Yusuf muhammad Ibrahim

Yusuf muhammad Ibrahim Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Yusuf muhammad Ibrahim, Digital creator, Garun Malam.

More ink to your pen Barr.👌😊Abdul-Hadee Isah Ibraheem
14/02/2026

More ink to your pen Barr.👌😊
Abdul-Hadee Isah Ibraheem

SHARHI: Tattaunawar El-Rufai da Arise TV.
Abu ne mai matukar wahala gwamnati ta k**a El-Rufai a yanzu, ko kuma tasa a rike shi a hannun jami'an tsaro ko gidan Yari.

Daga Abdul-Hadee Isah Ibraheem

Wato manyan 'yan siyasa a fadin duniya wadanda suke da zurfi ilimi akan siyasa da yadda gwamnati take s**an tattara abubuwa masu yawa su ajiye a cikin zuciyar su, duk yadda abun yake da muhimmanci ba zasu fitar dashi ba matukan bai kai matsayin da zai zama makami (political weapon) ga abokan adawar su ba, me wannan maganar take nufi?

Abu na farko, ka tsaya ka duba da kyau tun yaushe El-Rufai ya bar Nigeriya? yafi wata uku baya Nigeria, ya tafi kasashe guda uku wadanda ya bayyana yaje. Banda wadanda bai bayyana ba. Ya tafi Asibiti a Australia, yaje Saudi Arebia yin Umrah, yaje Masar domin koyon Larabci, duk tafiye tafiyen nan ba haka kawai yayi su ba.

Kafin ya dawo Nigeria da Awanni 48 ya sanar cewa ana kokarin k**a shi, so yana sane da abubuwan da ake yi domin a k**a shi, ta ina yake samu bayanan? daga cikin wadanda suke shirya abun, k**ar yadda Gwamnan Bauchi yace yana samun wasu bayanai daga EFCC akan wadanda suke shirya masa Gadar zare.

So, da wahala wani abu ya buya ga El-Rufai daga kowace irin hukuma a kasar nan, a cikin kaso 100 zai iya sanin akalla 40 ne move din da gwamnati da 'yan siyasar cikin ta suke yi akan sa. El-Rufai ya karanta kuma ya gane gabar da ya k**ata ya dawo Nigeria, ko fita da yayi duk sai da ya gama kallon movements din masu adawa dashi.

Mu koma kan maganar mu ta farko:

Tunda El-Rufai bai kamu a Airport ba toh anyi missing, dama idan ya shigo zai yi hira da BBC, zai yi da Arise TV da sauran su, already ya riga yayi, wadannan maganganun masu nauyi da hatsari ya riga yayi su, ko sun rufe a gidan Yari ko an rike shi a hannun jami'an tsaro ya riga ya kai Target dinsa. Abinda ya rage shine idan an k**a shi already ya shimfida ya rubuta duk abubuwan da za'a yi a fagen adawa domin kayar da Tinubu a zaben.

Arise TV Tasha ce mai zaman kanta, suna da karfi a ciki da wajen Nigeria, private ce, ba ta gwamnati bace, kudi zaka je ka biya ka fadi duk abinda kake so, ka bayar da tambayoyin da kake so ayi maka, ka bayyana salon da kake so ayi maka tambayar sai ka amsa. So, duk abinda kaji Charles ya fada toh dama shiryayyen abu ne, abu na biyu:

Manyan 'yan siyasa s**an ajiye mak**an yaki domin sun san akwai fadan da zasu taro idan s**a harba wannan makamin toh dole a kyale su. Duk muhimmanci abun ba zasu fada ba idan ba su zasu amfana ba kai tsaye, misali:

1. El-Rufai yayi magana akan Dadiyata, mutane suna cewa yana sane tuntunin bai fada ba sai yanzu? eh ku talakawa haka zaku kalli abun, idan ya fada a wancan lokacin wane amfani zai yi masa? yace akwai Police officer din da dashi aka je daukan Dadiyata. Ya kuma jingina abun ga tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
~ Idan bangaren Ganduje s**a ce zasu tanka ma wannan maganar a yanzu daf da zabe toh abubuwa biyu zasu faru; ko dai asiri ya tonu, idan akwai hannun sa a ciki, ko kuma ya bata lokacin sa wajen fada da El-Rufai akan case din Dadiyata, wanda a yanzu babu abinda ke gaban Ganduje k**ar aikin kawo jihar Kano wa APC a zaben 2027.

2. Na biyu, El-Rufai yayi maganar jiyo kiran wayar mai baiwa shugaban kasa shawara akan lamarin tsaro, Malam Nuhu Ribado, wannan maganar ba karama bace, kuma bai yi ta ba sai da consultations, da kallon implications dinta, da way out idan ta juya upside down.
~ Duk maganganun da Hajiya Naja'atu Muhammad tayi akan Nuhu Ribado wancan shekarar kunji ya tanka mata? har aka yi zancen za'a kaita Kotu? yau ina maganar? Nuhu Ribado yaji tsoron ta ne? ko kuma idan ya tanka mata zai bata lissafin siyasar 2027 wa APC a Arewa?

3. Na uku, El-Rufai yayi maganar zai je EFCC ranar Litinin da karfe 10 na safe, yace ranar Birthday dinsa ma kenan, zai je ya dawo yayi hidimar birthday dinsa. Yana da tabbacin zai dawo din? daga wajen ba za'a wuce Kotu ba? daga Kotu a wuce gidan Yari ko hannun jami'an tsaro?

Idan aka rike El-Rufai a yanzu toh akwai abu biyu a nan;

A. Case din zai koma international, danne hakkin 'yan adawa, kokarin ganin bayan su, political observers daga wajen duniya zasu yi chaa ma gwamnatin Nigeria, domin na tabbata duk wadannan abubuwan El-Rufai ya shirya su kafin ya dawo.

B. Idan aka rike shi, zai tayar da Karnukan da El-Rufai ya ajiye cewa idan an k**a ni ga abinda za'a yi a lokaci kaza da kaza. Sannan k**a shi zai zama abun kunya ga gwamnatin koda taci zabe cewa ta gagara cin zabe har sai data daure El-Rufai, dan haka ba wani kokari tayi ba.

Zasu gwammace su kyale shi a fili, suci zaben akan Idon sa yana gani, gwamnati bata yin abubuwa haka kawai duk sai sun buga wannan lissafin. Haka kuma barin sa a yana yawo yana fadin duk abinda yaso babban hatsari ne wa gwamnatin da jam'iyyar ta.

3. El-Rufai yayi maganar Kwankwaso da batun Shari'ar Musulunci da cewa da hadin bakin APC aka yima Kwankwaso irin wannan abun daga Nigeria amma aka je America aka harbo abun daga can. Dama El-Rufai yana tare fadawa Kwankwaso ne? a'a baya yi, suna tafiya tare ne? No, why now? saboda dukkan su sun gamsu suyi adawa da gwamnatin.

Kusan a yanzu duk wani babban 'dan siyasar da yake da mabiya masu yawa a Arewa baya tare da APC, dole APC taji zafin wannan abun, kuma dole tayi duk abinda zata iya wajen ganin ta tsare martabar ta.

Atiku Abubakar, baya tare dasu.
Kwankwaso, baya tare dasu.
El-Rufai baya ciki.
Aminu Tambuwal, baya yi.
Sen. Bala Abdul-Kadeer, shima haka.
Abubakar Malami, ya janye daga cikin su.
Peter Obi, baya yi.
Ra'uf Aregbesola.
Rotimi Ameichi.

So, ko da gwamnati zata tura El-Rufai Kotu zai yi wahala s**e a kulle shi ko a rike shi irin yadda s**ai wa Abubakar Malami, SAN.
Domin rike mutum irin El-Rufai zai tayar da wata kurar da ita kanta gwamnatin zata ga cewa adawar da za'a yi mata zai yi muni, kuma zasu kara karfafa 'yan adawa.

Daga cikin target dinsa shine a k**a shi din, domin k**a El-Rufai zai rura wutar adawa da APC musamman a cikin manyan 'yan siyasar kasar wadanda jira suke yi ayi primaries a APC su fasa kwai kowa ya rasa.

Daga Abdul-Hadee Isah Ibraheem

17/07/2025
15/07/2025

Ka Tsoraci Mu'amala Da Mutumin Da Baya Iya Yafewa Matacce.
Copied

Address

Garun Malam

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yusuf muhammad Ibrahim posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share