25/07/2025
Na yi aure shekaru biyu da s**a wuce. Ina aiki a wata makarantar sakandare a matsayin mai lissafi (accountant), ina samun albashi ₦110,000 a kowane wata.
Kwana biyu kacal bayan aure, mijina ya karɓi katin ATM ɗina. Duk lokacin da albashi ya shigo, shi ne ke cire duk kuɗin, ya ɗauki ₦70,000, ya bani ₦40,000 in yi komai da shi – abinci, sufuri, da duk wasu buƙatun gidan.
Na tambaye shi sau ɗaya, me yake yi da sauran kuɗin? Sai ya ce yana amfani da shi ne wajen taimaka wa harkar kasuwancinsa na dinki. Na kai ƙorafi wajen mahaifiyata, amma ta ce na yi haƙuri, ai shi mijina ne.
Wata rana, bayan watanni na yin shiru, na ce masa ya bar ni in yi amfani da cikakken albashina wata guda kacal don na sayi takalma da kayan zuwa aiki. Abin da ya ce kawai shi ne: “Ke wawiya ce.” Ya ce in ci gaba da amfani da abin da nake da shi. Da na dage, sai ya buge ni da bel.
Na kasa jurewa, sai na je wurin shugabarmu a makaranta, na gaya mata halin da nake ciki. Ta bani shawara na bude sabon asusun ajiya, kuma ta shirya yadda albashina zai rika zuwa rabin-rabi — ₦60,000 zuwa tsohon asusun, ₦50,000 zuwa sabon na sirri.
Na yaudare shi cewa makaranta ta rage albashi zuwa ₦60,000 saboda rage ma’aikata. Da albashi ya shigo, sai ya cire ₦40,000, ya bani ₦20,000. Na tambaye shi ta yaya zan iya kai kaina aiki da waɗannan kuɗin? Ina tambayar kuɗin da ya ke ajiyewa ma? Cikin dare sai ya buge ni da ƙarfi, ya dukar min cikin da nake da ciki — har na zubar da juna biyu.
Bayan na fita daga asibiti, sai ya sake yi min barazana: idan na sake tambayar wani abu, zai lahanta ni. Shi ne mutum da muka yi soyayya shekara da watanni, amma ban taɓa ganin wannan halin nasa ba. Amma saboda dokar cocinmu, ba a yarda muyi zaman mu kadai kafin aure, don haka ban samu damar gane shi sosai ba kafin auren.
Bayan wani lokaci, mahaifiyata ta kamu da ciwo. Na roƙi mijina in aika mata ₦15,000 don kula da kanta. Sai ya ce a’a, mahaifiyarsa na buƙatar injin daskare kifi (freezer) domin kasuwancinta. Ban ce komai ba. A sirrance, na aika wa mahaifiyata kuɗi daga ƙaramin ajiyar da nake yi a sabon asusun.
Mako guda kacal sai mahaifiyarsa ta yi haɗari da Keke Napep. Sai ya zo yana cewa in ɗauki bashi daga ofishina don ya haɗa da na shi a biya kudin jinya. Na tuna masa da lokacin da ya hana ni taimaka wa mahaifiyata. Na ce masa a’a, ba zan ɗauki bashi ba.
Watanni biyu bayan haka, sai ya mayar min da katin ATM — saboda ya gane albashin baya zuwa can ba. Na ce masa ya ajiye katin kawai, ba na buƙatarsa. Cikin fushi ya ɗauki bel yana kokarin bugeni. Amma wannan karon, na ce ya isa. Na ɗauki bututun labule, na buge shi a wuya.
Sai ya rika ihu yana cewa wai na yi ƙoƙarin kashe shi. Iyalan sa s**a ce in je in ba shi hakuri. Na ce a gawata ma ba zan roƙe shi ba.
Washegari, na tattara kayana, na bar gidan. Wata mata da na taɓa yi mata aikin nanny tun bayan sakandare ta taimake ni. Na gaya mata halin da nake ciki. Sai ta bani ₦450,000 don in k**a gida. Na koma sabuwar rayuwa – na samu salama da natsuwa.
Daga baya malamaina s**a ce in koma, a gyara zaman aure. Na ce a'a, ni dai na fi so in zauna lafiya fiye da mutuwa a cikin aure. Duk da haka na je na nemi gafara, amma na gaya musu gaskiya: “Rayuwata ta fi komai muhimmanci.”
Yanzu kuma mahaifiyata – wacce ke da ciwon suga da hawan jini, har yanzu tana cikin jimamin rasuwar mahaifina – tana ce min idan ban koma ba, zan karya mata zuciya, har ta mutu.
Wannan ne kadai ke damuna yanzu.
Amma gaskiya, ba zan iya komawa rayuwar azaba ba. Rayuwa guda ce. Ban shirya barin kaina cikin hannun wanda ke bugeni, ke ɗaukar ni k**ar baiwar sa, kuma ke barazana ga lafiyata ba.
---
Ina roƙon shawarar ku.
Me ya k**ata nayi?
Shin jin daɗin zuciyata ba ya da daraja idan mahaifiyata na cikin damuwa?
Ina jin laifi, amma ban ji kuskure ba.
Daga Shafin Naomi David