GUDI MEDIA TV

GUDI MEDIA TV GUDI MEDIA TV, bata ƙarƙashi ko wakiltar gomnati, masarauta ko wata jam'iyyar siyasa, shafi ne na gidan telebijin mai zaman kanta.

Aikin ta shi ne, yaɗa labarai, rahotanni, wayarwa da kuma faɗakarwa bisa turbar gaskiya da amana ba tare da son zuciya ba.

Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar ADC a Jihar Gombe, Abdulrahman Buba Zaune, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar nan ...
07/08/2026

Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar ADC a Jihar Gombe, Abdulrahman Buba Zaune, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar nan take.

Zaune ya bayyana hakan ne cikin wasiƙar murabus da ya rubuta mai ɗauke da kwanan wata 5 ga Agustan 2026, wadda ya aike wa Shugaban jam'iyyar ADC na Mazabar Zaune, a Ƙaramar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe.

A cikin wasiƙar, wadda jaridar Punch ta gani a ranar Alhamis, tsohon Sakataren Yaɗa Labaran ya gode wa jam'iyyar bisa damar da ta ba shi na yin aiki da ita a matakai daban-daban, da s**a haɗa da matakin ƙaramar hukuma, na jiha da kuma na ƙasa.

Matatar Man Fetur ta Dangote ta bayyana cewa ta sake zarce Amurka a samar da man jiragen sama (Jet Fuel) karo na biyu a ...
07/08/2026

Matatar Man Fetur ta Dangote ta bayyana cewa ta sake zarce Amurka a samar da man jiragen sama (Jet Fuel) karo na biyu a jere.

A cikin wata sanarwa da matatar ta fitar ranar Alhamis, ta ce wannan nasara na nuna yadda tasirinta ke ci gaba da ƙaruwa a kasuwannin mak**ashi na duniya.

Sanarwar ta ce: “Matatar Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals ta ƙara ƙarfafa matsayinta a matsayin babbar mai samar da ingantaccen man jiragen sama a duniya, bayan da ta zama babbar mai samar wa Turai wannan man karo na biyu a jere, inda ta zarce Amurka. Wannan ya nuna irin tasirin da matatar ke da shi a kasuwannin mak**ashi na duniya.”

Matatar ta ce sabon bayanan shigo da mai na Turai da kamfanin binciken kasuwannin kayayyaki na duniya, Kpler, ya tattara sun nuna cewa sama da tan 400,000 na man jiragen sama da aka samar a matatar Dangote aka kai Turai a watan Yuli. Wannan ya kai kusan kashi 20 cikin 100 na dukkan man jiragen sama da Turai ta shigo da shi a wannan watan.

Haka kuma, matatar ta ce wannan ya biyo bayan rikodin tan 466,000 da aka fitar zuwa Turai a watan Yuni, lokacin da Najeriya ta fara maye gurbin Amurka a matsayin babbar mai samar da man jiragen sama da ake shigowa da shi zuwa Turai.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan ci gaba na nuna cewa matatar Dangote na da ƙarfin ci gaba da samar wa ɗaya daga cikin kasuwannin man fetur mafi tsauri a duniya man jiragen sama da ya cika ƙa’idojin inganci na ƙasa da ƙasa.

Ta kuma bayyana cewa Turai ta shigo da kusan tan miliyan 2.06 na man jiragen sama a watan Yuli, inda matatar Dangote ta kasance mafi girman mai samar da wannan mai, ta zarce masu samar da shi daga Amurka da ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Wallahi babu wanda ya isa ya sake ƙaƙa ba mana Tinubu a Najeriya. Mutum ko aman wuta yake, bai isa ba, domin babu biyayy...
07/08/2026

Wallahi babu wanda ya isa ya sake ƙaƙa ba mana Tinubu a Najeriya. Mutum ko aman wuta yake, bai isa ba, domin babu biyayya ga azzalumin shugaba," in ji jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq.

Ku bayyana mana ra'ayinku ?

Mahaddata 335 daga ƙasashe daban-daban ne suke fafatawa domin lashe kyautar Naira biliyan 3.7 a Gasar karatun Alkur’ani ...
07/08/2026

Mahaddata 335 daga ƙasashe daban-daban ne suke fafatawa domin lashe kyautar Naira biliyan 3.7 a Gasar karatun Alkur’ani ta duniya da ke gudana a ƙasar Saudiyya.

Mahaddata maza da mata daga ƙasashe 133 ne suke fafatawa a gasar Alƙur’ani Mai Girma ta Sarki Abdulaziz ta Duniya karo na 46 wadda aka buɗe a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya a ranar Alhamis.

Yawan mahaddata da ke fafatawa a gasar bana, shi ne mafi girman adadin mahalarta tun bayan ƙaddamar da gasar.

A karon farko a tarihin gasar, za a gudanar da gasar mata daban a Makkah Hilton Hotel & Convention, yayin da za a gudanar da zagayen ƙarshe na maza da kuma bikin rufe gasar a Masallacin Harami.

Gasar ta ƙunshi hadda da tafsirin Alkur’ani, kuma ana gudanar da ita ne a ƙarƙashin jagorancin Mai Kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki, Sarki Salman bin Abdulaziz.

Gasar ta ƙunshi rukuni biyar, kuma jimillar kuɗin kyaututtukanta ya kai Riyal miliyan 10.26 na Saudiyya, kwatankwacin kusan Naira biliyan 3.7, wanda shi ne mafi girman adadin kyauta tun bayan fara gudanar da gasar.

Gasar, wadda Ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci, Wa’azi da Shiryarwa ta Saudiyya ke shiryawa, za ta gudana har zuwa ranar 6 ga Rabi’ul Awwal, wadda ta yi daidai da 19 ga Agusta.

Manufar gasar ita ce ƙarfafa matasan Musulmi su haddace Alƙur’ani, su fahimci ma’anoninsa tare da yin nazari a kansa, da bunƙasa gasa ta gari a tsakaninsu, tare da nuna irin ƙoƙarin da Saudiyya ke yi wajen hidimtawa Alƙur’ani da girmama masu haddace shi.

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa an tura wasu k...
07/08/2026

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa an tura wasu kuɗaɗe cikin ɗaya daga cikin asusun ajiyarsa na sirri da ke wani babban bankin kasuwanci a Najeriya, lamarin da ya bayyana a matsayin abin da ke da matuƙar tayar da hankali.

Sai dai, Atiku ya ce ya riga ya sanar da hukumomin tsaro domin su binciki wannan lamari k**ar yadda shafin labari BBR Hausa ta ruwaito

Menene Ra’ayinku kan wannan batu ?

Jam'iyyar ADC Za Ta Kalubalanci Takardun Karatun Tinubu a Kotu Gabanin Zaɓen 2027Jigon jam’iyyar ADC, kuma Lauya a Najer...
07/08/2026

Jam'iyyar ADC Za Ta Kalubalanci Takardun Karatun Tinubu a Kotu Gabanin Zaɓen 2027

Jigon jam’iyyar ADC, kuma Lauya a Najeriya Solomon Dalung, ya bayyana cewa jam’iyyarsa za ta garzaya kotu domin kalubalantar takardun karatun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Dalung ya ce ADC za ta nemi kotu ta yi fassarar doka kan sahihancin takardun karatun da Shugaba Tinubu ya miƙa wa INEC, yana mai cewa hakan na daga cikin matakan da jam’iyyar ke shirin ɗauka kafin zaɓen mai zuwa.

A cewarsa, matakin neman fassarar kotu zai taimaka wajen fayyace batutuwan da s**a shafi cancantar takardun ilimi da aka gabatar wa hukumar zaɓe.

Rashida Adamu Abdullahi ta yi martani mai zafi ga mambobin Kwankwasiyya a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan...
07/08/2026

Rashida Adamu Abdullahi ta yi martani mai zafi ga mambobin Kwankwasiyya a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta. Ta ce za su fito domin tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai jaddada cewa za su yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin ya samu nasara a zaɓe.

ICPC ta bankado sabbin hukumomin bogi biyu yayin bincike kan PFIPCHukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (ICPC...
07/08/2026

ICPC ta bankado sabbin hukumomin bogi biyu yayin bincike kan PFIPC

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (ICPC) ta bayyana cewa ta gano wasu sabbin hukumomin bogi guda biyu a yayin da take gudanar da bincike kan hukumar PFIPC.

Shugaban ICPC, Dr. Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu rahoton binciken da hukumar ta gudanar.

A cewarsa, binciken ya nuna cewa Darakta Janar na hukumar PFIPC, Prince Adeyemi Adeniyi, ne ya ƙirƙiri sabbin hukumomin bogin guda biyu.

HOTUNA: Gwamna Mai Mala Buni Ya Rantsar da Sabbin Jami'ai a Gwamnatin Jihar YobeDr. Muhammad Goje ya zama Babban Sakatar...
06/08/2026

HOTUNA: Gwamna Mai Mala Buni Ya Rantsar da Sabbin Jami'ai a Gwamnatin Jihar Yobe

Dr. Muhammad Goje ya zama Babban Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe (SSG) na dindindin.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Girma Hon. Mai Mala Buni, ya rantsar da sabbin jami'an da aka naɗa domin riƙe muhimman muƙamai a gwamnatinsa, ciki har da Babban Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Mai Ba da Shawara na Musamman, Shugaban Hukuma da kuma Sakatarorin Dindindin guda huɗu.

An gudanar da bikin rantsarwar ne a yau Alhamis, 6 ga Agustan 2026, a Fadar Gwamnatin Jihar Yobe da ke Damaturu.

Da yake jawabi yayin bikin, Gwamna Mai Mala Buni ya buƙaci sabbin jami'an da su yi aiki da gaskiya, riƙon amana da sadaukarwa, tare da tabbatar da inganta ayyukan gwamnati domin amfanin al'ummar jihar.

Ya kuma jaddada cewa, yana sa ran sabbin waɗanda aka naɗa za su tabbatar da amincewar da aka yi musu ta hanyar gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa, gaskiya da nuna cikakkiyar biyayya ga al'ummar Jihar Yobe.

Bikin ya samu halartar manyan jami'an gwamnati, sarakunan gargajiya da sauran su.

GUDI MEDIA TV

KAJI BABBAN RABO: Gwarzuwa Hafsa Muhammad Sada Ta Tafi Saudiyya Domin Wakiltar Najeriya a Gasar Musabaƙar Al-Qur'ani ta ...
06/08/2026

KAJI BABBAN RABO: Gwarzuwa Hafsa Muhammad Sada Ta Tafi Saudiyya Domin Wakiltar Najeriya a Gasar Musabaƙar Al-Qur'ani ta Duniya

Gwarzuwa Hafsa Muhammad Sada ta k**a hanya zuwa Ƙasar Saudiyya domin wakiltar Najeriya a gasar musabaƙar Al-Qur'ani ta duniya ta ɓangaren mata.

Za a gudanar da gasar ne a Birnin Makka, cikin Masallacin Harami, kuma wannan shi ne karo na farko da za a shirya wannan babbar musabaƙa ta duniya ta musamman ga mata.

Ana sa ran Hafsa Muhammad Sada za ta wakilci Najeriya tare da nuna bajinta a wannan gasa mai muhimmanci, wadda ta haɗa manyan mahaddatan Al-Qur'ani mata daga ƙasashe daban-daban na duniya.

Wane fatan za ku mata?

GUDI MEDIA TV

Address

Gadaka

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GUDI MEDIA TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category