31/10/2023
Zipline Bai Nuna Ban-Banci Tsakanin Ma'aikatansa Mata Da Maza- Faith
Daga Abubakar Abba
Daya daga cikin matan da ke aiki a kamfanin Zipline a sashen kula da tashin jiragen sama maras matuki wato Drone, Faith Sunday ta bayyana cewa, Zipline bai nuna ban-banci a tsakanin ma'aikatansa mata da maza.
Faith ta bayyana hakan a hirarta da tawagar ‘yan jarida da s**a ziyarci cibiyar Zipline da ke a Pambegua a jihar Kaduna, inda kamfanin ke tura magunan gwamnatin jihar Kaduna zuwa ga surkukin yankunan da ke a da wahalar shiga da ke a jihar, ta hanyar yin amfani da jirage mallakar kamfanin Zipline maras matuki.
Ta ce, a Zipline ta na gudanar da yin aikin gyaran jiragen idan sun samu wata matsala bayan sun kai magungunan sun dawo cibiyar.
Kazalika Faith ta ce, kamfanin Zipline na karfafa wa daukacin ma'aikatansa, musamman mata guiwa wajen gudanar da ayyukansu ba tare da wata tsangwama ba.
Faith ta ce, bayan ta yo karantun kimiyya ne da kuma Zipline ya dauke ta aiki, sa kuma ta kara samun wata kwarewa sanin makamar aiki a kamfanin na Zipline.
A karshe, Faith ta yi kira ga mata 'yan uwanta da su rungumi fannin ilimin kimiyya, inda ta ce, kar mata su ga kamar ba za su iya yin aikin ba domin fannin ba wai na nuna karfi bane kwarewa kawai akin ke bukata.