Jaridar Arewa

Jaridar Arewa Jarida ce ta Online da zata kawo maku ingantattun labarai na cikin gida Nijeriya, da ƙasashen ƙetare.
(2)

Idan kuna buƙatar talla ko wallafa rubutunku, ku tuntuɓi wannan Numbar
👉 +234 912 409 9064

Uwargidan shugaban ƙasar Nijeriya Sanata Oluremi Tinubu ta ziyarci iyalan tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari...
08/08/2025

Uwargidan shugaban ƙasar Nijeriya Sanata Oluremi Tinubu ta ziyarci iyalan tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari a yau Juma'a, a gidansu na Kaduna.

Mahaifiyata First Lady ce ta jihar Bauchi, ƴar kasuwa ce, kuma shugabar jami'a ce, kuma har yau tana girki wa mijinta - ...
08/08/2025

Mahaifiyata First Lady ce ta jihar Bauchi, ƴar kasuwa ce, kuma shugabar jami'a ce, kuma har yau tana girki wa mijinta - Inji Shamsudeen Bala Mohammed, Ɗan Gwamnan Bauchi.

Gwamnatin Tarayya Da Ofishin Jakadancin Amurka Sun Haɗa Gwiwa Don Wayar Da Kan ‘Yan Nijeriya Kan Sababbin Ƙa’idojin Samu...
08/08/2025

Gwamnatin Tarayya Da Ofishin Jakadancin Amurka Sun Haɗa Gwiwa Don Wayar Da Kan ‘Yan Nijeriya Kan Sababbin Ƙa’idojin Samun Biza

Gwamnatin Tarayya ta haɗa gwiwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya domin wayar da kan ‘yan Nijeriya kan sababbin ƙa’idojin neman bizar Amurka tare da tabbatar da bin ƙa’ida yayin neman.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudana tare da Jakaden Amurka a Nijeriya, Richard M. Mills Jr., a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce wannan yekuwar wayar da kan ta zama dole saboda Amurka tana ci gaba da zama ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suke yawan ziyarta.

Idris ya ce a tsawon shekaru ‘yan Nijeriya suna tafiya Amurka saboda dalilai daban-daban, ciki har da yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu, da kuma neman magani.

Ya ce: “An san Nijeriya a duniya a matsayin ƙasar da ‘yan ƙasar ta suke yawan yin tafiya zuwa ƙasashe daban-daban, suna hulɗa da ƙasashen duniya ta fuskar harkar kasuwanci, ilimi, yawon buɗe ido, da sauran muhimman fannoni. Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya s**a fi ziyarta, abin da ke nuna zurfin dangantaka mai tsawo tsakanin ƙasashen biyu.

“Yawancin ‘yan Nijeriya suna zuwa Amurka ne domin karatu, aiki, neman magani, ziyartar ‘yan'uwa, yawon buɗe ido, da damar zuba jari.

"Wannan mu’amala mai ƙarfi tana ci gaba da bunƙasa al’ummomin biyu.

"Sababbin abubuwan da Ofishin Jakadancin Amurka ya bayyana game da sauye-sauye a ayyukan ofishin jakadancin da hanyoyin neman bizar sun jima suna cikin labarai kwanan nan.

“Waɗannan sauye-sauyen, kamar yadda Ofishin Jakadancin Amurka ya bayyana, wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta bayar da sabis, ƙara saurin aiki, da mayar da martani ga sauye-sauyen buƙatun ayyukan jakadanci.”

Ministan ya yaba wa gwamnatin Amurka bisa ƙoƙarin yin bayani kai-tsaye ga ‘yan Nijeriya a wannan taro tare da tabbatar da samun sahihan bayanai na zamani ga kowa.

Haka kuma ya jaddada girmamawa da haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Amurka da kuma jajircewar Ofishin Jakadancin wajen sanar da matafiya ‘yan Nijeriya.

A nasa jawabin, Jakaden Amurka, Ambasada Mills, ya ce bin ƙa’idojin neman biza da dokokin Amurka na ‘yan Nijeriya abu ne mai muhimmanci wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

“Bin dokokin neman biza na Amurka ba kawai wani nauyi ba ne, amma ginshiƙi ne na amincewa da girmama juna tsakanin ƙasashen biyu,” inji Ambasada Millis.

Ya ƙara da cewa: “Kamar yadda Minista ya bayyana, ni da shi mun yi tattaunawa mai amfani game da dokokin biza na Amurka da kuma yadda za mu isar wa ‘yan Nijeriya muhimmancin bin waɗannan dokokin.

“Bari in fayyace cewa Amurka tana daraja ƙarfaffar dangantakar ta da Nijeriya da kuma nau’o’in hulɗa da yawa da ke tsakanin ƙasashen biyu.

"Bizar Amurka na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da riƙe waɗannan lamurran dangantaka da ƙarfafa su, ko ta hanyar bai wa mutane damar tafiya domin ilimi, kasuwanci, yawon buɗe ido, ko musayar al’adu.”

Jakaden ya jaddada cewa ya zama dole a yi amfani da biza bisa ga dokoki da ƙa’idojin Amurka.

Ya ce: “Tabbas, muna maraba da baƙi ‘yan Nijeriya a Amurka kamar yadda Nijeriya take maraba da ‘yan Amurka masu zuwa wannan ƙasa. Dukkan gwamnatoci suna son baƙi su girmama dokokin ƙasashen mu da ƙa’idojin mu.”

Ya gargaɗi masu neman biza cewa yin amfani da ita ba bisa ƙa’ida ba ko bayar da bayanan ƙarya yayin neman ta yana iya rage amincewar juna a tsakanin ƙasashen biyu.

Ya ce: “Muna kira ga dukkan masu neman biza da su bayar da sahihan bayanai kuma su bi sharuɗɗan biza ɗin su, domin na sani, mafi yawan ‘yan Nijeriya suna yin hakan. Ta yin haka, za mu ƙarfafa ɗorewar zumunci tsakanin ƙasashen mu.”

Ambasada Mills ya kuma yaba wa Idris bisa jajircewar sa wajen kare ‘yancin faɗar albarkacin baki a Nijeriya, yana mai jaddada cewa wannan ɗabi'a ce da ta yi daidai da manufofin Amurka.

Ya kuma yaba wa haɗin kai da ake samu daga hukumomin Nijeriya, ciki har da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, Hukumar Kwastan ta Nijeriya, da Fadar Shugaban Ƙasa, wajen wayar da kan jama’a kan ƙa’idojin biza.

Haka kuma ya shawarci ‘yan Nijeriya da su nemi sahihan bayanai daga shafin soshiyal midiya na Ofishin Jakadancin Amurka kuma su tabbatar da cewa duk wata tambaya da suke da ita za su samu amsa cikin lokaci.

Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya kai wa ɗan gwagwarmaya Bello Galadanci (Ɗan Bello) ziyarar ta'aziyya...
08/08/2025

Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya kai wa ɗan gwagwarmaya Bello Galadanci (Ɗan Bello) ziyarar ta'aziyya bisa rasuwar mahaifinsa Malam Habib.

08/08/2025

YANZU-YANZU: Omoyele Sowore ya shaƙi iskar 'yanci.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya buƙaci Peter Obi da ya dawo jam'iyyar PDP, domin haɗa kai wajen ciyar da ƙasa gaba...
08/08/2025

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya buƙaci Peter Obi da ya dawo jam'iyyar PDP, domin haɗa kai wajen ciyar da ƙasa gaba.

Gwamna Bala Muhammad ya yi wannan kiran ne ya yin da ya karɓi bakwancin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar Peter Obi a gidan Gwamnatin jihar, ya yin ziyarar da ya kai yau Juma'a kamar yadda Punch ta ruwaito.

NELFUND: Jami'ar Tarayya Ta Dutsin-ma Ta Karɓi Naira Biliyan 1.06 Domin Biyan Ƙuɗin Ɗalibai 10,018Jami’ar Tarayya ta Dut...
08/08/2025

NELFUND: Jami'ar Tarayya Ta Dutsin-ma Ta Karɓi Naira Biliyan 1.06 Domin Biyan Ƙuɗin Ɗalibai 10,018

Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina ta bayyana cewa ta karɓi naira 1,065,391,000 daga hukumar NELFUND domin biyan kuɗin karatu na ɗalibai 10,018.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata wasika da Muƙaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Aminu Ado, ya aika wa da Daraktan Ayyuka na NELFUND.

Bisa ga bayanin jami’ar, kuɗin da aka karɓa za su taimaka wajen tabbatar da cewa dukkan ɗaliban da abin ya shafa sun sami damar ci gaba da karatun su ba tare da tangarɗa ba.

Wannan mataki yana cikin tsarin Gwamnatin Tarayya na tallafa wa ɗalibai da rage masu nauyin kuɗin makaranta.

Jami’ar ta yi godiya ga NELFUND da Gwamnatin Tarayya bisa wannan tallafi, tare da bayyana cewa hakan zai inganta cigaban ilimi da tallafa wa marasa galihu a faɗin ƙasar nan.

TIRƘASHI: Za a fara bawa ‘yan gidan yari damar kaɗa ƙuri'unsu a lokutan zaɓe.Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta bayyana cewa z...
08/08/2025

TIRƘASHI: Za a fara bawa ‘yan gidan yari damar kaɗa ƙuri'unsu a lokutan zaɓe.

Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta bayyana cewa za a fara bawa fursunoni damar kaɗa ƙuri'unsu a lokutan gudanar da zaɓe.

Shugaban hukumar zaɓen ta ƙasa Yakubu Mahmood ne ya bayyana haka, ya yin da shugaban hukumar kula da gidajen yari na ƙasa Sylvester Nwakuche ya kai masa ziyara yau Juma'a a Ofishinsa da ke birnin Abuja.

— Jaridar Arewa

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kammala Gyaran  Alau Dam Akan Kuɗi Naira Biliyan 80 Nan Da 2027, Don Inganta Noman Rani Da Samar...
08/08/2025

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kammala Gyaran Alau Dam Akan Kuɗi Naira Biliyan 80 Nan Da 2027, Don Inganta Noman Rani Da Samar Da Wutar Lantarki

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa aikin gyare-gyare da fadada Alau Dam da ke jihar Borno, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 80, zai kammala nan da shekarar 2027. Ministan Ruwa da Tsabtace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar aiki da ya kai wurin aikin a garin Alau, kusa da Maiduguri. Ya ce an fara aikin ne da amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu karkashin shirin Renewed Hope Agenda, domin Dan din ya zama mai amfanarwa sosai, ciki har da ban ruwa don bunkasa noman rani da kuma shirin samar da wutar lantarki a nan gaba.

Ministan ya bayyana cewa aikin ya kasu kashi biyu, inda kashi na farko zai kare a watan Satumba na wannan shekara, domin rage hadarin ambaliyar ruwa a wannan damina. Kashi na biyu kuma zai fara a watan Oktoba kuma ya kammala a watan Maris 2027, wanda zai kai ga kammala sake ginawa da fadada Dam din. Ya ce, bayan kammala aikin, Dam din zai kara inganta samar da ruwan sha ga Maiduguri da kewaye, ya tallafa wa noman rani, tare da bai wa yankin damar samar da wutar lantarki ta hanyar ruwa.

Farfesa Utsev ya gode wa Shugaba Tinubu da Gwamna Babagana Umara Zulum bisa jajircewa wajen ganin aikin ya tabbata, yana kuma kira ga manoma a yankin su daina shuka amfanin gona a gefen Dam din domin kauce wa matsaloli yayin aikin. Ya kuma shawarci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu kan yiwuwar ambaliya, yana mai bayyana cewa aikin na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin ruwa da inganta harkokin noma a Borno da ma kasa baki daya.

08/08/2025

YANZU-YANZU : Ɗan gwagwarmaya Sowore yana ganawa da ‘yanjarida a hedkwatar ‘yansanda da ke Abuja.

Gwamnatin tarayya za ta gina Layin Dogo a tsakiyar birnin Kano da ya kai Naira Tiriliyan 1.5Gwamnatin Tarayya ta sanar d...
08/08/2025

Gwamnatin tarayya za ta gina Layin Dogo a tsakiyar birnin Kano da ya kai Naira Tiriliyan 1.5

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin gina sabon layin dogon jirgin kasa na haske a cikin birnin Kano da kudinsa ya kai Naira tiriliyan 1.5. Shugaban Kwamitin Kidaya Kudin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Abubakar (Bichi) ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai a Kano. Ya ce wannan aiki zai rage matsalolin sufuri a cikin birnin Kano, inda ya kara da cewa irin wannan aikin ana ganinsa a kasashen Turai da yankin Asiya, kuma yana da matukar amfani wajen bunkasa tattalin arzikin jihar bayan kammalawa.

Hon. Bichi ya musanta rade-radin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya sanya ayyuka a Arewa, inda ya bayyana cewa shugaban kasa ya kaddamar da muhimman ayyuka a fannoni daban-daban kamar su gine-gine, lafiya, noma, ilimi da tsaro a yankin. Ya ce daga cikin ayyukan akwai aikin hanyar Kaduna–Zaria–Kano wanda ya kusa kammaluwa, da aikin Kaduna–Abuja mai tsawon kilomita 400 da aka sake bai wa wani kamfani wanda yanzu aikin ya fara tafiya cikin sauri, tare da burin kammala shi kafin karshen zangon farko na shekara mai zuwa. Haka kuma, akwai aikin hanyar Kano–Hadejia mai tsawon kilomita 200 da aka kammala, da kuma hanyar Kano Northern Bypass da ta kai sama da Naira biliyan 250.

Ya bayyana cewa ziyararsu a Kano ta yi daidai da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC domin tsara dabarun samun nasara a zaben 2027. Ya tunatar da cewa a zaben 2023, Kano ta bai wa Shugaba Tinubu kuri’u sama da 500,000 — mafi girma a duk fadin kasar. Haka kuma, taron ya kasance na nuna goyon baya ga tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu nasarar sauya jihohin PDP da dama zuwa hannun APC.

YANZU-YANZU Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 Peter Obi ya sauka birnin Bauchi domin ziyarar duba wasu Makar...
08/08/2025

YANZU-YANZU

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 Peter Obi ya sauka birnin Bauchi domin ziyarar duba wasu Makarantu.

📷- Albarka Radio

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Arewa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Arewa:

Share

Category