Duniyar Tarihi Tv

Duniyar Tarihi Tv Arewa

Wato rayuwar nan abar tsoro ce 😭Kuduba yadda rayuwar jaruma Ummi Nuhu ta koma Allah sarki. Ance sunyi lokaci tare da su ...
25/07/2025

Wato rayuwar nan abar tsoro ce 😭
Kuduba yadda rayuwar jaruma Ummi Nuhu ta koma Allah sarki.

Ance sunyi lokaci tare da su hadiza kabara
Rukayya Dawayya
da sauran su
Amman se naga ita ta tsufa akan su😭
Se kuma na tuna cewa ba iya shekaru kesa tsufa ba
tashin hankali ma yana iya jawo tsufa

Duk me fama da damuwa Allah ka yaye mashi alfarmar manzo SAW.
Ameen 🤲

Ganganci ko Tsautsayi
24/07/2025

Ganganci ko Tsautsayi

Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto (1909 – 1966), Shahararren dan Najeriya ne kuma daya daga cikin jigo a tarihin siyasar...
22/07/2025

Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto (1909 – 1966), Shahararren dan Najeriya ne kuma daya daga cikin jigo a tarihin siyasar kasar nan, Laƙabin gida, haifaffen Rabah, wanda a halin yanzu ake kira Jihar Sakkwato, ya kasance daga cikin Sarakunan Fulani, kuma zuriyar Usman Dan Fodio ne kai tsaye, wanda ya kafa Daular Sakkwato. Majagaba a matsayi da kuma zamanin mulkin mallaka a tarihin Najeriya

Sir Ahmadu Bello ya yi karatunsa ne a fannin ilimin addinin musulunci na gargajiya, sannan ya halarci makarantar Middle School ta Sokoto. Ya shiga harkar siyasa ne a karshen shekarun 1940, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar NPC ta Arewa a shekarar 1951, wadda aka kafa ta domin inganta muradun yankin arewacin Najeriya.

A matsayinsa na Firimiyan Arewacin Najeriya daga shekarar 1954 zuwa 1966, Bello ya taka rawar gani wajen ci gaban yankin, da bayar da shawarwari kan harkokin ilimi, bunkasa noma, da zamanantar da jama'a, tare da inganta dabi'un Musulunci. Ya yi kokarin daidaita al’adun gargajiya da tsarin mulki na zamani, wanda ya haifar da gagarumin ci gaban tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa a Arewacin Najeriya.

Tasirin Bello ya wuce siyasar gida; ya kasance jigo a fagen ‘yancin kai na Nijeriya, ya kuma yi kokarin tabbatar da dunkulewar Nijeriya, ko da yake ana yawan kallonsa a matsayin mai wakiltar muradun Arewa. Abin takaici, an kashe shi ne a lokacin juyin mulkin da aka yi a watan Janairun 1966, wanda ya zama wani gagarumin sauyi a fagen siyasar Najeriya. Har yanzu ana jin tarihinsa a Najeriya, musamman a yankunan Arewa, inda ake tunawa da shi a matsayin shugaba mai hangen nesa kuma alama ce ta hadin kan Arewa.

tarihi 'adu

ME YASA SHUGABANNIN AREWA KAWAI?An kashe Sir, Ahmadu Bello Sardauna Da Sir, Abubakar Tabawa Balewa a ranar 15 ga Janairu...
22/07/2025

ME YASA SHUGABANNIN AREWA KAWAI?

An kashe Sir, Ahmadu Bello Sardauna Da Sir, Abubakar Tabawa Balewa a ranar 15 ga Janairu 1966. Dakarun sojojin Najeriya da ke karkashin jagorancin Major Chukwuma kaduna da Samuel Ifeanjuna.

Dimka da Bisala ne s**a kashe Janar Murtala Ramat Muhammad a ranar 13 ga Fabrairu 1976.

Janar Sani Abacha 1943- 1998. Dalilin mutuwar wasu sun ce guba.

Umaru Musa Yar’Adua 2010. Sanadin rasuwa haka da Janar Muhammadu Buhari.

Allah ya jikan su da rahama.

'Yammatan Sudan ta kudu🔥🔥
21/07/2025

'Yammatan Sudan ta kudu🔥🔥

R.I.P UMAR MUSA YAR'ADUABaza mu iya mantawa da kaiba, Allah ya jikanka da rahama Ameen 🤲 ya Allah.
21/07/2025

R.I.P UMAR MUSA YAR'ADUA
Baza mu iya mantawa da kaiba, Allah ya jikanka da rahama Ameen 🤲 ya Allah.

Marigayi tsohon shugaban Nijeriya Mallam Umaru Musa Yar'adua tareda tsohon ministan Abuja Dr Aliyu Modibbo Umar a wata s...
21/07/2025

Marigayi tsohon shugaban Nijeriya Mallam Umaru Musa Yar'adua tareda tsohon ministan Abuja Dr Aliyu Modibbo Umar a wata sallar idi a birnin Abuja.
Allah ya jikan Matawalle.
Ameen 🤲

Ameen 🤲

Wannan shine Muhammad Ghaddafi Tsohon shugaban kasar libya Shine shugaba mafi  iya mulkin da adalci da kyautatawa a nahi...
21/07/2025

Wannan shine Muhammad Ghaddafi Tsohon shugaban kasar libya
Shine shugaba mafi iya mulkin da adalci da kyautatawa a nahiyar afrika.

A shekara 1951 kasar Libya ita ce kasa mafi talauci a duniya, amma da zuwan Gaddafi saida ya sanya kasar ta zama kasa mafi ci gaba a nahiyar afrika baki daya, domin a lokacin mulkinsa an rawaito cewa idan saurayi ya tashi yin aure za'a bashi gida sannan a bashi gudunmawa mai tsoka a bashi aikinyi, sannan kasace mai maturkar saukin rayuwa haka nan yasa baki musamman yan nijar da nigeria suke zuwa.

A lokacinsa Libya tana daya daga cikin manyan kasashen mafiya arziki a duniya amma daga karshe sabo da butulci irin na dan adam a shekara ta 2011 yan kasar Libya da hannunsu s**a bada gudummawar kashe ghaddafin suna gani ana jan gawarsa akasa 😭😭😭

Marigayi shugaban Nijeriya Janar Sani Abacha tareda shugaban kasar Libya Kanar Muammar Gaddafi. Allah ya jikansu da rahm...
21/07/2025

Marigayi shugaban Nijeriya Janar Sani Abacha tareda shugaban kasar Libya Kanar Muammar Gaddafi.
Allah ya jikansu da rahmah.

Tinubu Ne Zabinmu A Zaben 2027, Cewar Sarkin DauraSarkin ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakoncin Uwargidan Shug...
21/07/2025

Tinubu Ne Zabinmu A Zaben 2027, Cewar Sarkin Daura

Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakoncin Uwargidan Shugaban Kasan, Remi Tinubu a fadarsa.

Amma a haka kullum maza suke cewa sune suke tsada🤔🤣Inji Hajiya Maimuna Idris Sani Beli
21/07/2025

Amma a haka kullum maza suke cewa sune suke tsada🤔🤣

Inji Hajiya Maimuna Idris Sani Beli

Wannan shine Blackwood, ɗaya daga cikin mafi tsada kuma mafi ƙarancin itace a duniyaHaka nan ana kiransa da "baƙin zinar...
21/07/2025

Wannan shine Blackwood, ɗaya daga cikin mafi tsada kuma mafi ƙarancin itace a duniya

Haka nan ana kiransa da "baƙin zinaren gandun daji"

Saboda tsananin launin baƙinsa da taurinsa na musamman s**a sa ya zama abin sarrafawa a cikin masana'antu da yawa, kamar kera kayan kiɗa da kayan ɗaki masu kyau

Ana samun wannan itace na Blackwood a ƙasashe kamar Tanzania, Mozambique da Zimbabwe

Address

Dutse

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniyar Tarihi Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category