
06/11/2023
بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ
"مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيْهِ ۖ فَمِنْهُم مَّن قَضَىٰ نَحْبَهُۥ وَمِنْهُم مَّن يَنتَظِرُ ۖ وَمَا بَدَّلُواْ تَبْدِيلًا"
Cikin Alhini da juyayi muke mika sakon ta'aziyyar mu ga Sahibul Asr (Ajjalallah Farajahu Sharif), Da Jagoran mu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).
Na Rashin; Marhum. Muhammad Najib Haruna.
Marhum. Ya kasance Hazikin Matashi abin misali wajen kula da Addini, Bayan haka ya kasance cikakken ma'aikaci a cikin Matasa na Rundunar Jaishi Shaheed Ahmad Zakzaky (JASAZ) a Zone ɗin Hujr Bin Adi, kuma mai bada gudunmawa da himma wajen sauke haƙƙin daya ke wuyansa.
An Shaidi Muhammad da nutsuwa, haƙuri yayin aiki da tsananin Sallamawa ga Jagora.
Ya rasu a safiyar yau Lahadi 5/11/2023 wanda yayi daidai da 21/04/1445 Sakamakon rashin Lafiya daya yi fama da ita. Inda yayi zaman jinya a Qauna Clinic dake Maraba kafin daga bisani ya koma Zariya inda Allah yayi masa rasuwa. An buzne shi tare da yima sa Sallah a Garin Zariya Jihar Kaduna.
Muna kara mika sakon ta'aziyyar mu ga iyaye, abokai da yan uwansa, Allah ya girmama matsayin sa ya karɓi Uzurinsa.
Muna rokon yan uwa da su sanya shi cikin addu'oin su tare da barar Fatiha daya, da salatin Annabi goma sadaukarwa zuwa ga ruhin sa.
KULLU NA AHMAD YA ABA AHMAD
JASAZ SHUHADA MEDIA
05-11-2023