29/01/2026
Rabiu Boyora ne ya rubuta!
BA ZAMU AMINCE DA ZABUKAN DA SHUGABAN INEC PROFESSOR JOASH AMUPITAN ZAI JAGORANTA A NIGERIA BA...
Inji SCSN
Majalisar Koli ta Shari'a a Najeriya ta bayyana cewa ba za ta amince da zaben da INEC zata gudanar a karkashin jagorancin Farfesa Joash Amupitan ba, sakamakon kalaman da ya furta akan yankin Arewacin Najeriya...
Sheikh Bashir Umar shugaban zauren majalisar koli ta Shari'a shine yake bayyana haka a lokacin taron da kungiyar tayi a Abuja jiya laraba 28 ga watan Janairu 2026..
Amupitan yayi kalaman da suke ba gaskiya ba wadanda s**a haifar da kiyayya tare da yada propaganda akan wai ana yiwa kiristoci kisan kiyashi a Arewa wanda hakan zallar nuna wariya ne..
Mutanen da suke da tabo akan kalaman nuna wariyar addini ba irinsu ne ya kamata ace suna shugabantar babbar hukuma dake da alhakin kulawa da hakkin kiristoci da musulmi..