
09/03/2025
Dan Majilisar Wakilai Hon. Shehu Dalhatu Tafoki Ya Rabawa Al'ummar Shi Na Yankin Kankara, Faskari Da Sabua N150m.
Dan majalisar Tarayya na mazabar Ƙanƙara/Faskari/Sabuwa Hon Engr Shehu Dalhatu Tafoki ya raba buhunan shinkafa ƙanana 10kg 2500,25kgs 500 da kuma manya Masu nauyin 50kgs 100.
Dan Majilisar Bai Tsaya nanba yakara da tsabar kuɗi N52m a matsayin tallafin azumi ga al'ummar mazaɓarsa
Taron rabon kayayyakin ya gudana ajiya Asabar 8 ga watan March 2025, daidai da 8 ga watan Ramadan 1446, a Farfajiyar Kasuwar Zamani ta garin Kankara.
Dr.Bishir Usman Ruwangodiya ya bayyana yadda tsarin rabon kayan arziki yake, inda yace kayan da aka sawo sun kai N98m sai kuma tsabar kudi N52m, da in an haɗa gaba ɗaya ƙimar kayan da kudin sun kai N150m
Dr. Ruwangodiya ya cigaba da cewa wadanda zasu amfana da tallafin akwai, Party excos na matakin dukkanin mazaɓun Kankara/Faskari/Sabuwa sun sami jimillar N4m, sai chairman party na mazabu su 31 kowa 20k, excos na LG su 72 kowa 20k each, shuwagabannin APC su uku na ƙananan hukumomin kowa zai sami 50k
Akwai kuma manyan exco na jiha suna da 500k, shuwagabannin jam'iyyar APC a matakin jiha N1m, hakimai kowa 50k, limamai 50k magaddai 20k masu da'awa 3m jami'an tsaro 3m, yan kwamiti 4m, yan Midiya 1.5m
Akwai kuma mutum 1500 da aka zabo daga Kankara/Faskari/Sabuwa, kowa 10k, ƴan amanar ɗan majalisar wato support interest group N5m, masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC N4m, executive stake holders N2m, wadanda iftilain yan bindiga ya shafa 2m, uwar gidan ɗan majalisar ya ware mata N3m don ta rarraba ma mata ƴan uwanta, masu dakko kaya don rarrabuwa N3m, yan jarida N1m, da dai sauransu
Jaridar Rana24 ta kasance yayin gudanar da taron ta kuma ruwaito buhunan shinkafa da za a raba wa shuwagabannin
Waɗanda s**a halarci taron akwai mataimakin gwamnan jihar Katsina Mai girma Faruk Lawal Jobe, sakataren jam'iyyar APC na jiha, zababbun shuwagabanin Kananan hukumomin Sabuwa Engr Sagir Tanimu, zababben shugaban karamar hukumar Kankara Hon. Kasimu Dantsoho, zababben mataimakin shugaban karamar hukumar Faskari Hon Isyaku Wada da sauran mutane da dama.
Dasauran manyan baki da dama