20/08/2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa Gwamnatin Jihar Kano na shirin ƙirƙirar sabbin birane a jihar ta hanyar ware filaye 2,483 a Yargaya da Rijiyar Gwangwan a karamar hukumar Dawakin-Kudu da kuma filaye 1,671 a Unguwar Rimi da Lambu a karamar hukumar Tofa, a yunƙurin rage cunkoso a cikin birnin Kano. Duk da cewa wannan shiri yana da kyau, amma ina ganin akwai hanyar da ya kamata gwamnatin ta bi don samar da kyakkyawan sakamako wanda zai bambanta da na gwamnatocin da s**a gabata.
Sanata Rabiu Kwankwaso da Sanata Ibrahim Shekarau su ma sun aiwatar da irin waɗannan ayyukan gina birane a lokacin mulkinsu. Misali, Sanata Kwankwaso ya ƙirƙiri biranen Kwankwasiyya da Bandarawo a wajen birnin Kano da nufin rage cunkoso a cikin gari. Amma abin takaici, duk da biliyoyin nairorin da aka kashe, har yanzu waɗannan birane ba a fara amfani da su yadda ya kamata ba.
A nawa hangen Gwamna Abba Yusuf kamata yayi ya dauki tsarin dabarun da tsohon Gwamna Nasir el-Rufai na Jihar Kaduna ya aiwatar. Ya kafa hukumomi uku a jiharsa: Hukumar Babban Birnin Kaduna, Hukumar Birnin Zaria, da Hukumar Karamar Hukumar Kafanchan (Kaduna Capital Territory Authority, Zaria Metropolitan Authority, da Kafanchan Municipal Authority) Wannan tsarin ya bai wa mazauna waɗannan yankuna damar gina biranen su tare da taimakon gwamnati.
A Kano, irin wannan tsari ne zai iya zama mafi tasiri. Misali, za mu iya kafa Hukumar Birnin Gaya a Kano ta Kudu, Hukumar Birnin Dambatta a Kano ta Arewa, yayin da Kano ta Tsakiya za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin Hukumar Babban Birnin Kano (a turance, Gaya Metropolitan Authority in Kano South, a Dambatta Municipal Authority in Kano North, while Kano Central continues to operate under the Kano Capital Territory Authority). Irin wannan tsarin zai karfafawa mutanen waɗannan yankuna gwiwa don ganin sun gina yankunan su tare da taimakon gwamnatin jiha, a maimakon dogaro da wannan tsari na gina manyan gidaje kamar Kwankwasiyya da Bandarawo, waɗanda watakila ba za su cimma burin da ake so ba.
Idan zai yiwu, Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf, muna roƙon ka da ka sake duba wannan shirin, ka mayar da hankali kan inganta ci gaban akalla guda biyar daga cikin ƙananan hukumomin mu 44. Wannan tsarin zai iya haifar da tasiri, rage cinkoso a cikin birni da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a jiharmu.
Na gode, Mai girma Gwamna.
Bashir Ahmad, OON.