma.
A dalilin haka muka samar da Gidauniya mai zaman kanta "Youth Initiative Forum Against Drug Abuse and Human Trafficking, (YIFDAT)" kungiya ce mai wayar da Kan Al'umma akan Illolin Shaye-shaye da safarar mutane a cikin Al'umma, kofa a bude take kai da ke ku shigo domin bada taku gudunmuwar. Mungode!
✍🏼 Rubutawa:
Comr. Usman H. Rafukka
National Secretary, YIFDAT
Katsina State - 15/07/2022.