
26/06/2025
Ba zan goyi bayan Tinubu ba a zaben 2027 muddin ya canza Shettima - Sheikh Jingir
Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’a Wa’ik**atis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bayyana matsayansa kan zaben 2027 mai zuwa, inda ya ce, ba zai goyi bayan takarar Bola Tinubu ba a zaben 2027 matukar ya canza Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.
A cewar Sheikh Jingir, “Ni da wasu na kusa da ni mun goyi bayan Tinubu da Kashim, kuma za mu sake goyon bayan takararku a tare. Duk wani yunkuri sabanin haka ba na tare da shi kuma ba zan goyi baya ba saboda a baya sun amince su yi aiki tare.
Sheikh Jingir ya bayyana hakanne yayin wani taron wa’azi a masallacinsa na ’Yan Taya da ke Jos, babban birnin jihar Filato.
Ya kara da cewa, “Na ji akwai wasu mutane marasa kishin kasa daga ciki da wajen APC da ke kokarin lalata alakar da ke tsakanin Tinubu da Kashim domin cimma mummunar manufarsu. To mu ba ma maraba da wannan Shugaba Tinubu.