Arewa4Real

Arewa4Real Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa4Real, News & Media Website, Fagge Kano, Fagge.

Newly appointed Kano Pillars FC Technical Adviser, Daniel Ogunmodede has vowed to leave a lasting legacy at the club, de...
11/07/2026

Newly appointed Kano Pillars FC Technical Adviser, Daniel Ogunmodede has vowed to leave a lasting legacy at the club, declaring that his mission is to deliver success rather than simply become another name on the list of coaches who have managed the four-time Nigeria Premier Football League champions.

Ogunmodede made the bold declaration while speaking to journalists shortly after he was officially unveiled by the club's management at the Kano Pillars FC Secretariat in Kano.

Expressing appreciation to the club's leadership for entrusting him with the responsibility, the experienced tactician pledged to repay their confidence through commitment, discipline, and positive results on the pitch.

«“I am here to conquer, not to be counted. My mission is to build a competitive team that the supporters will be proud of. I know the expectations are high, but I am ready for the challenge,” Ogunmodede said.»

The new Technical Adviser described Kano Pillars as one of Nigeria's most successful and respected football clubs, renowned for its rich tradition and passionate supporters. He stressed his determination to work closely with the players, technical crew, and management to restore the club to the summit of Nigerian football.

Ogunmodede also appealed to the club's supporters to remain patient and continue giving the team their unwavering backing throughout the season, noting that their encouragement would play a vital role in achieving the club's ambitions.

Earlier, the management of Kano Pillars FC officially welcomed Ogunmodede and expressed confidence in his ability to lead the Sai Masu Gida to greater success in the upcoming Nigeria Premier Football League season.

The unveiling ceremony attracted club officials, supporters, members of the media, and other football stakeholders, all of whom wished the new Technical Adviser a successful and impactful tenure with the club.

✍️ By Arewa4Real

11/07/2026
Sabon Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Tukur Muhammad Babangida, ya kai ziyarar ba-zata zuwa Filin Wasan S...
11/07/2026

Sabon Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Tukur Muhammad Babangida, ya kai ziyarar ba-zata zuwa Filin Wasan Sani Abacha da ke Kofar Mata domin duba yanayin filin da kuma ƙarfafa gwiwar ma'aikatan da ke gudanar da ayyukansu a wurin.

A yayin ziyarar, shugabannin filin wasan, ma'aikata da sauran masu ruwa da tsaki sun tarbe shi cikin girmamawa. Wannan ita ce ziyararsa ta farko a hukumance zuwa filin wasan tun bayan da ya karɓi ragamar jagorancin Hukumar Wasanni ta Jihar Kano.

Da yake jawabi ga ma'aikatan, Alhaji Tukur Muhammad Babangida ya yabawa irin ƙoƙarin da suke yi wajen kula da filin wasan, tare da ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin gaskiya, jajircewa da haɗin kai.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Jihar Kano ta himmatu wajen inganta ababen more rayuwa na wasanni da samar da yanayin da zai taimaka wajen bunƙasa harkokin wasanni a faɗin jihar. A cewarsa, Filin Wasan Sani Abacha na da muhimmiyar rawa a ci gaban wasanni, don haka za a ci gaba da ba shi kulawar da ta dace domin ya kasance cikin mafi kyawun filayen wasa a Najeriya.

Ziyarar ta nuna kudirin sabon shugaban hukumar na kusantar ma'aikata, tantance ƙalubalen da ake fuskanta tare da samar da hanyoyin magance su domin ci gaban harkokin wasanni a Jihar Kano.

✍️ Arewa4Real

10/07/2026

Ga Mbappe Ga Hakimi

Wasu matasa ne s**a zargi Ahmad Dankoli da satar babur, kafin a ankara kawai s**a bi shi s**a cinna masa wuta har sai da...
09/07/2026

Wasu matasa ne s**a zargi Ahmad Dankoli da satar babur, kafin a ankara kawai s**a bi shi s**a cinna masa wuta har sai da ya mutu! Jami'an tsaro sun zo amma saboda yawan mutane ba su iya hanawa ba, jama'ar sun rinjaye su! InnaliLLAH wa'inna ilaihi rajiun! 😭💔

Na san malam Ahmad domin ina ganin rubutunsa wani lokaci a kan siyasa a (facebook), kwatsam kuma sai na ji ana maganar ya mutu, ba mutuwar ce abin mamaki ba, a'a, yadda aka kåshe shi. Innalillah wa'inna ilaihi rajiun! 😭💔

Haka kawai iyaye da iyalai suna zaune sai dai su ji wannan labari yaya za su ji don Allah... Wannan mãsifa da me ta yi k**a a ƙasar nan.

Allah gafarta masa, ka ba wa iyaye da iyalai haƙurin wannan walaƙanci da rashin. Allah ka tsara mu ya Allah.

Alƙalin bayan fage,
Ahmad Usman Elnafaty.

09/07/2026

Ƙungiyar Triple R Kannywood Ta Kai Ziyarar Musamman Domin Duba Aikin Titin Kaduna–Abuja da Gwamnatin Shugaba Tinubu Ke Gudanarwa

KADUNA – A wani mataki da ke nuna goyon baya ga manyan ayyukan raya ƙasa da kuma ƙarfafa wayar da kan jama’a game da ci gaban ababen more rayuwa, Ƙungiyar Triple R Kannywood ta kai wata ziyara ta musamman domin duba yadda aikin sake gina da faɗaɗa titin Kaduna–Abuja ke gudana, aikin da Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ke aiwatarwa.

Titin Kaduna–Abuja na daga cikin manyan hanyoyin da s**a fi muhimmanci a Najeriya, kasancewar shi ne ke haɗa Babban Birnin Tarayya da mafi yawan jihohin Arewa. Saboda haka, ana kallon sake gina da inganta wannan hanya a matsayin wani muhimmin aiki da zai sauƙaƙa zirga-zirga, bunƙasa kasuwanci da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

A yayin ziyarar, mambobin Triple R Kannywood sun zagaya sassa daban-daban na aikin, inda s**a ga irin ci gaban da aka samu a gina titin, gadoji, magudanan ruwa da sauran muhimman abubuwan da ke cikin aikin. Sun kuma samu bayanai daga injiniyoyi da masu kula da aikin kan irin fasahohin zamani da ake amfani da su domin tabbatar da inganci, ɗorewa da kuma kammala aikin cikin lokacin da aka tsara.

Mambobin ƙungiyar sun bayyana cewa ci gaban da s**a gani ya nuna yadda gwamnati ke mayar da hankali kan inganta hanyoyin sufuri, wanda ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma da bunƙasar tattalin arziki. Sun ce idan aka kammala aikin gaba ɗaya, zai rage cunkoson ababen hawa, rage yawan haɗurran hanya, da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar matafiya da jigilar kayayyaki tsakanin Abuja da jihohin Arewa.

Sun ƙara da cewa ingantacciyar hanyar za ta rage kuɗin sufuri, ta sauƙaƙa wa manoma da ’yan kasuwa kai kayayyakinsu cikin sauri zuwa kasuwanni, tare da ƙarfafa alaƙar kasuwanci tsakanin yankuna daban-daban na ƙasar.

Masana harkokin sufuri sun bayyana cewa manyan hanyoyi irin wannan na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki, jawo masu zuba jari, ƙarfafa masana’antu da samar da ayyukan yi. Sun ce inganta hanyar Kaduna–Abuja zai ƙara inganta zirga-zirgar kasuwanci da kuma taimakawa wajen haɗa sassan ƙasar cikin sauƙi.

A cewar wasu daga cikin mahalarta ziyarar, kasancewar fitattun jaruman Kannywood sun kai ziyara irin wannan na taimakawa wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin ayyukan raya ƙasa, tare da ƙarfafa al’umma su kula da kadarorin gwamnati domin amfanin kowa.

Ƙungiyar ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan ababen more rayuwa a faɗin ƙasar, tana mai bayyana cewa ci gaba da saka hannun jari a hanyoyi, gadoji da sauran muhimman ayyuka zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da inganta rayuwar al’umma.

A ƙarshe, mambobin Triple R Kannywood sun yi kira ga masu amfani da hanyar su ba injiniyoyi da ma’aikatan da ke gudanar da aikin cikakken haɗin kai, su kiyaye dokokin zirga-zirga a wuraren da ake aiki, tare da kare kayan aikin gwamnati domin tabbatar da cewa aikin ya kammala cikin nasara kuma ya amfani al’ummar Najeriya baki ɗaya.

Gwamnatin Kano Ta Fara Gina Babbar Gadar Jaba–Gayawa–Dausara–Ɗan KunkuruGwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Gi...
08/07/2026

Gwamnatin Kano Ta Fara Gina Babbar Gadar Jaba–Gayawa–Dausara–Ɗan Kunkuru

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta fara aikin gina babbar gada da za ta haɗa al’ummomin Jaba, Gayawa, Dausara da Ɗan Kunkuru, a wani yunƙuri na inganta hanyoyin sufuri da kuma magance matsalar ambaliyar ruwa da ke addabar yankin.

Wannan aiki na daga cikin manyan ayyukan raya ababen more rayuwa da gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama'a da kayayyaki, tare da ƙarfafa tattalin arzikin al’ummomin da abin ya shafa.

Bayanan da na samu daga wurin aikin sun nuna cewa an fara aiwatar da matakan farko na ginin gadar bisa ƙa’idojin aikin injiniya na zamani, tare da amfani da ingantattun kayan aiki domin tabbatar da cewa gadar za ta kasance mai ɗorewa kuma za ta iya jure yawan zirga-zirgar ababen hawa da sauye-sauyen yanayi.

Mazauna yankunan Jaba, Gayawa, Dausara da Ɗan Kunkuru sun shafe shekaru suna fama da matsalar katsewar hanyoyi musamman a lokacin damina, lamarin da ke kawo cikas ga zirga-zirgar jama'a, jigilar amfanin gona, kai marasa lafiya asibitoci da sauran harkokin yau da kullum.

Ana sa ran idan aka kammala wannan babbar gada, za ta kawo ƙarshen waɗannan ƙalubale tare da samar da ingantacciyar hanyar wucewa a duk lokacin shekara. Hakan zai rage wahalar sufuri, bunƙasa kasuwanci, da kuma ƙarfafa alaƙar tattalin arziki tsakanin al’ummomin yankin.

Haka kuma, ana sa ran aikin zai ƙara wa manoma sauƙin kai amfanin gonarsu zuwa kasuwanni cikin lokaci, tare da rage asarar da suke fuskanta sak**akon matsalolin hanyoyi.

Mazauna yankunan sun bayyana farin cikinsu da fara aikin, suna mai bayyana shi a matsayin wani babban ci gaba da zai inganta rayuwa tare da magance matsalolin da s**a daɗe suna fuskanta.

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada cewa aikin na daga cikin shirinta na ci gaba da gina hanyoyi da gadoji a faɗin jihar domin tabbatar da cewa al’ummomin karkara da na birane suna cin gajiyar romon dimokuraɗiyya ba tare da nuna bambanci ba.

Innalillahi wainna ilaihi rajun,Wannan mutumin da kuke gani lecturer ne a wata jamia a Kano"Anman yakan shiga university...
08/07/2026

Innalillahi wainna ilaihi rajun,

Wannan mutumin da kuke gani lecturer ne a wata jamia a Kano

"Anman yakan shiga university's dayawa yayi lecturing ,shekara biyu kenan daya hana yarinyan mutane gama makaranta idan tayi project takai Saiyace bahaka ba yace saita sake shine s**a hada baki da mujinta, s**ayi masa wayyo yace su Hadu a Cikin BuK saboda yayi lalata da ita.

Bayan ya shiga hannu anga videon sa yana cin dukaa kan lamarin"

Daga Madam Korede

Golden Eaglets Suffer Back-to-Back Defeats, Target Strong Finish Against ChinaNigeria's Golden Eaglets endured a 4-2 def...
08/07/2026

Golden Eaglets Suffer Back-to-Back Defeats, Target Strong Finish Against China

Nigeria's Golden Eaglets endured a 4-2 defeat to Australia in their second fixture of the Four-Nation U-17 Invitational Tournament in China, extending their winless start to the competition.

The defeat came after a hard-fought 3-2 loss to Tanzania's Serengeti Boys in their opening match, leaving the Nigerian side with consecutive defeats in the tournament.

Across their first two outings, the Golden Eaglets have scored four goals but conceded seven, highlighting the challenges they have faced against quality opposition.

The team will now shift its focus to Saturday's final fixture against tournament hosts China, where they will be aiming to secure their first victory and conclude the competition on a positive note.

✍️ Reporting: Isa Wapa II

Tsohon ɗan wasan Super Eagles,Omeruo da Umar Sani Sekarege sun hadu a filin atisaye, inda s**a gudanar da atisaye tare c...
08/07/2026

Tsohon ɗan wasan Super Eagles,
Omeruo da Umar Sani Sekarege sun hadu a filin atisaye, inda s**a gudanar da atisaye tare cikin yanayi mai cike da nishadi da himma.
Irin wannan haduwa na nuna kyakkyawar alaka da kuma ci gaba da shirye-shiryen kakar wasa.
Me kuke tunani game da wannan haduwar?

Address

Fagge Kano
Fagge
700001

Telephone

+2349067214481

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa4Real posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share