
03/07/2025
Kungiyar MTK Ta Raba Tallafin Abinci Ga Marasa Lafiya a Asibitin Dan Dutse Funtua.
A ranar Asabar 28/6/2025.
kungiyar jin kai mai zaman kanta Mutaimaki Kanmu Da Kanmu Support Organization (M T K) ta gudanar da rabon abinci ga marasa lafiya a Asibitin Dan Dutse, dake cikin karamar hukumar Funtua Jihar Katsina.
A cewar shugaban kungiyar, Malam Mustapha Abdul wanda kuma shine shugaban gidauniyar Arbyan Charitable Foundation wannan tallafi na daga cikin shirin kungiyar na rage radadin rayuwa ga marasa galihu, musamman masu fama da cututtuka a cibiyoyin lafiya.
Mun zo nan domin mu nuna cewa muna tare da jama'a musamman wadanda ke cikin mawuyacin hali a Asibitoci. Wannan tallafi wani bangare ne na aikace-aikacen jin kai da muke gudanarwa a fadin jihar Katsina," in ji Mustapha Abdul yayin rabon abincin.
Tallafin ya ƙunshi kayayyakin abinci da aka raba kai tsaye ga marasa lafiya da ke kwance a asibitin lamarin da ya haifar da farin ciki da godiya daga bakin iyalai da jami'an lafiya.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da kungiyar M T K ke irin wannan aiki ba. Kungiyar na da tarihin gudanar da ayyukan jin kai a fannoni da dama, ciki har da ilimi, lafiya, da rage talauci, musamman a yankin Funtua da sauran sassan jihar Katsina.