28/08/2024
Ladubban Hira da Mutane
1- Ka guji ƙarya, da gulma, da yi da mutane, da yi musu tonon silili.
2- Yawaita amfani da kalmomin kyautata zance: "Don Allah", "in ba damuwa", "na gode", "madalla!"
3- Kada ka shagaltar da abokan hirarka da yawan faɗa musu matsalolinka. Ka zama mai yakana.
4- Kada ka riƙa tambayar abokin hirarka keɓantattun abubuwa da s**a shafi rayuwarsa.
5- Idan wani yana ba da labarin da ka sani, kada ka katse hanzarinsa, bari ya kai gaci, kana mai nuna labarin ya shige ka.
6- Kada ka wawantar da ra'ayin wasu, ka wulakanta su.
7- Kada ka nuna ra'ayinka shi ne ƙololuwar gaskiya. Ka riƙa cewa: A ganina.
8- Ka riƙa rarraba dubanka ga waɗanda kake zantarwa, kada ka sa mutum ɗaya a gaba kana yi masa kallon ƙurilla.
9- Ka guji gamammen hukunci a kan mutane, kamar ka ce "Duk mutane sun lalace.."
10- Kada ka ce wa mai zance: "ƙarya kake" haka gatsal. Ka koyi cewa: Ni kuma na ji an ce kaza ne ya faru.
* Umar bn Khattab (RA) ya ce: "Idan aka wurgo kalmar da za ta ɓata maka rai, ka sunkuya ta wuce ta samanka."
* An tambayi Abbasu ɗan AbdulMuɗɗalibi (RA): Da kai da Manzon Allah (SAW) wane ne babba?
Ya ce: "Shi ne babba, amma an haife ni kafin haihuwarsa."
* Aɗa'u ɗan Abu Rabahi ya ce: Mutum yakan zantar da ni wani labari, sai in nutsu, ina sauraronsa, duk da tun kafin a haife shi, na san wannan labarin da yake gaya mini."
* Ma'amunu ya tambayi sunan wani mutum da ake kira: Sayyid ɗan Anas, ya ce: "Kai ne Sayyid?"
Mutumin ya ce: "A'a, Sarkin muminai shi ne sayyid (shugaba), ni ɗan Anas nake."
Dr. Aminu Isma'il