27/02/2024
KAFIN MU SAMI 'YANCI SAI MUN NEMI 'YANCI (1)
Shinfida da Gabatarwa:
Kamar yadda na rubuta a taken rubutu kafin mu sami 'yanci sai mun nemi 'yanci , to haka wanan Magana take daga nan har birnin Sin.
Ba'a taba yin wata al'umma ba da ta sami 'yanci batare da aiki Tukuru domin samun 'yanci ba a Tarihin Duniya, kuma ba za'a fara daga Nigeria ba.
Duk wata Daula ko wata ƙasa da muke kallo ta zama abin kwatance a yau, ta fannin ci gaban tattalin arziki, tsaro da rayuwa mai inganci, to wasune s**ayi aiki domin samar da wanna yanayin, da yanzu wasu suke mora kuma suke Girmamawa tare da sanya Albarka ga gwarazan da s**a samar da wanna yanayin.
Shi 'Yanci Nemansa ake a wajen wanda ya tauye ma al'umma shi, sannan a kwace shi ta yadda daga wanan lokacin to wannan mai tauye 'yanci din ya rabu da ikon da yake dashi na Bautarwa ga al'umma sannan dole ya tabbatar bashi da ta cewa a cikin al'amurran da s**a shafi wannan al'umma, kuma wannan al'umma bata bukatar izninsa wajen yin abinda ya dace ga Al'ummar ta, a takaice de Gudanar da wannnan al'umma ya dawo hannunta Dari Bisa Dari.
Tarkon Masu Bautarwa Ga waɗan da Ake Bautarwa:
Koda mutum kiwo yake to dole ne yasan irin dabbar da yake kiwo, dakuma halayyar ta a maban-bantan yanayi, Ya takeyi ida tana jin yunwa, Yaya takeyi idan tana jin ƙishirwa, wanne irin abinci tafi so, ya takeyi idan bata da Lafiya, ya takeyi idan ta fusata, wanne irin kololuwar mataki take dauka idan tayi Fushi?
Shin Halbi take ? ko Tunkuyi take ? shin Cizo take ? ko kuma kuka takeyi kawai ?
Kuma Dole wannan Mai kiwo yayi tanadin Yadda zai shawo kanta kowanne irin yanayi take ciki, ta hanyar amfani da dabaru, tsoratarwa, Yaudara, Da duk wata hanya mai yiwuwa, Shiyasa Masu kiwon suke samun damar sarrafa abin kiwonsu cikin sauki, koda kuwa sun nufi yanka abin da suke kiwon ne to turjiyar da zasu samu kadance kuma baze hana yanka abin kiwon ba, kuma sauran Dabbobin Bazasu iyayin komai ba. Domin Shi mai kiwon yasan Halayyar abin da yake kiwo ciki da bai a kowanne yanayi.
Dan Adam Kamar Abin kiwo ne Ga Masu Bautar dashi:
Kamar yadda mukayi bayani a sama yadda Masu kiwo Sukeyi na dabba da Allah bai bata Daraja , Ta Hankali kamar dan Adam ba, da yadda Masu kiwon suke ɓata lokaci wajen karantar Halayyar abin kiwonsu, to inaga Masu Sarrafa Dan adam domin su bautar dashi ?
To masu bautar da dan adam da suke kwace masa dukkan 'Yanci na rayuwa da zamantakewa, suma suna karantar Al'ummar da zasu bautar ne tun kafin su mamaye ta, Dole su karanci Dabi'a ta wannnan Al'umma, Shin wannnan Al'umma Tana da tsarin gudanarwa ne , Yayi tsarin shugabancin su yake, Idan akazo musu da bakon abu yaya Sukeyi, Idan sunajin Yunwa yaya Sukeyi, idan an kwace musu Wani abu nasu mai girma a wajensu yaya Sukeyi, Maganar wa sukeji, Idan Sunje Kololuwar yin fushi da tunzura iya me suke iya yi, Shin suna da juriya da Hakurin gwagwarmayar kwato abinda aka kwace musu ko de kawai bari sukeyi ya kwatu?
dade sauransu.
Sannan Masu Mulkin Mallaka suna tanadin ya Zasuyi su samar da maganin waɗan nan yanayi na al'ummar sannan kuma su Bautar da ita, ba tare ma ita Al'ummar tasan bautar da ita ake ba, b***e tayi Yunkurin Neman Hakkinta.
To waɗan da suke bautar da al'ummar Nigeria dama Nahiyar Afirka baki ɗaya, suna Bautar da Al'ummar ne ta hanyar amfani da duk wata hanya ta sarrafawa da suke da ita kuma har gobe A Kangin Bauta Nahiyar Afirka take, Saide bautarwar da ake yiwa wani wajen tafi ta wani wajen rashin Imani.
Zamu ci Gaba Da wannan rubutu Insha Allahu, a fita ta 2.
©️Ibn Abubakar Alhausawy