Funtua Post News

Funtua Post News Funtua Post,Dandalin kawo ingantattun labarai daga Funtua da sauran sassan Najeriya. Muna tabbatar da gaskiya tare da sahihanci a kowanne labari.

WhatsApp=08166055055

Wasu daga cikin hotunan taron Katsina MSME Awards, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima ya halarta a Ji...
21/10/2025

Wasu daga cikin hotunan taron Katsina MSME Awards, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima ya halarta a Jihar Katsina yau Talata.

Yanzu -Yanzu:-Mataimakin Shugaban Ƙasa Sen. Kashim Shettima ya baiwa ₦250,000 ga kowane ɗan kasuwa da ya baje kolin kasu...
21/10/2025

Yanzu -Yanzu:-Mataimakin Shugaban Ƙasa Sen. Kashim Shettima ya baiwa ₦250,000 ga kowane ɗan kasuwa da ya baje kolin kasuwancinsa a wajen taron National MSME Clinic da aka gudanar a jihar Katsina.

Yanzu-Yanzu: Gwamna Dikko Radda Ya Shirya Kaddamar da Sababbin Hanyoyi a Birnin KatsinaAna ci gaba da shirye-shiryen kad...
21/10/2025

Yanzu-Yanzu: Gwamna Dikko Radda Ya Shirya Kaddamar da Sababbin Hanyoyi a Birnin Katsina

Ana ci gaba da shirye-shiryen kaddamar da sababbin hanyoyi da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya gina a cikin birnin jihar Katsina.

Wannan babban bikin zai samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, wanda shi ne zai kaddamar da sabbin hanyoyin a yau.

A cewar majiyarmu, wannan aikin hanyoyi yana cikin shirin gwamnatin jihar na inganta sufuri, bunƙasa kasuwanci, da sauƙaƙa zirga-zirga a cikin babban birnin Katsina.

Gwamnatin Radda ta bayyana cewa za ta ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa, musamman waɗanda ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.

Sunan Dakta Mustapha Muhammad Inuwa,  tsohon laccar a jami a. tsohon shugaban hukumar sufiri ta jahar katsina,( ktsa) ts...
20/10/2025

Sunan Dakta Mustapha Muhammad Inuwa, tsohon laccar a jami a. tsohon shugaban hukumar sufiri ta jahar katsina,( ktsa) tsohon kantoman karamar hukumar Dan Musa,tsohon kwamishinan ilmi na jahar katsina. Tsohon sakataren gwamnatin jahar katsina har karo uku.yanzu kuma madugun adawa na jahar katsina. Me zaku ce akanshi?

Hotunan Yadda Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima Ya Kai Ziyarar Aiki Ta Kwanaki Biyu A Katsina, Yau Litinin
20/10/2025

Hotunan Yadda Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima Ya Kai Ziyarar Aiki Ta Kwanaki Biyu A Katsina, Yau Litinin

Labari Cikin Hotuna Yau ma tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sake haɗuwa da wani ɗaya daga cikin...
19/10/2025

Labari Cikin Hotuna

Yau ma tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sake haɗuwa da wani ɗaya daga cikin matasan jihar Kano da ya ɗauki nauyin karatunsu a lokacin da ya ke gwamnan ya je ya koyi tuƙin jirgin sama.

Matashin mai suna Ibrahim, ma'aikaci ne da sabon kamfanin sufurin jiragen saman nan na Umza Air, inda Kwankwaso ya shiga jirginsu zuwa Kano daga Abuja a yau Lahadi.

Sabuwar jami’ar kimiyya da lafiya ta Funtua ta fitar da sanarwar tantancewar Post-UTME ta shekarar 2025/2026Jami’ar Fede...
19/10/2025

Sabuwar jami’ar kimiyya da lafiya ta Funtua ta fitar da sanarwar tantancewar Post-UTME ta shekarar 2025/2026

Jami’ar Federal University of Medical and Health Sciences Funtua, Jihar Katsina, ta sanar da fara tantancewar daliban da s**a nemi shiga makarantar ta hanyar jarabawar UTME domin karatun shekarar 2025/2026.

Sanarwar da Ofishin Rajista na jami’ar ya fitar a ranar 19 ga watan Oktoba, 2025, ta bayyana cewa tantancewar za ta kasance ta yanar gizo (online) kacokam, kuma za ta fara ne daga Talata 21 ga Oktoba 2025 zuwa Jumma’a 25 ga Oktoba 2025.

Dukkan daliban da s**a zabi jami’ar a matsayin zabinsu na farko a lokacin cike takardar JAMB, ana shawartar su da su shiga shafin jami’ar https://portal.fumhsf.edu.ng domin yin rijista ta yanar gizo.

Matakan tantancewa sun haɗa da:

Bude sabon account ta amfani da adireshin imel mai aiki.

Tabbatar da lambar rijistar JAMB.

Biyan kuɗin tantancewa na Naira dubu biyu (₦2,000) ta hanyar Remita.

Sannan a ɗora takardun shaida (credentials) da s**a dace kafin bugawa.

Hukumar makarantar ta jaddada cewa tantancewar ba ta bukatar halartar jami’a kai tsaye, domin ana gudanar da ita ta online kacokam.

Ranar ƙarshe ta yin rijista ita ce Jumma’a, 25 ga watan Oktoba, 2025.

Haka kuma, daliban da s**a samu maki 180 zuwa 199 za a iya ba su damar canja zuwa wasu shirye-shiryen karatu da ke da sarari, amma dole ne su shiga shafin JAMB su amince da canjin kafin kammala shirin karɓar dalibai.

Domin karin bayani, ana iya tura sako zuwa: [email protected]

FEDERAL UNIVERSITY OF MEDICAL AND HEALTH SCIENCES, FUNTUA ANNOUNCES POST-UTME SCREENING EXERCISE FOR 2025/2026 SESSIONTh...
19/10/2025

FEDERAL UNIVERSITY OF MEDICAL AND HEALTH SCIENCES, FUNTUA ANNOUNCES POST-UTME SCREENING EXERCISE FOR 2025/2026 SESSION

The management of the Federal University of Medical and Health Sciences, Funtua (FUMHSF), Katsina State, has announced the commencement of its online Post-UTME screening exercise for the 2025/2026 academic session.

According to a statement signed by the Registrar, Dr. Muhammad Ali, the exercise is scheduled to begin on Tuesday, October 21, 2025, and will close on Friday, October 25, 2025.

All candidates who applied for admission into the institution through the Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) and selected the University as their first choice are advised to visit the University’s admission portal via https://portal.fumhsf.edu.ng to complete their online screening.

Applicants are to:

Create an account using a valid email address.

Verify their JAMB registration number.

Pay a non-refundable screening fee of ₦2,000 only via Remita.

Upload their relevant credentials and print the acknowledgement slip.

The management emphasized that the screening exercise is strictly online, and no physical appearance at the University is required.

The deadline for submission of online applications is Friday, October 25, 2025.

Candidates who scored 180 and above but could not meet the cut-off mark of 200 in their preferred programmes may be considered for other available courses. Such candidates are advised to log into the JAMB portal to accept the change and finalize their admission process.

For further inquiries, candidates can contact the admissions office via [email protected].

Shugaban karamar hukumar Faskari, Hon. Surajo Aliyu Daudawa, ya shiga daji da kansa zuwa wajen Fulanin da aka yi sasanci...
19/10/2025

Shugaban karamar hukumar Faskari, Hon. Surajo Aliyu Daudawa, ya shiga daji da kansa zuwa wajen Fulanin da aka yi sasanci da su, inda ya ceto mutum 26 da 'yan bindiga s**a yi garkuwa da su a yankin Tafoki.

Isiya Kwashen Garwa ne ya jagoranci tattaunawar da ta kai ga sakin mutanen a yau.

Shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano tare da shugabannin majalisun ƙananan hukumomin sun kai wa jagoran jam’iyy...
18/10/2025

Shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano tare da shugabannin majalisun ƙananan hukumomin sun kai wa jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ziyarar ban girma a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dutsinma a Jihar Katsina ta k**a wata matar aure bisa zargin yawon dare a unguwar Abuj...
18/10/2025

Hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dutsinma a Jihar Katsina ta k**a wata matar aure bisa zargin yawon dare a unguwar Abuja Road da ke garin Dutsinma.

A cewar jami’in Hisbah mai kula da fasahar sadarwa, BYareema, jami’an hukumar ƙarƙashin jagorancin A. Lawal Namanu ne s**a gudanar da samamen da misalin ƙarfe 12:30 zuwa 1:00 na dare, bayan samun bayanan sirri daga mazauna yankin, inda s**a k**a matar yayin da take yawo a tsakiyar dare.

A wani samame daban, hukumar ta kuma k**a wani mutum tare da wata mace da ake zargi da aikata baɗala a bayan tsohon asibitin Dutsinma, bayan samun bayanan sirri daga mazauna yankin.

Hukumar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kafin a mika waɗanda ake zargi ga hukumomin da s**a dace domin ɗaukar matakin doka.

Hotunan Yadda Al'ummomin Kananan Hukumomin Dake Yankin Arewacin Jihar Neja S**a Gudanar Da Taron Addu'o'i Na Musamman Do...
18/10/2025

Hotunan Yadda Al'ummomin Kananan Hukumomin Dake Yankin Arewacin Jihar Neja S**a Gudanar Da Taron Addu'o'i Na Musamman Domin Neman Allah Ya Yaye Musu Matsalar Ƴanbindiga Dake Addabarsu

Aminiya

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Funtua Post News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Funtua Post News:

Share