News Room Radio Jigawa

News Room Radio Jigawa News Production

24/02/2024

24-02-2024 GUMEL
Nine people were prosecuted by the Sanitation mobile court for violating Sanitation rules in Gumel local Government area.
The affected people were private and commercial owners, motorcyclists and tricycles.
Passing the Judgment, the mobile court Judge, Magistrate Mannir Sarki said they were to pay fine of between one thousand to five thousand Naira or serve two weeks imprisonment for the offences.
In his part , the State Sanitation Supervisor in the area, Murtala Bako appreciated the level of cleanliness at Model Boarding Primary school and Gumel Correctional centre.
However , he called on Lautai Boarding Science Secondary School to clean the bush within the School premises.
Murtala Bako then commended the council for the provision of enough Sanitation working materials.
Similarly, Sabon Layi Community development Association has donated fifty brooms to Gumel local Government.
Chairman of the Association Malam Idris Hashim Gumel said the aim is for the association to contribute towards a clean Gumel.
IO/MAG

24/02/2024

24-02-2024 GUMEL
Kotun tafi da gidanka kan tsaftar mahalli a karamar Hukumar Gumel ta hukunta mutane tara bisa lefin karya dokokin tsaftar mahalli
Wadanda kotun ta hukunta sun hadar da masu motoci na kansu da na haya da kuma masu Babura
Alkalin kotun , Majistare Mannir Sarki yace an ci tarar kowannensu naira dubu biyar-biyar ko kuma zaman gidan yari na tsawon makonni biyu
A wani labarin kuma kungiyar cigaban Unguwar Sabon Layi a garin Gumel ta bada gudunmawar tsintsiya bandir hamsin ga karamar hukumar Gumel
Shugaban kungiyar Malam Idris Hashim Gumel ya mika gudunmawar ga mukaddashin shugaban KH Haladu Musa Mele
A jawabinsa jamiin sa ido na aikin daga jiha, Murtala Bako ya ziyarci makarantar firamaren kwana ta Gumel da kuma gidan gyaran taribiyya inda ya yaba da yadda aikin ya gudana
Ya kuma shawarci mahukuntan sikandaren kimiyya ta Lautai dasu tabbatar da share ciyayin dake harabar makarantar

24/02/2024

24-02-2024 GONA
Shugaban kwamitin aikin gona na majalissar dokokin jihar Jigawa Alhaji Hassan Sheriff Kirya ya bukaci alumma dasu rungumi sana-ar noma domin wadata kasa da abinchi
Alhaji Hassan Sheriff ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci gonar Dan Makwayon Gumel Alhaji Muhammad Idris dake garin Gilima ta karamar hukumar Taura
Yace kwamiti da kuma gwamnati suna muna da kuma maraba da samun muhimman mutane irin su Hakimi suna yin noma domin bada misali ga na baya
Dan majalissar dake wakiltar karamar Hukumar Birniwa, yace zasu gayyato Gwamna Umar Namadi domin ganin irin wadannan gonaki domin sanya albarka da kuma baiwa mutane shaawar shiga shirin noma
A jawabinsa wakilin mai martaba sarkin Gumel kuma Majidadin Gumel Alhaji Murtala Aliyu yace akwai bukatar alumma su rungumi noma domin samar da abinchi ga jiha da kuma kasa baki daya
A jawabinsa tun da farko Dan Makwayon Gumel Muhammad Idris ya bukaci gwamnati data rinka samarwa da manoma taki da Irin shuka akan lokaci
Ya kuma baiwa gwamnati shawarar yin rangwamen kayayyakin noma domin baiwa manoma damar yin noma

24/02/2024

24-02-2024 BUJI
Karamar Hukumar Buji zata sayo kayayyakin tsaftar muhalli domin saukaka ayyukan masu shara a kowanne wata.
Shugaban karamar karamar Abdullahi Suleiman Yayari ya sanar da hakan ta hannun kansilan sashen ruwa da tsaftar muhalli Alhaji Isa Jata a lokacin aikin tsaftar muhalli na karshen wata
Ya kuma yaba da irin yadda kwamitin masu ruwa da tsaki akan tsaftar muhalli ya jajircewa wajen samun nasarar aikin tsaftar mahalli a yankin
Tunda farko shugaban sashen ruwa da tsaftar muhalli Alhaji Baffa Abdullahi Kudai yace KH ta na bada kulawa akan harkokin tsaftar muhalli da kuma kiwon lafiya
Ya kara da cewar KH ta gina asibiti a Garin Karanjau da Tudun Wada
Shima da yake duba aikin tsaftar muhalli, Jamiin kula da tsaftar muhalli na maaikatar kare muhalli ta jiha Alhaji Lurwanu Aminu ya yaba da yadda aikin ya gudana a gundumomin Yayari da Buji da kuma Gantsa.

24/02/2024

24-02-2024 SOJA
Wakilin mazabar Dutse a majalissar dokokin jihar Jigawa, Tasiu Ishaq Soja yace gwamna Mallam Umar Namadi ya amince da ware naira miliyan 30 daga cikin naira miliyan dari na aiyukan mazabu domin bunkasa tattalin arzikin alummar jihar nan
Tasiu Ishaq ya sanar da hakan ne ta cikin shirin Radio FM Andaza mai suna Jigawa a yau.
Yace gwamna Umar Namadi ya bullo da tsarin ne domin bada jari ga masu kananan sanaoi maza da mata domin rage radadin tsadar rayuwa
Dan majalisar yakara da cewar tuni ya gabatar da matsalolin zaizayar kasa dake damun garin Dutse ga gwamnati kuma tuni aka sanya kasafin kudin bana
Yace a aljihunsu ya gyara tuka tuka fiye da dari biyu yayinda a duk wata yake biyan kudin magani a asibitoci na kusan naira miliyan biyar da aljihunsu
Dan majalissar yana mai cewar ya gina gidajen marayu guda bakwai , yayinda ya aurar da marayu bakwai tare da yi musu kayan daki
Haka kuma yace yana da mararsa lafiya kusan 40 a kwance a asibitoci yake daukar nauyin bi ya musu kudaden magani
Tasiu Ishaq Soja ya kara da cewar karkashin aiyukan mazabu, an bada aikin gina makarantun Islamiyya da masalatai a mazabarsa daban daban
Ya bada tabbacin cigaba da zama wakilin mutanen Dutse na gari a majalissar tare da nemowa mutanen mazabarsa hakkokinsu a duk inda ya makale

23/02/2024

23-02-2023 KADUNA
Ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Jigawa tare da hadin gwiwar kamfanin kwararru na Anas Ibro International company sun gudanar da taron bita na yini uku ga shugabannin kananan hukumomi da shugabannin majalissun kamsiloli da Daraktoci da shugabannin sassan jin dadin jama-a da kuma Jamian Yada labarai na kananan hukumomi
Taron bitar mai taken nauyin da ya rataya akan shugabanni ga alumma an gudanar dashi ne a garin Kaduna.
Daya daga cikin mahalarta taron bitar kuma shugaban karamar hukumar Babura Alhaji Lawan Ismail yace sun kara samun ilmi kan yadda zasu gudanar da aiyukansu ga alumma
Yace taron bitar yana da muhimmanci ga shugabanni domin tallafawa alumma a bangarori daban daban domin samun zaman lafiya da kuma karuwar arziki
Shima da yake jawabi daraktan jin dadin jama-a na maaikatar kananan Hukumomi ta Jiha Muhammad Mukaddas yace wannan ba sabon abu bane a jihar Jigawa, kuma wannan taron bitar sake tunatar wa ce.
Muhammad Mukaddas yana mai cewar sun karu da abubuwa da zasu yi amfani dasu wajen taimakawa alumma.
Daga nan sai ya bada tabbacin isar da sakon da s**a samu a wajen bitar ga mahukunta

23/02/2024

23-02-2024 KADIRA
Hadejia Emirate Zakkat Committee has distributed zakat of farm Produce worth seven point four million naira to the needy at Kadira District in Guri local government area
Vice chairman of the committee and chief Imam of Hadejia Malam Yusuf Abdurrahman who presided over the distribution exercise, described Zakkat is one of the five pillars of Islam.
Farm produce distributed include 149 bags of Millet, 59 Bags of Rice and five hundred thousand naira cash.
Malam Yusud Abdurahaman advised wealthy in the society to give out zakkat as and when due.
On his part, the secretary of the committee Engineer Isma`ila Barde Hadejia said the alms was distributed to needy in line with Islamic injunction.
In his welcome address the District Head of Kadira, Alhaji Haruna Abbas commended Hadejia emirate Zakkat committee for its commitment towards the collection and distribution of Zakkat.
FMM/MAG/BS

23/02/2024

23/02/2024 CONDOLENCE
Kwamishinan ma`aikatar yada labarai na jiha, Alhaji Sagir Musa Ahmad ya bayyana rasuwar tsohon jami`in yada labarai na kananan hukumomin Guri da KiriKasamam Alhaji Sunusi A Doro da cewa babban rashin ne ga ma`aikatar yada labarai baki daya.
Kwamishinan wanda ya bayyana haka ne ta hannun daraktan yada labarai na ma`aikatar, Alhaji Isma`ila Yakubu, rasuwar ta girgiza ma`aikatan, inda ya bayyana marigayi Sunusi A. Doro a matsayin haziki ma`aikaci mai aiki tukuru.
Daga nan kwamishinan yayi addu`ar Allah ya jikansa da rahama ya kuma baiwa iyalai da yan`uwa hakurin hakurin jure rashin..
Hakazalika kungiyar yan`jaridu reshen ma`aikatar yada labarai ta jiha ta bayyana rasuwar Sunusi A. Doro da cewa babban rashin ne ga al`ummar musulmi baki daya.
Shugaban kungiyar comrade Muhammad Umar ne ya bayyana haka a sakon ta`aziyya mai dauke da sa hannun ma`ajin kungiyar Nasiru Yusuf Birnin kudu, yace za`a dade ana tunawa da irin gudunmawar da ya bayar a fannin yada labarai.
Daga nan yayi addu`ar Allah ya gafarta masa ya kuma baiwa iyalai da yan`uwa hakurin jure rashin.
Haka kuma kungiyar yan`jaridu reshen gidan rafiyo Jigawa ta mika makamanciyar wannan ta`aziyya ga iyalan marigayi.
Sakataren kungiyar Sani Muhammad Gumel wanda ya bayyana haka a sakon ta`aziyya, yayi addu`ar Allah ya jikan sa rahama.

23/02/2024

23-02-2024 KADIRA
An raba zakkar kayan amfanin gona da kudin su ya kai naira miliyan bakwai da bubu dari hudu ga mabukata a gundumar Hakimin Kadira dake yankin karamar hukumar Guri.
Kayayyakin da aka raba sun hadar da buhu 59 na shinkafa da kuma zunzurutun kudi naira dubu dari biyar.
Da yake kaddamar da rabon zakkar wakili a kwamatin zakka na masarautar Hadejia, Sheik Yusuf Abdulrahman ya bayyana zakka a matsayin daya daga cikin shika-shikakan addinin Musulunci biyar.
Yayi kira ga wanda Allah ya h**e wa dukiya su tabbatar da fidda zakka daga cikin dukiyoyin su.
A nasa jawabin sakataren kwamatin zakka na masarautar Hadejia, Injiniya Isma’ila Barde ya ce ana raba zakka ne ga mabukata kamar yadda Allah ya bada umarni.
Tun farko a jawabin sa na maraba, Hakimin Kadira Alh Haruna Abbas ya yabawa mai martab sarkin Hadejia bisa baiwa kwamatin zakka na masarautar damar kewayawa gundumomin hakimai domin raba zakka ga mabukata.

23/02/2024

23/02/2024 JNI/JG
Kungiyar Jama`atul Nasril Islam ta kasa reshen jihar Jigawa ta bukaci samun hadin kai da goyon bayan gidan Radiyo Jigawa wajen halartar taron lacca na azumin watan Ramadan da take shiryawa a kowace shekara.
Bukatar hakan na kunshe ne cikin takarda mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar na jiha, Malam Muhammad Ahmad Babangida.
Taron lacca da kungiyar ke gayyato malamai da sauran masu ruwa da tsaki, domin bayyanawa al`ummar Musulmi falalar azumin watan Ramadan, da kuma muhimmancin hadin kai da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki da tsaro a tsakanin Musulmi.
Taron mai taken Tasirin Kafafen Yada Labarai ga harkokin addini da kyawawan al`adu a mahanga ta addini da kuma tsarin zamantakewa da tsaro da tattalin arzikin al`umma, wanda za`a gudanar a ranar 29 ga wannan watan a Sakatariyar kungiyar a kusa da gidan mai na B.A Bello dake kan hanyar zagaye a Unguwar Yalwawa a nan birnin Dutse da karfe hudu na yamma.
Daga nan sanarwar tayi fatan samun halartar wakilan kafafen yada labarai domin cimma burin da ake bukata.

22-02-2023                      NUT Kungiyar malaman makaranta ta kasa reshen jihar Jigawa ,  tace tana tattara bayanan ...
22/02/2024

22-02-2023 NUT
Kungiyar malaman makaranta ta kasa reshen jihar Jigawa , tace tana tattara bayanan malamai da kuma makarantun da ake dasu a kananan hukumomin jihar nan 27 domin sabunta bayanansu
Shugaban kungiyar, Comrade Abdulkadir Yunusa Jigawa ya sanar da hakan a lokacin ganawa da wakilinmu
Yace kungiyar ta bukaci rassanta na kananan hukumomi su aike mata da yawan malamai da yawan makarantun da suke kananan hukumomi domin ajiye bayanansu
Abdulkadir Yunusa Jigawa yana mai cewar tattara bayanan ya zama wajibi domin sabunta bayanan da suke dashi tun shekaru uku da s**a gabata
Ya musanta bullar wani jaddawalin yawan malamai da kuma makarantu da suke yawo a kafar sadarwa ta Zamani, yana mai cewar jaddawalin tsoho ne da suke da shi tun shekaru uku da s**a gabata
Shugaban kungiyar malaman na Jigawa ya bukaci malamai da su cigaba da jajircewa wajen koyar da dalibai domin cimma manufar gwamnati na bunkasa Ilmi a kowanne mataki
Ya kuma nuna gamsuwar kungiyar kan yadda aka gudanar da jarrabawar maida malaman shirin koyarwa na j-teach zuwa na dindindin a fadin jihar jigawa

22/02/2024

22-02-2024 B/KUDU
Kungiyar masu motocin sufuri ta kasa reshen karamar hukumar Birnin kudu ta gudanar da addu`o`i na musamman domin neman sauki dangane da halin da ake ciki na tsadar kayan abinci da sauran kayayyalom masarufi.
A jawabin da ya gabatar shugaban Alhaji Suleiman Jibrin yace sun shirya taron addu`ar a karo na farko domin neman sauki dangane da tsadar rayuwa da kuma tunawa da yan`kungiyar da s**a rasu.
Yace haka kuma sun gudanar da addu`o`in-neman zaman lafiya mai dorewa ga kasa da jihar Jigawa da kuma karamar hukumar Birnin kudu.
A nasa jawabin tsohon shugaban kungiyar, Malam Abdullahi Suleiman yayi kira ga sauran shugabannin kungiyar na jihar an suyi koyi da takwarorinsu na karamar hukumar Birnin kudu wajen shirya irin wannan taron.
A sakon da ya aike wajen taron addu`ar shugaban karamar hukumar Alhaji Magaji Yusuf wanda ya sami wakilcin makaddashin sakatare, Alhaji Ali Abdullahi ya yabawa kungiyar bisa hangen nesan su wajen shirya wannan taron.

Address

JRC
Dutse

Telephone

+2347037414765

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when News Room Radio Jigawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to News Room Radio Jigawa:

Share