
28/07/2025
WATA SABUWA: "Peter Obi Zai Koma PDP Don Takarar Shugabancin Kasa a 2027 –Inji-Ali Modu Sheriff
Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya tabbatar da cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, na shirin komawa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin yin takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da Channels Television a daren Litinin.
“A game da wannan siyasa, su (ADC) babu su a cikin lissafi. Bayanai da nake da su sun nuna cewa ko da yaushe daga yanzu, Peter Obi zai koma PDP kuma zai tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar,” in ji shi.
A baya-bayan nan, dattijo kuma daya daga cikin wadanda s**a kafa PDP, Farfesa Jerry Gana, ya bayyana cewa jam’iyyar ta fara tattaunawa da Peter Obi da wasu fitattun ‘yan siyasa daga Kudu gab da zaben 2027.
Farfesa Gana, wanda ya taba rike matsayin Ministan Yada Labarai, ya ce PDP na kokarin sake gyara kanta kuma tana nazarin abubuwan da s**a faru a zabukan fidda gwani na baya domin daukar sabbin matakai.
Jita-jitar dawowar Obi PDP ta kara karfi bayan rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar na iya bai wa yankin Kudu tikitin shugaban kasa a 2027.
Hakan ya kara kara da wutar rade-radin ne bayan Mataimakin Sakataren Yada Labarai na PDP na kasa, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana Peter Obi a matsayin “muhimmin jigo” ga jam’iyyar.