TTN News Hausa

TTN News Hausa TIMES HAUSA, jarida ce ta Hausa da aka samar domin samar da sahihan labarai kan harkokin siyasa, ilimi, kasuwanci, tattalin arziki, lafiya, da sauransu.

Za a ɗauki ma’aikatan lafiya 20,000, kaso 60% nas da ugozoma ne, za a kuma inganta aikinGwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da...
10/10/2025

Za a ɗauki ma’aikatan lafiya 20,000, kaso 60% nas da ugozoma ne, za a kuma inganta aikin

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon tsarin bunƙasa aikin nas da ungozoma domin ƙara yawan ma’aikatan lafiya da tabbatar da samun Universal Health Coverage (UHC) da cimma manufofin ci gaba mai ɗorewa (SDGs).

Ƙarin bayani:

Ƴan Sandan Jigawa sun wayar da kan ƴan jari-bola kan kare kai daga taka bom yayin tsince-tsinceRundunar Ƴan Sanda ta Jih...
10/10/2025

Ƴan Sandan Jigawa sun wayar da kan ƴan jari-bola kan kare kai daga taka bom yayin tsince-tsince

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta gudanar da taron wayar da kai ga ƴan kasuwar shara da ƙarafa (ƴan jari-bola) a jihar domin faɗakar da su kan haɗarin abubuwa masu fashewa (irin su bom).

Ƙarin bayani: https://tinyurl.com/37cnre4e

ICPC ta yi nasarar samun hukuncin ɗaurin shekaru ga wani tsohon daraktan da ya yi zambar miliyoyin nairoriKotun Tarayya ...
10/10/2025

ICPC ta yi nasarar samun hukuncin ɗaurin shekaru ga wani tsohon daraktan da ya yi zambar miliyoyin nairori

Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Daraktan Kuɗi da Gudanarwa na Abuja Metropolitan Management Council (AMMC), Garuba Mohammed Duku, hukuncin shekara 24 a gidan yari bisa laifin zamba da almundahanar kuɗi har naira miliyan 318.

Ƙarin bayani: https://tinyurl.com/39kkx8b6

ICPC za ta gurfanar da wani ɗan jaridar ƙarya kan zambar miliyoyin nairoriHukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta...
10/10/2025

ICPC za ta gurfanar da wani ɗan jaridar ƙarya kan zambar miliyoyin nairori

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta bayyana shirinta na gurfanar da wani mutum mai suna Alkazim Kabir, wanda aka fi sani da “Abbati Kabiru Abuwa,” bisa tuhumar zamba da ta kai kusan naira miliyan 14.

Ƙarin bayani: https://tinyurl.com/3s7uss9x

ADC ta bayyana ra’ayinta kan naɗa sabon shugaban INECJam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa tana ku...
10/10/2025

ADC ta bayyana ra’ayinta kan naɗa sabon shugaban INEC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa tana kula da matakin da gwamnati ke ɗauka na naɗa Farfesa Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), amma tana fatan zai tabbatar da sahihin shugabanci mai gaskiya da inganci.

Ƙarin bayani: https://tinyurl.com/yeyrms9e

Yanzu duk wata kwangila da ba ta haura naira biliyan 20 ba kamfani ɗan Najeriya ne zai na yi – MinistaƘarin bayani: http...
10/10/2025

Yanzu duk wata kwangila da ba ta haura naira biliyan 20 ba kamfani ɗan Najeriya ne zai na yi – Minista

Ƙarin bayani: https://tinyurl.com/4awkz9dv

Ƴan Sanda sun cafke masu safarar miyagun ƙwayoyi da ɓarayin dabbobi a JigawaRundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta sanar ...
02/10/2025

Ƴan Sanda sun cafke masu safarar miyagun ƙwayoyi da ɓarayin dabbobi a Jigawa

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta sanar da cafke mutane 21 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da ɓarayin dabbobi da masu fasa-gidaje a sassa daban-daban na jihar.

Karin bayani: https://tinyurl.com/nz3v9872

Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ya ƙaddamar da sabbin injinan ruwa domin tabbatar da samar da tsaftataccen ruwaƘara...
02/10/2025

Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ya ƙaddamar da sabbin injinan ruwa domin tabbatar da samar da tsaftataccen ruwa

Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da sabbin injinan samar da ruwan sha masu ƙarfin KB 250 da KB 150, tare da gyaran babban injin Mahadi Kature da ke haɗe da babbar tashar ruwan sha ta yankin, domin magance matsalar ƙarancin ruwa da ta daɗe tana addabar jama’a.

Karin bayani:

Likita ɗaya na kula da marassa lafiya sama da 9,000 a Najeriya, likitoci sun ƙayyade iya awanni da zasu na aiki daga yan...
02/10/2025

Likita ɗaya na kula da marassa lafiya sama da 9,000 a Najeriya, likitoci sun ƙayyade iya awanni da zasu na aiki daga yanzu

Ƙungiyar Nigerian Association of Resident Doctors (NARD) ta bayyana takaici kan rashin daidaituwar adadin likitoci da marasa lafiya a Najeriya, inda kowane likita ɗaya ke kula da mutane 9,083 – lamarin da s**a ce ya yi nisa da ƙa’idar duniya.

Karin bayani: https://tinyurl.com/bdcsv9eb

An zargi jam’iyyun siyasa da durƙusar da ci gaban Najeriya a shekaru 65 na ƴancintaManyan masu fafutukar kare haƙƙin ɗan...
02/10/2025

An zargi jam’iyyun siyasa da durƙusar da ci gaban Najeriya a shekaru 65 na ƴancinta

Manyan masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam a Najeriya, Femi Falana (SAN), da tsohon ɗan majalisar wakilai, Usman Bugaje, sun soki tsarin jam’iyyun siyasa a ƙasar a matsayin babban dalilin da ya hana ci gaban Najeriya shekaru 65 bayan samun ƴancin kai.

Karin bayani: https://tinyurl.com/4uv6bezs



Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi sun kai ziyarar ta’aziyya kan rasuwar haziƙin ɗalibi a JigawaWata tawaga daga ƙungiyar...
02/10/2025

Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi sun kai ziyarar ta’aziyya kan rasuwar haziƙin ɗalibi a Jigawa

Wata tawaga daga ƙungiyar Colleges of Education Academic Staff Union (COEASU) ta kai ziyarar ta’aziyya ga majalisar gudanarwa ta Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel, bisa rasuwar dalibi mafi ƙwarewa a fannin Mathematics/Physics na NCE 2, Khalid Yunusa, wanda ya rasu a hanyar zuwa Gusau domin rubuta jarrabawar neman tallafin karatu na ƙungiyar.

Karin bayani: https://tinyurl.com/2p9hvj2k


Address

Dutse

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TTN News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to TTN News Hausa:

Share