06/11/2025
SAƘON JAJE ZUWA SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR GAYA.
A Madadin Mai girma Ɗan majalisar Tarayyar Mai wakiltar ƙananan hukumomin Gaya Ajingi Albasu Hon Dr Ghali Mustapha Panda, yana miƙa saƙon jajantawa ga mai girma shugaban ƙaramar hukumar Gaya Hon Dr Mahmoud Gaya Tajo Sani bisa iftila’in daya faru na sata Ranar Talata 04/11/2025 a sakateriyar mulki ta ƙaramar hukumar Gaya jihar Kano.
Ba shakka wannan abun Takaici ne da kuma Allah wadai ga mutanen da s**a aikata wannan mummunar ta'asa.
Muna roƙon Allah maɗaukakin Sarki ya ƙara tsare mana yankin Mu na Gaya, Ajingi, Albasu da jihar Mu da ƙasar mu baki ɗaya.
Muna kuma Addu'a ga waɗanda s**a jikkata Allah ya inganta musu lafiya, ya kuma kare afkuwar Hakan Anan Gaba.
✍️Bashir Ɗanzarewa Gaya
Matemaki na musamman ga Hon Dr Ghali Mustapha Tijjani Panda.
06 November, 2025