04/07/2025
MUTANEN AREWA MASU ABIN MAMAKI
A daidai lokacin da rayukan 'yan Arewa suke salwanta a wasu jihohin Arewa irinsu Sokoto, Katsina, Zamfara da Borno wanda ya kamata muyi ta yayatawa domin a dauki mataki..
Amma sam wannan bai damemu ba, abinda muka mayar da hankali a daidai wannan lokaci da jinanen 'yar Arewa suke kwarara shine musu da jayayya akan cewa tsakanin motar Mawaki Rarara da ta Naziru Sarkin waka wacce ta fi tsada?
Ance wai Naziru ya sayi mota ta sama da kudi Naira Miliyan dari biyar, akace wai ta fi motar Rarara tsada, akan wannan ake ta musu da jayayya har ya zama abin trending a Facebook
Ni banga wani abin burgewa anan ba, idan motar Naziru ta fi na Rarara tsada to sai me?, abin da ya kamata ayi musu ma a kai shine tsakanin Mawaki Rarara da Naziru Sarkin Waka wa yafi amfani da damarsa wajen taimakon talakawa?
Inda zamu sa su a mizani na adalci Rarara ya fi naziru amfanar da al'ummah, a yanzu bani da wata alaka da Rarara, kuma bana ra'ayin siyasarsa, na taba alaka dashi farkon lokacin da ya fara yiwa Buhari waka a 2015, har ma ya nemi nambar wayata yake kirana mu gaisa a wancan lokaci
Lokacin da ya kirkiri wani website da yake tura wakokinsa ni ya fara yiwa magana domin na tallata masa a Facebook, kuma haka akayi na tallata a wancan lokaci, duk da ni bana ra'ayin wakoki da kide-kide irin na zamanin mu, amma saboda soyayyar Buhari na tallata masa
A yanzu ina ganin yadda Rarara yake fitar da kudade ya sayi abinci masu yawa ya raba wa bayin Allah kyauta, abinda ban taba gani Naziru Sarkin waka yayi ba kenan, gaskiya ko kusa ba za'a kwatanta kirkin Rarara da na Naziru ba, Rarara ya fishi kyauta da tallafawa mabukata nesa ba kusa
A yanzu ma nayi wannan tsokacin ne saboda ina free babu wani update mai ma'ana da zanyi, mu dawo kan matsalolin da s**a addabemu a Arewa don Allah
Ubangiji Allah Ka yaye mana matsalolin da suke addabarmu a Arewa
Datti Assalafiy