18/11/2025
NYCN Reshen Gaya Ta Shirya Walimar Cika Shekara ĆŠaya Ta Shugaban Karamar Hukumar Gaya
A ranar Talata, 18 ga Nuwamba, 2025, Majalisar Matasan Najeriya (NYCN) reshen karamar hukumar Gaya ta gudanar da walima tare da bikin karramawa domin taya shugaban karamar hukumar, Hon. Mahmoud Gaya Tajo Sani, murnar cika shekara guda a kujerar mulki.
An shirya taron ne domin bayyana godiya da yaba wa irin ayyukan ci gaban da shugaban ya aiwatar a cikin shekara guda, wanda hakan ya inganta harkokin zamantakewa, tattalin arziki, da walwalar al’umma a yankin Gaya.
A yayin taron, NYCN Gaya ta karrama shugaba Hon. Mahmoud Tajo Sani da lambar yabo (Award) bisa irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban karamar hukumar, musamman a fannin ayyukan yau da kullum da tallafa wa matasa.
Haka zalika, kungiya ta karrama Hon. Yassir Abdullahi Jobe, mataimakin shugaban karamar hukumar Gaya, saboda irin gudunmawar da yake bayarwa a harkokin matasa da shawarwari kan sana’o’in dogaro da kai da kuma Rt. Hon. Nazifi Sabiu Kalahaddi, shugaban majalisar kansiloli ta Gaya, bisa cikakkiyar gudunmawa, haɗin kai da kasancewarsa ginshiƙi ga kungiyar NYCN. da Hon. Suraj Akilu, shugaban hukumar ilimi bai daya na Gaya( Education Secretary Gaya), bisa jajircewarsa wajen tallafawa al’umma da bunkasa sha’anin ilimi.
Shugabannin NYCN Gaya sun kuma kaddamar da wani littafi mai dauke da jerin muhimman ayyuka da nasarorin da Hon. Mahmoud Tajo Sani ya cimma a cikin shekara guda na shugabancinsa.
Hon. Mahmoud Tajo Sani ya bayyana jin dadinsa da godiyarsa ga kungiyar NYCN kan wannan girmamawa.
NYCN GAYA
Idris Ibrahim Adam