07/03/2026
ƘUNGIYAR KWANKWASIYYA TA GARGADI MAJALISAR KANO KAN SHIRIN TSIGE GWAMNAN KANO AMINU ABDUSSALAM GWARZO. tace hakan Na Iya Haddasa fitina tsakanin Al ummah.
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta gargadi Majalisar Dokokin Jihar Kano game da shirin tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, inda ta bayyana cewa hakan na iya Haddasa rigingimun siyasa a jihar.
Kungiyar ta bayyana cewa ci gaba da yunkurin tsige Gwarzo wanda ta jaddada cewa rinjayen masu zaben Kano ne s**a zabe shi, ai watar da wannan quduri na iya kara kawo rarrabuwar kawuna a fagen siyasa, sannan hakan zai zama tamkar dakile amanar da al’umma s**a bai wa gwamnatin ne.
A ranar Alhamis ne mambobi talatin da takwas na jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar Dokokin Jihar s**a sanya hannu kan takardar neman tsige Mataimakin Gwamnan, bisa zargin cin amanar kasa da kuma amfani da iko ta hanyar da ba ta dace ba. ‘Yan majalisar sun zargi Gwarzo da taba kudin gwamnati a lokacin da yake rike da mukamin Kwamishinan kananan hukumomi, inda s**a ba shi wa’adin mako biyu ya kare kansa ko kuma su tsige shi daga mukaminsa.
To sai dai, a wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Kwankwasiyya, Dr. Habibu Mohammad, ya fitar a ranar Juma’a, kungiyar tana cewa wannan yunkuri na tsige shi yana da alaka da siyasa kawai, kuma ba shi da wani ingantaccen dalili na shari’a.