23/07/2025
LABARUN DUNIYA
PDP TA OSUN TA MARA BAYA GA TAZARCEN TINUBU A 2027
Jam’iyyar PDP reshen jihar Osun ta amince da mara baya ga neman tazarcen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a babban zaben da ke tafe a 2027.
PDP ce ke da gwamnati a jihar ta Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya karkashin gomna Ademola Adeleke.
A zaben 2023, dan takarar PDP Atiku Abubakar ne ya yi nasara da tazara marar yawa kan shugaba Tinubu na APC.
Kakakin gwamna Adeleke, Adewale Rasheed ne ya karanta matsayar jam’iyyar da nuna duk da haka Adeleke na jam’iyyar PDP don raderadin zai sauya sheka zuwa APC ba daga gare shi ba ne.
Matsayar ta kara da cewa Adeleke zai sake takarar gomna a watan Agustar badi a inuwar PDP.
Masu sharhi na ganin hakan a matsayin wasu dabarun siyasa duk da sanarwar na nuna ai jihar Osun gidan shugaba Tinubu ne.
SANATA NATASHA TA YI YUNKURIN KOMAWA ZAMAN MAJALISAR DOKOKI
Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta yi yunkurin komawa zama majalisar dattawa a Talatar nan.
Natasha da rakiyar magoya baya ciki da ‘yar gwagwarmayar siyasa Aisha Yesufu ta yi kokarin shiga majalisar amma jami’an tsaro ba su ba da dammar hakan ba.
Natasha dai ta na aiki ne da hukuncin babbar kotun taraiya da ta ce umurci dawo da ita majalisar bayan dakatar da ita na tsawon wata 6.
Majalisar dai ta nuna bat a samu umurnin kotun ba kuma matakin Natasha k**ar rashin fassara umurnin kotun ne daidai gabanin kammalar wa’adin dakatarwar.
YUNWA TA YI SANADIYYAR MUTUWAR YARA 21 A GAZA
Tsananin yunwa ya yi sanadiyyar mutuwar yara 21 a Zirin Gaza a cikin sa’a 72 kacal k**ar yanda majiyoyi daga asibitin Annasr su ka baiyana.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin duniya ke kara nuna mawuyacin halin da yaran ke ciki a Gaza.
Kazalika akwai barazanar shigar yunwa don karancin abinci da ke abbadar al’ummar Falasdinawa a yankin da ke fama da hare-haren Isra’ila.
Alkaluma sun tabbatar da kashe fiye da mutum 1000 da ke fafutukar karbar abinci daga wani shirin agaji da majalisar dinkin duniya ke jagoranta a Gaza.
Sojojin Isra’ila kan kai hari da kan hallaka wadanda su ka taru a layin karbar kayan abinci da fakewa da cewa hare-haren na auna ‘yan kungiyar Hamas ne.
Jakadiyar taraiyar turai Kaja Kallas ta yi Allah wadai da kai hare-hare ga wadanda su ka taru don karbar kayan agajin abinci.
Kallas ta nuna ba yanda za a kare wadannan hare-hare don haka ma ta yi magana da ministan wajen Isra’ila Gideon Saar kan bukatar bad a kariya ga masu karbar kayan agaji ko tabbatar da kare rayukan al’umma a yankin.
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya yi kira da babbar murya na kare mutane masu taruwa don karbar kayan tallafin.
SAUDIYYA TA MARA BAYA GA SAKE GINA SHAM
Saudiyya ta mara baya ga aikin sake gina kasar Sham bayan shafe shekaru ta na fama day akin basasa.
In za a tuna mayakan tahrir sun yi nasarar kifar da tsohuwar gwamnatin Bashar Al’asad inda Ahmad Al-Sharaa ya zama jagoran gwamnatin kasar.
A zaman majalisar zartarwar Saudiyya karkakashin jagorancin Sarki Salman, Saudiyya ta ce ya na da muhimmaci a kwantar da duk wata fitina a Sham da taimakawa kasar ta sake farfadowa kuma tuni Saudiyya ta ware tallafi ga al’ummar Sham.
Kazalika Saudiyya ta mara baya ga matsayar ministocin wajen kasashe 28 kan kawo karshen yakin Gaza da barin kayan agaji su na shiga Zirin.
Kasar ta Larabawa ta bukaci kasashen duniya su yi tsayin daka wajen ganin lallai Isra’ila ta daina kawo tarnaki ga shigar agaji ga al’ummar Gaza.