
26/09/2025
Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru ya ce Najeriya ta sake jaddada kudirinta na hana yaduwar mak**an nukiliya tare da kira ga ƙasashen duniya da su gaggauta fara tattaunawa kan yarjejeniyar Fissile Material Cut-off Treaty (FMCT).
Ministan ya yi wannan kira ne a taron ministocin ƙasashen da ke goyon bayan FMCT a New York, inda ya ce hana kera kayan nukiliya zai hana yaki mara iyaka, ya kuma ƙarfafa yarjejeniyar hana yaɗuwar mak**an nukiliya.
Ya bukaci kasashen duniya su dauki mataki, musamman da wannan shekarar ke cika shekaru 80 da harin Hiroshima da Nagasaki.
Najeriya ta kuma tuna rawar da Afirka ta taka wajen hana mak**an nukiliya ta hanyar yarjejeniyar Pelindaba, tare da neman irin wannan tsari a duniya baki ɗaya.
Badaru ya ce rage mak**an nukiliya zai ba da damar amfani da albarkatun kasa a bangaren lafiya, ilimi da cigaban tattalin arziki, tare da goyon bayan shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.