24/10/2025
Bugun Littafin Al-Qur’ani Mai Tsarki Na Farko A Duniya
Bugun Littafin Al-Qur’ani Mai Tsarki Na Farko A Duniya, wanda aka buga da injin bugu ba rubutun hannu ba.
(Paganino & Alessandro Paganini) wani Kamfanin Ɗab’i da ke birnin Venice a Ƙasar Italiya sun fitar da Al-Qur’ani na farko da aka buga a inji da Larabci, wadda kwafi guda ne kawai ya tsira.
Tsakanin ranar 9 ga watan Agusta, Alif da Ɗari Biyar da Talatin da Bakwai (1537) da kuma 9 ga watan Agusta, Alif da Ɗari Biyar Da Talatin Da Takwas (1538), ma su buga takardu na (Venetian Paganino da Alessandro Paganini) su ka fitar da bugun Al-Qur’ani na farko da Larabci.
Wataƙila an yi niyyar fitar da shi zuwa Daular Usmaniyya ta Turkiyya tsawon ƙarnuka, ana tsammanin wannan bugun ya ɓace, sai dai akwai jita-jitar cewa Paparoma ne ya ƙone cikakken bugun.
A cikin shekarar Alif da Ɗari Tara da Tamanin da Bakwai (1987) Farfesa Angela Nuovo ta sami kwafi guda ɗaya a cikin ɗakin karatu na Franciscan Friars na Isola di San Michele, a birnin Venice na Kasar Italiya. Kwafin ya ƙunshi bayanin mallakar Teseo Ambrogio degli Albonesi, wanda ya mutu a shekarar Alif da Ɗari Biyar Da Arba’in (1540), da tambarin Arcangelo Mancasula, Vicar of the Holy Office (Holy Inquisition) na Cremona, wadda aka yi amfani da shi bayan ƴan shekaru.
Bayan haka, Albonesi, masanin ilimin gabas Ta Tsakiya daga Pavia, shi ne kawai mutumin da aka sani ya sarrafa bugun Al-Qur’ani na farko da aka buga a cikin Larabci, kuma ya ambace shi a cikin gabatarwarsa a yaren Armenicam a shekarar ta Alif da Ɗari Biyar da Talatin da Tara (1539).