Giant Space Communications Limited

Giant Space Communications Limited Barka da Hantsi TV is a Live/interactive program.

To become the leading media content planning company in Africa, delivering innovative and culturally rich radio and television programming that informs, educates, and entertains diverse audiences.

Yadda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya a halarci sallar juma'a a masallacin gidan gwamnati.
06/03/2026

Yadda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya a halarci sallar juma'a a masallacin gidan gwamnati.

05/03/2026

Mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo

📷 Muhammad Adam

05/03/2026

"Babu batun yin sulhu tsakanina da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf"

~Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda

05/03/2026

Jawabin Hon Umar Haruna Doguwa sabon shugaban jam'iyyar APC a gidan gwamnatin Kano

Hon Doguwa ya koÉ—a gwamna Abba tare da yaba masa da cewa jajirtaccen jagora ne.

Me za ku ce?

📷 Kano 360 TV

05/03/2026

Wata Babbar Kotu da ke birnin Abuja ta wanke tsohon mataimakin kwamishinan ’yan sanda, DCP Abba Kyari, daga tuhume-tuhume guda 23 da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta shigar a kansa.

Lauya Barrista Hamza Nuhu Ɗantani ne ya bayyana hakan, inda ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta saurari hujjojin da ɓangarorin biyu s**a gabatar a gaban ta.

A cewarsa, kotun ta bayyana cewa hujjojin da aka gabatar ba su wadatar ba wajen tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa Abba Kyari, don haka ta yanke shawarar wanke shi daga dukkan tuhume-tuhumen da aka gabatar.

Ɗantani ya ƙara da cewa kotun ta nuna cewa bai dace a jingina masa manyan zarge-zarge ba, musamman waɗanda s**a shafi mallakar dukiya ba bisa ƙa’ida ba da kuma zargin almundahana.

Ya kuma ce kotun ta bayyana Abba Kyari a matsayin gogaggen jami’in ɗansanda wanda ya taka rawar gani wajen yaƙi da aikata laifuka da tabbatar da tsaro a Najeriya.

Sai dai lauya Hamza Nuhu Ɗantani ya jaddada cewa har yanzu akwai wata shari’a dabam da ke gaban wata kotu, inda ya ce suna sa ran samun sakamako mai kyau a nan gaba, in Allah Ya yarda.

Ana zargin gwamnatin mulkin soji ta Nijar da rike albashin malaman makaranta da aka dauka karkashin tsarin aikin kwantar...
03/03/2026

Ana zargin gwamnatin mulkin soji ta Nijar da rike albashin malaman makaranta da aka dauka karkashin tsarin aikin kwantaragi.

Gamayyar ƙungiyar malaman makaranta ta Dynamique ta fito karara tana s**ar abin da ta bayyana a matsayin halin ko-in-kula da gwamnati ke nunawa dangane da biyan hakkokin mambobinta.

A cewar ƙungiyar, an shafe watanni uku — tun daga watan Disamba zuwa ƙarshen Fabrairu — ba tare da an biya malaman albashinsu ba, lamarin da ta ce na ƙara jefa su cikin mawuyacin hali.

Kungiyoyin sun yi kira ga mahukunta da su dauki matakin gaggawa domin warware matsalar, tare da jaddada cewa kare martabar malamai da inganta harkar ilimi a ƙasa ya kamata ya zama abin fifiko.

02/03/2026

Ban yi mamaki da kalaman Waiya a kaina ba, saboda abincinsa ya ke karewa - Buba Galadima.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake naÉ—a Dokta Ahmed Abubakar Audi a matsayin Kwamandan-Janar na Hukumar tsaro...
02/03/2026

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake naɗa Dokta Ahmed Abubakar Audi a matsayin Kwamandan-Janar na Hukumar tsaro ta Civil defence ta Najeriya, wato NSCDC, domin ci gaba da jagorantar hukumar na wani sabon wa’adin shekaru biyar.

Sake naɗin na zuwa ne bayan kammala wa’adin farko da Dokta Audi ya fara a shekarar 2021, lokacin da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar.

Bola Ahmed Tinubu ya amince da tsawaita haramcin fitar da man kadanya zuwa 2027.Shugaban Nijeriya ya kara wa’adin haramc...
26/02/2026

Bola Ahmed Tinubu ya amince da tsawaita haramcin fitar da man kadanya zuwa 2027.

Shugaban Nijeriya ya kara wa’adin haramcin da karin shekara guda, daga ranar 26 ga Fabrairu 2026 zuwa 25 ga Fabrairu 2027, a wani yunkuri na bunkasa sarrafa kayayyaki a cikin gida da kuma karfafa masana’antu.

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa matakin na da nufin kara habaka sarrafa man kadanya a Nijeriya, inganta rayuwar manoma da masu sana’ar, tare da kara darajar kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje.

25/02/2026

Dr Abdullahi Umar Ganduje yayin da gaisawa da shugaban jam’iyar APC na kasa Prof Nentawe Yilwatda a ofishin jam’iyar na kasa.

Mai bai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna shawara kan harkokin yaÉ—a labarai, Muyiwa Adekeye, ya sanar da cewa kotu ta É—age ...
25/02/2026

Mai bai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya sanar da cewa kotu ta ɗage shari’ar da ake yi da Nasir El-Rufai zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026. Hakan ya biyo bayan kasa gabatar da tsohon gwamnan a gaban Babban Kotun Tarayya da ke Abuja.

A cewar sanarwar, mai gabatar da ƙara ya roƙi kotu da ta ba da wa’adin makonni biyu domin bai wa jami’an DSS damar gabatar da El-Rufai, wanda a halin yanzu yake hannun ICPC.

Sai dai lauyan El-Rufai, Wole Iyamu, ya shaida wa kotu cewa babu wani uzuri da zai hana DSS gabatar da shi, tunda yana tsare a hannun wata hukuma ta gwamnati. Ya jaddada cewa ba lallai ba ne a nemi ƙarin lokaci kan lamarin.

Daga bisani, Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da ɗage shari’ar har zuwa watan Afrilu, abin da Muyiwa ya ce ya zarce buƙatar wa’adin da lauyoyinsu s**a nema.

Rahotanni sun nuna cewa ana tsare da El-Rufai tun ranar 16 ga Fabrairu, lokacin da ya amsa gayyatar EFCC da kansa. Daga bisani, ICPC ta karɓe shi a daren 18 ga watan, kuma har yanzu ba a ba da belinsa ba.

A gefe guda, ana kuma sauraron ƙarar da El-Rufai ya shigar a kotu kan DSS, yana zargin hukumar da take masa haƙƙinsa.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jigo a jam’iyyar haɗaka ta ADC, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar s**a ga gwamnat...
25/02/2026

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jigo a jam’iyyar haɗaka ta ADC, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar s**a ga gwamnatin APC bayan harin da aka kai wa wasu jagororin ADC a jihar Edo, ciki har da Peter Obi.

Atiku ya danganta lamarin da jam’iyyar APC, inda ya zarge ta da hannu a harin. Haka kuma, ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Najeriya ba tare da nuna wani bambanci ba.

Address

Dutse

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Giant Space Communications Limited posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Giant Space Communications Limited:

Share