
11/08/2023
Labarin Sirri Game Da Kin Amincewa Malam El-Rufai Ya Zama Minista.
Labarin da muke samu shi ne Janaral TY Danjuma na daya daga cikin wadanda suke kokarin hana a ba Malam Nasir El-Rufai minista, kuma yana amfani da Sanata Remi Tunubu, matar Shugaban Kasa ne wurin cinma burinsa. Laifin El-Rufai a wurin T.Y Danjume bai wuce maganar Muslim- Muslim Ticket da ya yi a Kaduna kuma wanda hakan ya taimaka aka yi a Kaduna. Abin da suke nuna wa Shugaban Kasa shi ne in aka ba El-Rufai minista hakan yana iya jefa Nijeriya cikin tashin hankali.
Sannan, Kungiyar Kiristoci ta CAN da na Shi’a na amfani da Shehu Sani wurin hada zanga zanga da kuma rubuta ‘petition’ din da aka kai Majalisar Dattawa. A labarin da muka samu, da farko tsohon sanatan ya so ya yi amfani da Mr La ne wurin mika takardar a majalisa amma Sanata Mr La ya ki amincewa shi ne ya yi amfani da na Kogi West.
Baya ga wadannan, akwai kuma wadanda ke yakin El-Rufai saboda suna tunanin in ya masto kusa da shugaban kasa zai hana su rawar gaban hantsi. Akwai masu son yin takarar Shugaban Kasa kuma suna son duk yadda za a yi su hana duk wani babba daga Arewa da zai iya shugaban kasa yin karfi a kusa da shugaban kasa Tinubu. Daya daga cikin masu yakin El-Rufai a boye shi ne Kashim Shettima, Mataimakin Shugaban Kasa. Duk wadannan masu yaki da El-Rufai a boye saboda hana shi yin karfi suna amfani da Nubu Ribado ne.
Sannan sanin kowa ne matsalar wutan lantarki a Nijeriya na daya daga cikin abin da ke mayar da kasar baya kuma yake kara jefa kasar cikin kangin talauci musamman Arewa. Kuma manyan kasar nan su suke siye da wadannan kamfanonin raba wutan lantarki. Saboda haka sun san El-Rufai in ya zama mininstan wutan lantarki sai ya karya su. Sai ya gwamnati ta kwace kaddarorrinsu kamar yadda ya kudirta wurin tantance shi a majalisa. Saboda haka, su ma sun fito da karfinsu na ganin sun hana El-Rufai zama minista.
In kun lura duk cikin sunayen da aka tura na ministoci daga Arewa babu jajirtacce irin El-Rufai saboda asara
Arewa Hausa Report