29/07/2026
DA ƊUMI-ƊUMI: An Kafa Ƙungiyar Ganye Old Market Progressive Minds Domin Haɗin Kai da Ci gaban Tsohuwar Kasuwar Ganye
Mazauna yankin Tsohuwar Kasuwa da ke ƙaramar hukumar Ganye a Jihar Adamawa sun kafa wata sabuwar ƙungiya mai suna Ganye Old Market Progressive Minds (GOMPM) da nufin ƙarfafa haɗin kai da kuma samar da ci gaba a yankin.
A cewar bayanin da ƙungiyar ta fitar, GOMPM ƙungiya ce mai zaman kanta da aka assasa domin bunƙasa harkokin ilimi, kasuwanci da zamantakewa tare da kare muradun mambobinta da kuma tallafa wa ci gaban Tsohuwar Kasuwar Ganye da al'ummomin da ke kewaye da ita.
An bayyana cewa ƙungiyar ta haɗa 'yan kasuwa, masu sana'o'i, ma'aikatan gwamnati, ƙwararru daga fannoni daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki, inda za ta yi aiki bisa ginshiƙan gaskiya, riƙon amana, haɗin kai, adalci da mutunta juna.
Haka kuma, ƙungiyar za ta kasance wata kafa ta tattaunawa da warware matsalolin al'umma, ƙarfafa zaman lafiya, bunƙasa kasuwanci da kuma haɗa kai da hukumomin gwamnati, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin ci gaba domin samar da ci gaba mai ɗorewa.
A cikin manufofinta, GOMPM ta ce za ta mayar da hankali kan wayar da kai, horas da mambobi, ƙarfafa su da aiwatar da shirye-shiryen ci gaban al'umma domin tabbatar da Tsohuwar Kasuwar Ganye ta kasance mai tsafta, tsaro, tsari da wadata.
Shugaban Kwamitin Riƙo na ƙungiyar, Malam Lawan Inuwa, ya yi kira ga al'ummar yankin da dukkan mambobin ƙungiyar da su haɗa kai wajen tallafawa wannan yunƙuri, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen dawo da martabar kasuwar da kuma samar da kyakkyawar makoma ga matasa masu tasowa.
An kuma buƙaci masu sha'awar samun ƙarin bayani su tuntubi lambar wayar: 08032075124.
Rahoto: Comrd Isa Oga Abdulmumini mukaddashin Kakakin Ƙungiyar Ganye Old Market Progressive Minds