TTN Hausa

TTN Hausa TTN Hausa kafa ce mai zaman kanta da aka samar don kawo sahihan labarai da rahotanni cikin harshen Hausa.

Ku tura mana sakonninku ta WhatsApp a +234 703 662 1583

Ku bi channel dinmu: https://whatsapp.com/channel/0029VbAuIz77dmebznWVa31L

09/09/2026


Naira dubu dari da goma a matsayin mafi ƙarancin albashi, gina asibitocin kwararru guda 21, da kuma amfani da jirage marasa matuki wajen yaƙar ‘yan bindiga — waɗannan na daga cikin manyan alkawuran da ’yan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a Arewa maso Yamma s**a yi gabanin zaɓen 2027.

08/09/2026


Mashigin Hormuz na dab da zama sabon fagen rikici — Iran ta ce za ta samar da wani iyakancaccen sabon yanki mai tsauraran dokoki, lamarin da ka iya ƙara dagula zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma kasuwar man fetur ta duniya.

07/09/2026


Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da nadin Dr Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin sabon Sarkin Gumel, bayan rasuwar mahaifinsa, Marigayi Sarkin Gumel na 16, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani na biyu. Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin ne bisa shawarar masu naɗa sarki na Masarautar Gumel da kuma Majalisar Sarakunan Jihar.

 Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya amince da naɗin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Gumel na 17, bayan rasu...
06/09/2026


Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya amince da naɗin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Gumel na 17, bayan rasuwar mahaifinsa, Alhaji Ahmed Muhammad Sani II. Naɗin ya biyo bayan shawarar Masu Zaɓen Sarkin Gumel da Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa. Kafin naɗinsa, shi ne Chiroman Gumel, sannan Daraktan Tsaron Intanet a NITDA. Ya yi karatun digirin-digirgir a fannin Computer and Communication Systems Engineering, tare da gogewa a ilimi, bincike da tsaron intanet.

Karanta cikakken labarin a comments:

06/09/2026


Jam’iyyar ADC, ta fitar da jerin ‘yan takararta na gwamna da mataimakin gwamna a jihohi 28 domin zaɓen shekarar 2027. Jerin da Sakataren Yada Labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ya ƙunshi wasu fitattun ‘yan siyasa da tsofaffin jami’an gwamnati.

  Hedikwatar Tsaron Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 36 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ƴan ta’adda a...
05/09/2026


Hedikwatar Tsaron Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 36 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ƴan ta’adda a ayyukan soji da aka gudanar tsakanin 31 ga Agusta zuwa 3 ga Satumba a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Karanta cikakken labarin a comments:

  JAMB ta fitar da sak**akon UTME na 2026 ga ɗaliban da ba su kai shekara 16 ba. Za su iya duba sak**akon ta hanyar aika...
05/09/2026


JAMB ta fitar da sak**akon UTME na 2026 ga ɗaliban da ba su kai shekara 16 ba. Za su iya duba sak**akon ta hanyar aika kalmar “RESULT” zuwa 55019 ko 66019, amma JAMB ta ce samun sak**akon ba ya tabbatar da samun gurbin karatu.

  Nasiru Musa Idris ya zargi Sheikh Ahmad Gumi da tsoma baki a aurensa da wata ƴar Morocco tare da hana binciken abin da...
05/09/2026


Nasiru Musa Idris ya zargi Sheikh Ahmad Gumi da tsoma baki a aurensa da wata ƴar Morocco tare da hana binciken abin da ya bayyana a matsayin ɓacewar matarsa. Gumi ya musanta zargin, yana mai cewa zai kai Idris kotu bias zargin ɓata masa suna.

  Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta k**a mutane 22 da ake zargi da canza salon suturar jinsunsu a wasu sassan jihar....
05/09/2026


Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta k**a mutane 22 da ake zargi da canza salon suturar jinsunsu a wasu sassan jihar. Hukumar ta ce waɗanda aka k**a sun haɗa da mata 10 da maza 12, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

  Gwamnatin Jihar Plateau ta ba da umarnin rufe makarantun firamare da sakandare daga Litinin, 7 ga Satumba, domin daƙil...
05/09/2026


Gwamnatin Jihar Plateau ta ba da umarnin rufe makarantun firamare da sakandare daga Litinin, 7 ga Satumba, domin daƙile yaɗuwar cutar diphtheria. Aƙalla mutane 23 sun mutu, yayin da ake zargin mutane 148 sun kamu da cutar.

Address

Sani Abacha Bypass
Dutse
720101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TTN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to TTN Hausa:

Shortcuts

Share