11/07/2025
Labari akan hukumar ƴan sanda
Lauya ya maka IGP da wasu mutane a kotu bisa ƙin biyaiya ga umarnin kotun a Abuja
Wani lauya a Abuja, Yahuza Maharaz, ya shigar da kara akan raina kotu kan Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP, Kayode Egbetokun, tare da Isah Yusuf Musa da wasu mutum biyu, bisa zargin kin bin umarnin kotu.
A ranar 25 ga Yuni, Mai shari’a M.A Madugu na Babbar Kotun Taraiya da ke zaune a Bwari ya bayar da umarnin wucin-gadi, inda ya bukaci ƴansanda da sauran wadanda ake kara su ci gaba da barin komai a yadda yake (status quo), kafin fara sauraron karar da Maharaz ya shigar, a madadin Pamodi Pharmacy da ke Abuja.
A cewar takardun kotu da DAILY NIGERIAN ta samu, karar mai lamba: HC/BW/CV/199/2025 ta samo asali ne daga saɓani kan yarjejeniyar haya tsakanin Pamodi Pharmacy da ke Hillcrest Shopping Complex, Lokogoma, Abuja da kuma Isah Yusuf Musa.
Karar ta hada da shi Isah Yusuf Musa, Hill Crest Estate Management Development, Rundunar Ƴansanda ta ƙasa da kuma IGP a matsayin wadanda ake kara na farko zuwa na hudu.
Yayin da ya ke yanke hukunci kan bukatar da ke dauke a takardar umarni lamba: FCT/HC/M/8303/2025, Mai shari’a Madugu ya bada umarnin cewa a tsaya a yadda ake dangane da ofishin haya mai fadin murabba’in mita 160 da ke cikin Hill Crest Shopping Complex/Mall a fili No. 102, Cadastral Zone C09, Ahmadu Bello Way, Lokogoma, Abuja FCT.”
Sai dai kuma duk da wannan umarnin kotu na ci gaba da barin komai yadda yake, wanda ya shigar da kara ya zargi Musa da bayar da umarni a yanke wutar lantarki da kuma rufe ruwan da katin sayar da maganin ke amfani shi.
Hakanan, ya zargi Mista Musa da cire takardar umarnin kotu da aka manna a jikin bangon ginin, duk da umarnin da kotu ta bayar.
Lauyan ya kuma ce rundunar ƴansanda ta gayyaci Manajan Daraktan kamfanin domin yi masa tambayoyi, abin da ya ce ya saɓa wa umarnin kotu.
A cewar saƙon kar-ta!kwana da aka turo masa, an bukace shi da ya bayyana a gaban wani kwamiti na AIG Zone 7 a uau Juma’a.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yansanda, Muyiwa Adejobi, bai amsa tambayoyin da wakilin Daily Nigerian ya aiko masa ba dangane da lamarin.