19/10/2025
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakanin Hamas da Isra’ila, Isra’ila ta kai hare-hare da dama a Gaza.
Daga Shaheed Abdulrahman Bala Idries
ABS Radio — 19 ga Oktoba, 2025.
Hukumar kashe gobara ta Falasɗinu a Gaza ta ce jerin hare-haren jiragen saman Isra’ila da aka kai a ranar Lahadi sun kashe aƙalla mutum 21 a cikin yankin da ke ƙarƙashin kulle, wanda hakan ke nuna sabon take hakkin yarjejeniyar tsagaita wuta.
Mai magana da yawun hukumar, Mahmud Bassal, ya ce mutum shida daga cikin waɗanda aka kashe sun rasu ne lokacin da harin Isra’ila ta kai akan gungun wasu Falasɗinawa a garin Al-Zawayda da ke tsakiyar Gaza.
Wata mace da yara biyu sun mutu lokacin da jirgin yaki mara matuki (drone) ya kai hari kan tanti da ke zaune da ‘yan gudun hijira a kusa da Asdaa City, arewacin Khan Yunis.
Mutane biyu kuma sun mutu, wasu da dama sun ji rauni a wani harin Isra’ila da aka kai a yammacin garin Al-Zawayda da ke tsakiyar Gaza.
A wani harin dabam, mutane biyu sun mutu kuma wasu sun ji rauni lokacin da harin Isra’ila ya auka kan tanti a yankin Al-Ahli Club a Nuseirat, tsakiyar Gaza, in ji Bassal.
Haka kuma wasu mutane biyu sun mutu a wani harin jiragen saman Isra’ila a gabashin Jabalia, arewacin Gaza, in ji shi.
Isra'ila ta take hakkin yarjejeniyar tsagaita wuta sau da dama.
Hamas ta zargi Isra’ila da take yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza akai-akai, inda ta kashe aƙalla Falasɗinu 46 tun bayan fara yarjejeniyar a ranar 10 ga Oktoba.
“Dakarun mamayar Isra’ila sun yi niyyar kai hari kan fararen hula kuma s**a bude musu wuta a wuraren da aka ba da damar motsi, lamarin da ya jawo mutuwar mutane 46 da raunata wasu 132,” in ji sanarwar.
Hamas ta ce galibin waɗanda s**a mutu yara ne, mata da tsofaffi, ciki har da iyalin Abu Shaban waɗanda aka ce “duk sun mutu baki ɗaya, ciki har da yara bakwai da mata biyu.”