
17/09/2025
DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu ya janye dokar-ta-ɓaci a jihar Rivers tare da umartar Fubara ya dawo aiki
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen dokar-ta-baci da ya kakaba a Jihar Rivers daga daren yau Laraba, 17 ga Satumba, 2025.
Tinubu, a wata sanarwar da kakakin da, Bayo Onanuga ya fitar, ya umarci Gwamna Fubara, mataimakiyar sa Ngozi Nma Odu da kakakin majalisar Martins Amaewhule tare da sauran ‘yan majalisa da su koma bakin aiki daga Laraba, 18 ga Satumba, 2025.
Tinubu ya bayyana cewa ya ayyana dokar ta-baci a ranar 18 ga Maris, 2025 ne bayan rikicin siyasa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar ya haifar da durƙushewar ayyukan gwamnati.
Ya ce dokar-ta-bacin ta zama dole ne domin hana jihar fadawa cikin tarzoma, inda aka dakatar da gwamna, mataimakiyar gwamna da ‘yan majalisa na tsawon watanni shida.
Ya yi kira ga shugabannin siyasa a duk fadin kasar da su tabbatar da zaman lafiya da kyakkyawar alaka tsakanin bangarorin gwamnati domin bai wa jama’a damar amfana da dimokuradiyya.