20/10/2025
Kotun majistire mai lamba 7 a jihar Kano ta umarci hukumar Hisbah ta ɗaura aure tsakanin Ashiru Mai Wushirya da Basira Yar Guda, nan da kwana 60.
Kotun ta kumakarkashin jagorancin mai Shari’a Halima Wali, ta umurci shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano ya sa ido wajen tabbatar da an ɗaura da auren kamar yadda kotu ta bayar da umarni.
Kotun ta ce idan aka kasa gudanar da auren cikin wa’adin da ta bayar, za a dawo da su gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin da s**a aikata.ta