Sabuwar Nigeria

Sabuwar Nigeria Tare ya kamata mu gina SABUWAR NAJERIYA

Za a Kammala Aikin Gidaje Na Renewed Hope City A Kano Cikin Mako Shida Masu Zuwa — Gwamnatin TarayyaGwamnatin Tarayya ta...
25/07/2025

Za a Kammala Aikin Gidaje Na Renewed Hope City A Kano Cikin Mako Shida Masu Zuwa — Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta ta kammala aikin gina gidaje na Renewed Hope City da ke Kano cikin mako shida, domin samar wa ‘yan Najeriya mafita kan matsalar rashin gidaje. Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Ahmad Musa-Dangiwa, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin ziyarar duban aikin da ya kai.

Ministan ya ce yana gamsuwa da yadda aikin ke tafiya da kuma ingancin aikin da ake yi, yana mai jaddada cewa aikin na tafiya daidai da yadda aka tsara. Ya bayyana cewa mafi yawan aikin da ya rage yanzu ya ta’allaka ne da gyare-gyaren cikin gida da kuma ayyukan wajen gini kamar shigar lantarki da tsarin rarraba ruwa.

Ministan ya samu rakiyar Ƙaramin Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Yusuf Abdullahi Ata, da wasu manyan jami’an ma’aikatar. Aikin na Renewed Hope City yana daga cikin shirin gwamnatin tarayya na rage gibin gidaje a kasar da samar da mafaka mai sauƙi ga ‘yan kasa.

Rayuwar Marigayi Sarkin Gusau cike take da hidima da sadaukarwa ga jama’a —Shugaba TinubuShugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu...
25/07/2025

Rayuwar Marigayi Sarkin Gusau cike take da hidima da sadaukarwa ga jama’a —Shugaba Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar Sarkin Katsinan Gusau, Dr Ibrahim Bello, wanda ya rasu da safiyar Juma’a a birnin tarayya Abuja yana da shekaru 71 a duniya.

A cikin wata sanarwa daga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai da dabarun watsa bayanai, Mista Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar marigayi sarkin a matsayin babban rashi da ya wuce iyakar masarautar Gusau, yana mai cewa rayuwarsa cike take da hidima da sadaukarwa ga jama’a a matakai daban-daban na rayuwa.

Shugaban ƙasa ya yabawa marigayin da kishinsa da jajircewa wajen kula da walwala da ci gaban jama’arsa. Ya ce za a ci gaba da tunawa da sarkin bisa jagoranci na nagarta da baiwar jagoranci da Allah ya h**e masa.

Shugaba Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar Zamfara, al’ummar Gusau da kuma iyalan marigayin, tare da addu’ar Allah ya jikan sa, ya sa Aljannah Firdausi ta zama makoma gare shi.

An zaɓi Farfesa Nentawe Yilwatda A Matsayin Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Bayan Saukar GandujeJam’iyyar APC ta zaɓi Minis...
24/07/2025

An zaɓi Farfesa Nentawe Yilwatda A Matsayin Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Bayan Saukar Ganduje

Jam’iyyar APC ta zaɓi Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar na ƙasa. Zaɓen ya gudana ne a ranar Alhamis yayin zaman Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar, inda aka zaɓe shi ba tare da hamayya ba, don maye gurbin Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya sauka daga mukamin bisa wasu dalilai na lafiya.

Farfesa Nentawe, wanda aka haifa a ranar 8 ga watan Agusta, 1968 a garin Dungung, ƙaramar hukumar Kanke ta Jihar Filato, fitaccen masani ne a fannin Injiniyan na’ura mai kwakwalwa da Lantarki. Ya yi karatunsa na farko a Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Makurdi, sannan ya samu digirinsa na biyu daga ATBU Bauchi, da kuma digirin digirgir daga Jami’ar Najeriya Nsukka. Ya kwashe sama da shekaru 26 yana koyarwa da gudanar da manyan ayyuka a jami’o’i, kuma ya taka rawa a matsayin darektan ICT na farko a jami’ar Makurdi.

Baya ga aikin ilimi, Farfesa Yilwatda ya taka rawa a bangaren kirkire-kirkire da sauyi ta fannin fasaha a ciki da wajen gwamnati. A matsayinsa na kwararre a harkar sadarwa da fasahar zamani, ya yi aiki da manyan kungiyoyin duniya irinsu EU, UNICEF, Bankin Duniya da TECHVILE USA. A shekarar 2017, ya zama kwamishinan zaɓe na INEC, inda ya kawo muhimman sauye-sauye a tsarin zaɓe da s**a haɗa da tsarin kada kuri’a ga ’yan gudun hijira da masu buƙata ta musamman.

Yanzu da ya zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Yilwatda ya shigo da ƙwarewa ta musamman, hangen nesa, da sadaukarwa da zai amfani jam’iyyar da ƙasa baki ɗaya. A matsayinsa na shugaban kamfen ɗin Tinubu/Shettima a Jihar Filato, kuma Ministan Jinƙai, yana da zurfin alaƙa da ɓangarori da dama na gwamnati da ƙungiyoyin ci gaba, wanda hakan zai taimaka wajen jagorantar jam’iyya cikin hadin kai da nasara.

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar da Sabbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji a NajeriyaGwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin jag...
24/07/2025

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar da Sabbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji a Najeriya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kaddamar da sabbin cibiyoyi guda uku na zamani domin kula da masu fama da cutar daji (cancer) a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Cibiyoyin sun haɗa da na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) a jihar Edo, Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya (UNTH) da ke Enugu.

Ministan Yada Labarai na Ƙasa, ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce wannan ci gaba wani ɓangare ne na shirin farfaɗo da harkar lafiya da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa a fadin ƙasa.

A cewar Ministan, shi da sauran abokan aikinsa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kudi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin kaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a jihar Katsina.

Cibiyoyin da aka kaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sabbin cibiyoyin maganin ciwon daji guda shida a manyan asibitocin koyarwa na Tarayya a ƙasar.

Wannan ci gaba wani muhimmin mataki ne wajen rage wahalar da marasa lafiya ke fuskanta wajen samun ingantacciyar kulawa, da kuma hana fita ƙasashen waje don neman magani.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa sauran cibiyoyin da s**a rage za su kammala nan ba da jimawa ba domin cika alkawarin samar da ingantaccen tsarin lafiya ga kowa da kowa a Najeriya.

Gwamantin tarayya ta biyawa ɗaliban jami’ar Dutsin-Ma fiye da dubu 10 kuɗin makarantaA ci gaba da aiwatar da shirin lamu...
24/07/2025

Gwamantin tarayya ta biyawa ɗaliban jami’ar Dutsin-Ma fiye da dubu 10 kuɗin makaranta

A ci gaba da aiwatar da shirin lamunin karatu na Tallafin Kuɗin Karatu ta Ƙasa (NELFUND) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma, jihar Katsina, ta tabbatar da karɓar Naira biliyan ɗaya da miliyan sittin da biyar da dubu ɗari uku da casa’in da ɗaya (₦1,065,391,000) domin biyan kuɗin makaranta na dalibanta.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da jami’ar ta fitar, wadda ke ɗauke da sa hannun Muƙaddashin Shugaban Makarantar, Farfesa Aminu Ado. A cewar takardar, kuɗaɗen za su biya kuɗin karatun dalibai 10,018 da s**a cancanci samun tallafin a wannan zangon karatu.

Wannan mataki ya zo daidai lokacin da ɗalibai da iyayensu ke fuskantar matsin tattalin arziki, kuma zai taimaka wajen saukaka nauyin kuɗin makaranta, da kuma karfafa damar koyo da cigaba a fannin ilimi.

Shirin NELFUND dai na daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu na tallafa wa fannin ilimi, ta hanyar samar da lamunin karatu da za a biya a hankali bayan kammala karatu da samun aiki.

Shugaba Tinubu Ya Tattauna da Gwamnonin APC Kafin Taron Kwamitin Zartaswa na ƘasaShugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana...
23/07/2025

Shugaba Tinubu Ya Tattauna da Gwamnonin APC Kafin Taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ganawar ta gudana ne kafin babban taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa NEC na jam’iyyar da za a gudanar a ranar Alhamis a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban ƙasa.

Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, wanda ke jagorantar Ƙungiyar Gwamnonin APC (Progressive Governors Forum), ne ya jagoranci sauran gwamnonin zuwa wannan taro da aka gudanar.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Gwamna Uzodimma ya bayyana cewa ganawar na da nufin karfafa jam’iyya da kuma inganta kyakkyawan shugabanci a matakin jihohi da ƙasa baki ɗaya. Ya ce sun tattauna hanyoyin da za a bi wajen ƙarfafa jam’iyyar daga tushe, tun daga matakin ƙananan hukumomi, zuwa jihohi har zuwa ƙasa baki ɗaya.

A kan yiwuwar fitowar sabbin matakai ko sauye-sauye daga taron na NEC, Uzodimma ya ce: “Ba za mu iya hango abin da za a cimma ba har sai mun isa wurin taron gobe.” An dai tsara taron NEC domin duba manyan batutuwan da s**a shafi jam’iyyar da kuma tsara sabbin dabarun ƙarfafa haɗin kai da shugabanci mai tasiri.

Daga cikin muhimman abubuwan da ake sa ran taron zai warware har da batun nada sabon shugaban jam’iyya na ƙasa, biyo bayan murabus din Dr. Abdullahi Umar Ganduje a watan Yuni.

Jaridar Blueprint ta karrama Sanata Babangida a matsayin mai yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya.A yau, T...
22/07/2025

Jaridar Blueprint ta karrama Sanata Babangida a matsayin mai yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

A yau, Talata, 22 ga Yuli, 2025, Sanata mai wakiltar Jigawa Arewa maso Yamma, Sanata Babangida Hussaini, ya karɓi lambar yabo daga Jaridar Blueprint a matsayin Sanatan da yayi fice a gwagwarmaya wajen yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

An gudanar da bikin bayar da lambar yabon ne a dakin taro na Ladi Kwali Hall, dake otal din Sheraton a Abuja, inda Mai Martaba Sarkin Nupe ya mika masa lambar yabon.

A cikin jawabin godiya da ya gabatar, Sanata Babangida ya bayyana cewa wannan karramawa na da matuƙar muhimmanci gare shi, ba kawai a matsayin ɗan majalisa ba, har ma a matsayin ɗan ƙasa da ya shaida illar da sha da fataucin da miyagun ƙwayoyi ke haddasawa ga matasa, iyalai da makomar al’umma.

Sanatan ya kuma ce ya sadaukar da wannan lambar yabo ga matasa masu ƙwazo da jajircewa na Jigawa Arewa maso Yamma da na fadin Najeriya, waɗanda ke ƙoƙarin gina kyakkyawar rayuwa duk da ƙalubalen da suke fuskanta.

Haka kuma, ya yaba da irin gudunmawar da kungiyoyi da mutane daban-daban ke bayarwa wajen wayar da kai, goyon baya, da kuma ceto waɗanda s**a fada tarkon miyagun ƙwayoyi.

Shugaba Tinubu Ya Bada Tabbacin Dorewar Tsaro da Zaman Lafiya a NajeriyaShugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa...
22/07/2025

Shugaba Tinubu Ya Bada Tabbacin Dorewar Tsaro da Zaman Lafiya a Najeriya

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ’yan Najeriya da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen dawo da tsaro, doka da oda a duk fadin ƙasar nan, musamman a yankunan da s**a fi fuskantar matsalolin rashin tsaro. Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata ta bakin Mai Ba Shi Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, yayin kaddamar da sabbin gidaje a Jihar Kaduna.

Aikin gina gidajen, wanda aka aiwatar tare da haɗin gwiwar Qatar Charity Organisation, na daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na dawo da martabar al’ummomin da s**a fuskanci hare-haren ’yan bindiga da tashe-tashen hankula.

Ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba wajen dawo da zaman lafiya a Jihar Kaduna. Ya kara da cewa gwamnatin sa za ta mayar da hankali kan bukatun ’yan ƙasa, musamman wadanda s**a rasa matsuguni ko s**a rasa ’yan uwa sakamakon rikice-rikice.

Shugaba Tinubu ya jinjinawa Gwamnatin Kaduna, Ofishin NSA da Babban Hafsan Tsaro bisa hadin gwiwa da s**a nuna ta hanyar amfani da dabarun yaki da na sulhu domin shawo kan matsalar tsaro. Ya bayyana nasarorin da aka samu kamar sake bude kasuwar Birnin Gwari da komawar manoma da aka raba da gonakinsu a matsayin alamun ci gaba da murmurewa.

Daga karshe, ya godewa Qatar Charity bisa tallafin da ta bayar, yana mai jaddada cewa yaki da ta’addanci yana da kalubale, amma yana daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin sa ta fi mayar da hankali a kai.

NNPC Ta Tura Sama da Naira Tiriliyan 6 Asusun Tarayya Cikin Watanni Biyar. * Ta Bayyana Ribar Naira Biliyan 905 a Yunin ...
22/07/2025

NNPC Ta Tura Sama da Naira Tiriliyan 6 Asusun Tarayya Cikin Watanni Biyar.

* Ta Bayyana Ribar Naira Biliyan 905 a Yunin 2025

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC Ltd.) ya bayyana cewa ya tura Naira tiriliyan 6.96 zuwa Asusun Tarayya cikin watanni biyar na farkon shekarar 2025. Wannan na kunshe ne a cikin Rahoton Watan Yuni da kamfanin ya fitar a ranar Litinin.

Rahoton ya nuna cewa kamfanin ya samu riba bayan fitar haraji da ta kai Naira biliyan 905 a watan Yuni, ta kuma samu Naira tiriliyan 1.054 a watan Mayu da ya gabata.

A cewar rahoton, yawan kuɗin da NNPC ta samu daga watan Janairu zuwa Mayu 2025 ya karu zuwa Naira tiriliyan 6.961, idan aka kwatanta da tiriliyan 5.583 da aka samu daga Janairu zuwa Afrilu.

Rahoton ya kara da cewa ana samun danyen mai da ya kai ganga miliyan 1.68 a kowace rana a watan Yuni, adadi mafi girma da aka samu tun farkon shekarar nan. Haka kuma, samun iskar gas ya karu daga Standard Cubic Feet biliyan 7.352 a rana a watan Mayu zuwa Standard Cubic Feet biliyan 7.581 a rana a watan Yuni.

A bangaren wadatar man fetur, rahoton ya bayyana cewa akwai ci gaba, inda samun man fetur a tashoshin sayar da mai na NNPC ya karu daga kashi 62% a Mayu zuwa 71% a Yuni.

Baya ga haka, ayyukan gine-ginen bututun gas masu muhimmanci kamar Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK) sun kai kashi 83% na kammala aiki, daga 81% a watan da ya gabata. Bututun OB3 kuwa ya kai kashi 96%.

Duk da cewa samun damar amfani da bututun mai ya dan ragu daga 98% zuwa 97%, rahoton ya bayyana nasarar kammala gadojin kogin Neja da ke cikin aikin AKK, wanda hakan ya rage hadarin da ke cikin gina bututun gaba daya. Har ila yau, an fara duba fasahar da za a yi amfani da ita wajen kammala gadar kogin OB3 bisa ilimin da aka samu daga aikin AKK.

Dangane da gyaran matatun mai na Fatakwal, Warri da Kaduna, rahoton ya ce ana ci gaba da duba tsarin da matatun ke ciki.

A fannin hidimar al’umma, NNPC ta sanar da gudanar da shirin wayar da kan matasa kan ilimin kudi ga sama da matasa 67,000 masu bautar ƙasa (NYSC) a watan Yuni kadai, wanda ya kai jimillar wadanda s**a ci gajiyar shirin zuwa 870,383.

SANATA BABANGIDA YA TALLAFA WA MANOMA DA TIRELA 12 NA TAKI A SHIYYAR JIGAWA AREWA MASO YAMMASanata Babangida Hussaini ma...
22/07/2025

SANATA BABANGIDA YA TALLAFA WA MANOMA DA TIRELA 12 NA TAKI A SHIYYAR JIGAWA AREWA MASO YAMMA

Sanata Babangida Hussaini mai wakiltar Jigawa Arewa maso Yamma a majalisar dattawa ya raba tirela 12 na taki ga manoma, da ƙungiyoyin manoma dake shiyyar sa domin tallafa wa harkar noma da inganta samar da abinci.

A yayin kaddamar da rabon a karamar hukumar Sule Tankarkar a ranar Talata, Sanata Babangida ya bayyana cewa kowacce daga cikin ƙananan hukumomi 12 da ke cikin shiyyar sa za ta samu tirela guda ɗaya domin rabawa manoma.

Ya bayyana cewa wannan tallafi na musamman an tsara shi ne domin ƙarfafa noman damina da kuma ƙara yawan amfanin gona a yankin, jihar Jigawa da ma ƙasar Najeriya gaba ɗaya, tare da nufin tabbatar da ingantacciyar tsaro ta fuskar abinci.

Sanatan ya ce taki yana daya daga cikin muhimman abubuwan da ke tabbatar da nasarar noma, kuma yana aiki kafada da kafada da hukumomin gwamnatin tarayya domin ganin an tabbatar da wadatar taki, saukin samu sa da kuma rangwamen farashi ga manoman shiyyar.

A cewarsa, yayin da kowacce karamar hukuma ta samu tirela guda ɗaya domin rabawa manoma a matakin mazaba, an kuma ƙara wasu tirela takwas (8) domin ƙungiyoyin manoma.

“A matakin mazabu, muna niyyar bai wa ’yan jam’iyyarmu ta APC tallafin, yayin da tirela takwas kuma muka ware su ga ƙungiyoyin manoma domin ƙara musu ƙarfi da ƙarfin aiki.” inji shi

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Raya Arewa maso Yamma (North-West Development Commission - NWDC), Farfesa Abdullah Shehu Ma’aji, ya bayyana cewa rabon takin na cikin tsarin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin bunkasa tsaro na abinci, kawar da talauci da samar da ayyukan yi ga matasa.

Farfesa Ma’aji ya tabbatar da cewa hukumar NWDC za ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka da tsare-tsare da za su inganta rayuwar al’umma da ci gaban tattalin arziki a yankin Arewa maso Yamma.

Shi ma da yake jawabi a madadin shugabannin ƙananan hukumomi 12 na shiyyar, Shugaban Karamar Hukumar Sule Tankarkar, Malam Tasiu Adamu, ya yaba da wannan kyakkyawar gudunmawa daga Sanata Babangida, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewar Sanatan wajen cika alkawari da tallafa wa jama’a.

“Za mu tabbatar da cewa an rabawa manoman da aka nufa da wannan tallafi, kuma za mu ɗauki matakan da s**a dace domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon.”

Ya kuma shawarci manoman da s**a amfana da su yi amfani da takin yadda ya kamata domin cimma burin da aka sanya gaba, wato ƙara yawan amfanin gona da habaka harkar noma a yankin.

21/07/2025

Bayanin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan yaɗa labarai Malam Abdulaziz Abdulaziz ya yi karin haske kan matakan gwamnatin tarayya na tattalin arziki da nasarorin da aka samu.

Yayi jawabin ne lokacin taron kungiyar Arewa Progressive Youth da akayi a Kano ranar Lahadi.

21/07/2025

Tsarabar Mako daga fadar shugaban ƙasa mai ɗauke da ayyukan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar a cikin makon da ya gabata.

Address

Fct Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sabuwar Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sabuwar Nigeria:

Share

Category