29/10/2025
Kakar Wasannin 2025-2026 | Sabbin Dokoki Sun Fara Aiki A Hukumance:
Ga manyan gyare-gyaren da Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya (IFAB) ta sanar:
1. Gyaran Doka ta 3 - 'Yan Wasa:
Kyaftin ɗin ƙungiyar ne kawai ke da izinin yin magana da alkalin wasa a lokacin wasan, ba dukkan 'yan wasa ba.
2. Gyaran Doka ta 5 - Alkalai:
Alkalin wasa zai yi amfani da ƙidaya ƙasa na daƙiƙa 5 na ƙarshe na daƙiƙa 8 da aka ba wa mai tsaron raga damar sakin kwallo daga hannunsa.
3. Gyaran Doka ta 8 - Bada kwallo:
Idan ƙwallo tana cikin yankin bugun fenariti a lokacin dakatarwar, Dan wasa yana iya bada kwallon kai tsaye ga mai tsaron ragar ƙungiyarsa.
4. Gyara ga Dokar 9 - Taba kwallo:
Idan koci ko wanda yake jiran maye gurbi [Dan Benci] ya taɓa ƙwallo yayin da ta fita waje ya dawo da ita cikin filin wasa don hanzarta wasa:
Ana iya ba wa abokan hamayya bugun kai tsaye.
Babu ba da gargaɗi ko kati sai dai idan hakan ya sake faruwa akai-akai.
5. Gyara ga Dokar 11 - Satar gida:
Ana amfani da wurin farko na taɓawa lokacin tantance satar gida.
Ga mai tsaron raga, ana amfani da wurin ƙarshe na taɓawa domin ƙara daidaito.
6. Gyara ga Dokar 12 - Kurakurai da Rashin Da'a:
Idan mai tsaron raga ya riƙe ƙwallo fiye da daƙiƙa 8:
Ana iya ba abokan hamayya bugun kusurwa.
Babu katin gargadi sai dai idan hakan ya sake faruwa akai-akai.
Haka zalika za'a iya amfani da bugun 'Tazara' a kaikaice akan wanan hukuncin:
7. Kwaskwarima ga Dokar 16 - Bugun falan daya:
Idan gola ya buga ƙwallo taje ta ketare layin tsakiyar ragar abokan hamayyarsa gaba ɗaya ba tare da an samu wani dan wasa ya taba, ana iya bada wani bugun falan dayan.
8. Kwaskwarima ga Dokar 17 - Bugun kusurwa:
Ana iya ba da sake bugun kusurwa idan ƙwallon ta ketare layin raga gaba ɗaya bayan ɗan wasan da ke kare ragarsa ya taɓa ta ta shiga / ba tare da an zura kwallon daga abokan hamayya.