15/08/2026
APPRECIATION TO DAKOBA FOR THE COMMUNITY HEALTHCARE SUPPORT INITIATIVE ON MY BEHALF
Zan yi amfani da wannan dama wajen miƙa godiyata ta musamman ga Ƙungiyar Abokan Karatuna (Classmates), Dawakin Kudu Old Boys Association Class of 2004 (DAKOBA), bisa gagarumar gudummawar da s**a bayar ta samar da katunan rubuta magani (Outpatient Cards) masu ɗauke da hotona da sunana, waɗanda aka bayar a Dawakin Kudu General Hospital domin tallafawa Marasa Lafiya
Nagode ƙwarai da gaske da wannan karamci da goyon baya. Allah Ya saka da alheri, Ya ƙara haɗin kai da zumunci a tsakaninmu.
Allah Ya bar zumunci. 🤲
HON. MUSA GUDA
MUSAN MATASA
15TH AUGUST, 2026