
13/03/2025
Ƙungiyoyin mata sama da 100 sun baiwa Akpabio da majalisar dattawa hakuri akan zarge-zargen Natasha
Kungiyar mata ƴan gwagwarmaya ta ƙasa, NWCGG, mai wakiltar kungiyoyin mata 100, ta mika sakon dannar ƙirji ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kuma majalisar dattawan Najeriya kan zargin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi.
Sun mika sakon hakurin ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a Jiya Talata.
Da ta ke magana a madadin kungiyoyin, Dokta Cecilia Ikechukwu ta yi Allah-wadai da zarge-zargen Sanata Natasha, inda ta bayyana hakan a matsayin "cin mutunci da rashin ta-ido"
A cewarta, abin da Natasha ta yi ya jawo wa matan Najeriya abin kunya tare da kawo cikas ga kokarin mata ‘yan siyasa da s**a yi aiki tukuru don samun amana da mutunta ‘yan Najeriya.