HausaLink Media

HausaLink Media đź“° SASHEN LABARAN HAUSALINK MEDIA

Barka da zuwa Sashen Labaran HausaLink Media, inda muke kawo muku sahihan labarai cikin gaggawa da adalci.

Muna wallafa labaran siyasa, tattalin arziki, ilimi, lafiya

Iran ta ƙirƙiri wani sabon jirgi mara matuki da ta yi masa laƙabi da Hadid 110, wanda ke da matsanancin gudu cikin ƙanƙa...
29/07/2026

Iran ta ƙirƙiri wani sabon jirgi mara matuki da ta yi masa laƙabi da Hadid 110, wanda ke da matsanancin gudu cikin ƙanƙanin lokaci kuma ƙasa-ƙasa, sannan yana iya kai farmaki cikin wani yanayi mai k**a da layar zana domin kuwa ba a ganin sa har sai bayan ya ƙaddamar da hari.

Karim Adeyemi mai shekara 24 ɗan kasar Jamus ya sanya hannu kan kwantaragi na shekara 5 da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barc...
26/07/2026

Karim Adeyemi mai shekara 24 ɗan kasar Jamus ya sanya hannu kan kwantaragi na shekara 5 da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona.

Lauyan dake kare waɗanda ake ƙarar ya nemi kotu ta yi musu sassauci tunda sun amince da laifin da s**a aikata, sannan su...
24/07/2026

Lauyan dake kare waɗanda ake ƙarar ya nemi kotu ta yi musu sassauci tunda sun amince da laifin da s**a aikata, sannan suna da mata da yara da kuma iyaye da s**a dogara dasu.

To sai dai mai shari’a Salim Ibrahim ya yi watsi da hakan, inda ya yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai, kuma zai fara aiki ne daga ranar da aka k**a su.

Hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya ICPC ta gano yadda rundunar ƴan sandan ƙasar da wasu ma’aikatun gwamnati biyar s**a f...
23/07/2026

Hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya ICPC ta gano yadda rundunar ƴan sandan ƙasar da wasu ma’aikatun gwamnati biyar s**a fi ko ina yawan jami’ai na bogi.

Shugaban hukumar, Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana haka da yake sanar da sak**akon binciken da s**a yi a tsarin biyan albashi na gwamnati.

Hukumar ta ce ta gano wasu ma’aikata da ake zargin na bogi ne aƙalla su 908 a ma’aikatu da hukumomi 59, inda s**a ƙwato kusan naira miliyan 942 da aka biya waɗannan jami’ai albashi.

SALLAR ROQON RUWA AZARE...MAI MARTABA A MAFI TAUKI DA TAUKI.Mai Martaba Sarkin Katagum Mai Martaba Dr. Umar Faruq II ya ...
22/07/2026

SALLAR ROQON RUWA AZARE...MAI MARTABA A MAFI TAUKI DA TAUKI.

Mai Martaba Sarkin Katagum Mai Martaba Dr. Umar Faruq II ya nuna goyon baya da jagoranci a ci gaba da gudanar da addu’o’in samun ruwan sama a garin.

Ga Duk kan alamu maganar da Magajin garin New York Zohran Mamdani, wanda ya ce ya na nazarin k**a Netanyahu domin miƙawa...
22/07/2026

Ga Duk kan alamu maganar da Magajin garin New York Zohran Mamdani, wanda ya ce ya na nazarin k**a Netanyahu domin miƙawa kotun duniya dake neman sa ruwa a jallo ya sa natanyahu da Donal trump cikin kokwanto ko zai aikata.

Mamdani ya ce babu inda ya dace da Netanyahu da ya wuce Hague wadda ke tuhumar sa da laifukan yaƙi saboda kashe Falasɗinawan da aka yi a Gaza.

Kowacce shekara Netanyahu na ziyartar New York domin halartar taron Majalisar ĆŠinkin Duniya, sai a bana barazanar Mamdani na haifar da cece kuce.

GA DUK ALAMA JAJIRCEWAR DA IRAN TAYI SHINE ZAI KAN JARO YANCIN LEBANON DA MA SAURAN KASASHEN LABAWAN DA AMURKA TA SASU G...
21/07/2026

GA DUK ALAMA JAJIRCEWAR DA IRAN TAYI SHINE ZAI KAN JARO YANCIN LEBANON DA MA SAURAN KASASHEN LABAWAN DA AMURKA TA SASU GABA.

Haka zalika, Trump ya ce zai yi duba kan zargin da ake wa dakarun Isra'ila na buÉ—e wuta kan takwarorinsu na Lebanon.

Shugaban na Amurka ya kuma sake nanata aniyarsa na hana Iran mallakar makamin nukiliya, inda ya ce sun naƙasa ƙarfin sojinta.

Maroko da Senegal da Masar su ne ƙasashe uku da suke kan gaba a wajen iya ƙwallo a nahiyar Afirka, a jadawalin FIFA na b...
21/07/2026

Maroko da Senegal da Masar su ne ƙasashe uku da suke kan gaba a wajen iya ƙwallo a nahiyar Afirka, a jadawalin FIFA na baya bayan nan, inda ta zama ta huɗu duk da cewa ba ta halarci Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 ba. Sauran wasau ƙasashen da suke cikin goman farko sun haɗa da Kongo DRC da Afirka ta Kudu.

A Ranar Jumma'a, Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Canada da haddasa hadarin hayaƙi da ya fito daga gobarar daji da ...
20/07/2026

A Ranar Jumma'a, Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Canada da haddasa hadarin hayaƙi da ya fito daga gobarar daji da ya lulluɓe kaso mai yawa na Amurka, yana mai barazanar ƙara kuɗin wannan gurɓata iskar cikin harajin da zai ƙaƙaba wa kayayyakin da Canada ke fitartwa a Amurka.

A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, mazaunin fadar White House ɗin ya yi hasashen cewa Ottawa bata tafiyar da dazukanta yadda ya k**ata, inda yake zargin Canada da ƙyale iska mai datti da haɗari ta afka wa Amurka. Trump ya nuna cewa zai iya magana daga baya da Firayimministan Canada domin gano matakan da ake shiryawa don sauƙaƙa yanayin.

Shugaban na Amurka ya zargi Canada da ƙin ɗabbaka matakai na kula da daji da kuma nome ciyawa, yana mai bayyana shi a matsayin "rashin kula na gangan." Ya ce waɗannan lamurran na faruwa a ko wace shekarar kuma Amurka na rasa "biliyoyin daloli" sak**akonsu.

Yaki dai na shirin kara tsamari a gabas ta tsakiya.
20/07/2026

Yaki dai na shirin kara tsamari a gabas ta tsakiya.

Address

Abuja
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HausaLink Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HausaLink Media:

Shortcuts

Share